Kalmar Ahlussunnah kalma ce da
take nufin ma’abota sunnar Annabi
(S.A.W), ma’ana wadanda suke
kan sunnar Annabi (S.A.W) a cikin
akida da ibada da mu’amala. An
fara amfani da wannan suna tun a
cikin karni na daya, a lokacin da
bidi’o’i da fitintinu suka kunno cikin
wannan addini kamar yadda
babban tabi’in nan Muhammad Bin
Sireen ya fada, akan kara lafazin
jama’a, a ce Wal Jama’a saboda
Ahlussunnah a hade suke, sun
hadu a babin akida da ibada da
mu’amala, tushen addininsu daya
ne, Alkur’ani da Sunnah da Ijma’i,
sabanin wadanda ba su ba, zaka
same su a rarrabe, akida ta
banbamta, hakanan ibada da
mu’amala.
Don haka cikakken Ahlussunnah
shi ne wanda ya tsaya akan littafin
Allah da Sunnar Manzon Allah, a
bisa fahimtar muminan farko,
sahabban Annabi (S.A.W) da
wadanda suka biyo su da
kyakkyawa. Allah ka samu cikin
cikakkun Alhlussunnah.
Leave a Reply