ALKAKI DA RUWAN ZUMA( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa Ta 24
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam A Lokacin Samartaka
3. Kungiyar Tabbatar Da Adalci Da
Kariyar Marasa Galihu
Bayan gama wancan yakin da muka
fada ne aka kafa wata kungiya a garin
Makka domin agaza ma wadanda suke
marasa galihu ne daga cikin mazauna
garin Makka da kuma baki masu kawo
ziyarar kasuwanci ko ta ibada. Dalilin
kafa wannan kungiya ya samo asali ne
daga wani zalunci da Asi dan Wa’il ya
so ya yi ma wani bako da ya zo da
hajarsa daga kasar Yemen. Asi ya sayi
kayansa ya ki biyan sa, ya kuma yi ma
sa barazanar ya je ya kai kara duk
inda yake ganin za a iya kwatar ma sa
hakkensa. Jin haka da wannan bako
ya yi sai ya fashe da kuka, ya koma
daidai Ka’aba yana kururuwa yana
neman mai agaza ma sa. A nan ne
baffan manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam Zubairu dan Abdulmuttalib
ya tashi yana neman a hada kai don a
taimaka ma sa. Mutanen arziki daga
gidaje daban daban suka amsa kiran
sa, sai suka hadu a gidan Abdullahi
bin Jud’an inda suka sa hannu a wata
yarjejeniya cewa, daga yau duk wanda
aka zalunta za su taimake shi su
kwato ma sa hakkensa. Ba su bari aka
kwana ba a rannan suka tashi suka je
da karfin tsiya suka matsi Asi dan
Wa’il suka amsar ma wannan bako
hakkensa. Daga nan ne kuma suka
shiga sa ido ga al’amurran manyan
gari domin su tabbata an yi ma
mutane adalci.
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya
fadi wannan kwamiti da aka yi tare da
shi a lokacin yana saurayi. Ya ce bai
taba nadamar an yi wannan aiki da shi
ba, kuma da za a sake kafa irin
wannan kwamiti a musulunci to da zai
zama memba a cikin sa. As-Sunan na
Baihaki 3/367 da kuma Fiqh As-Sirah
na Ghazali, shafi na 72.
Da wannan ne malamai suka fahimci
cewa, aikin alheri a ko ina ake yin sa
alheri ne. Kuma ya halalta a hada kai
da kowane irin mutum a kan manufar
da take kawo ci gaba in dai ba ta ci
karo da Shari’ar musulunci ba. Allah
Tabaraka Wa Ta’ala yana cewa:
“.. Kuma ku taimaki juna a kan
ayyukan da’a da tsoron Allah, kuma
kada ku taimaki juna a kan ayyukan
zunubi da ta’adi” Suratul Ma’ida: 2.
Haka kuma muna iya fahimta daga
labarin kafa wannan kwamiti cewa,
duk yadda aka lalace ba za a rasa
mutanen kirki ba a koda yaushe masu
mutunci kuma masu neman gyara.
Tun kafin ya zamo manzo, Muhammad
Sallallahu Alaihi Wasallam bai ware
kansa daga jama’a ba, a’a, yana tare
da su ga ayyukan alheri masu alfanu
da kawo ci gaba. As- Siratun
Nabawiyyah na Sallabi, shafi na
59-61.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates