Tambaya: Shin acikin watan Almuharram akwai wata rana da azumi yake zama wajibi acikinta?
Amsa: Babu wata rana ko wata acikin watanni da azumi ke zama wajibi sai watan ramadan, duk wani wata bayan ramadan azumi acikinsa yana zama azumi ne na tadawwu’i, ma’ana ba wajibi ba, mutum ne yake yi don samun lada da son ransa, sai dai in kuma azumin ramako ne, Akwai watanni da ranaku da azumi acikinsu suke da falala, annabi yayi bayaninsu, kaman wannan wata ta Almuharram, musamman ma Ranar goma ga wata wacce itace ranar “Ashura” da rana daya kafinta da rana daya bayanta, wannan azumin nada mahimmanci sosai, domin yana kankare zunuban shekara, sannan azumi acikin watan Almuharram ma yana da falala sosai kaman yanda muslim ya rawaito, Manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) yace: “Mafi falalar azumi bayan watan ramadan shine azumin watan Allah Almuharram, mafi falalar sallah bayan sallar farilla itace sallar dare”.
Wannan baya nuna wajibci, amma mustahabbi ne mutum yayi, Allah yasa mudace, Ya bamu daman Bauta masa abisa basira.
Leave a Reply