Me ake fadi yayin da iska ya kaɗa?

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Me ya dace Musulmi ya faɗa lokacin da iska ke kaɗa wa?

A’isha Allah ya ƙara mata yarda ta rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama idan iska ya tashi yana cewa:

اللَّهُمَّ إنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ ما فِيهَا، وَخَيْرَ ما أُرْسِلَتْ به، وَأَعُوذُ بكَ مِن شَرِّهَا، وَشَرِّ ما فِيهَا، وَشَرِّ ما أُرْسِلَتْ به


Allahumma inni As’aluka khairaha, wa khaira ma fiha, wa khaira ma ursilat bihi. wa a’uzu bika min sharriha wa sharri ma fiha wa sharri ma ursilat bihi.


Fassara:

Allah ina roƙonka alherinta da kuma alherin dake cikinta, da kuma alherin da aka turo ta dashi, Allah ina neman tsari daga sharrinta da kuma sharrin dake cikinta, da kuma sharrin da aka turo ta dashi.

Wannan hadisi ingattacce ne Muslim ya rawaito shi a hadisi mai Lamba ta 899

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories