Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da
Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi
Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala
Alihi Wasallam
Fitowa Ta 30
Daga Cikin Fifikonsa
Babu wani mahaluki da Allah
Tabaraka Wa Ta’ala ya girmama
matsayinsa kamar wannan bawan
Allah da muke cikin tarihinsa. Kuma
ya kebance shi da wasu darajoji da
ba shi tarayya da kowa a cikin su. Za
mu zayyana kadan daga cikin su:
1. Fifikon Shiriyarsa
Daga cikin darajojin ma’aiki
Sallallahu Alaihi Wasallam akwai
kasancewar shiriyarsa ita ce
mafificiya a kan ta kowa. Kuma duk
abin da ya saba ma umurninsa ko ya
kauce daga tafarkinsa sunan wannan
abin batacce. Allah Tabaraka Wa
Ta’ala da kansa ya ba shi shedar
cewa, ba shi furuci da son zuciya.
Suratun Najm: 1-4. Haka kuma
madaukakin sarki ya shedi harshensa
da zuciyarsa da ganinsa, ya tabbatar
ma sa da mafi kyawo da nagartar
halaye.
Sanin wannan wajibi ne domin shi ne
hakikanin ma’anar shedar da muke yi
“Muhammadur Rasulullah” a cikin
kalmar shahada.
Bisa ga haka, duk wanda yake da
wani abin biya wanda yake saba ma
manzon Allah, ko yake neman raba
gardama a wurin wani ba shi ba, ko
yake tafiya kan wani tafarki da ya yi
hannun riga da nasa to, wannan bai
darajanta manzon Allah yadda ya
dace da matsayinsa ba. Ba ka gani
ba, a kullum Allah ya ce a yi ma sa
biyayya ko a mayar da al’amari gare
shi sai ya mayar da mu ga manzon
nasa? Wane ne yake tarayya da shi a
wannan matsayi? Kwantar da
hankalinka ka yi nazarin wadannan
ayoyi alal misali:
(( ﻭﺇﻥ ﺗﻨﺎﺯﻋﺘﻢ ﻓﻲ ﺷﻲﺀ ﻓﺮﺩﻭﻩ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﺮﺳﻮﻝ
ﺇﻥ ﻛﻨﺘﻢ ﺗﺆﻣﻨﻮﻥ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻵﺧﺮ( (
) )ﻣﻦ ﻳﻄﻊ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻓﻘﺪ ﺃﻃﺎﻉ ﺍﻟﻠﻪ( (
) ) ﻟﻘﺪ ﻛﺎﻥ ﻟﻜﻢ ﻓﻲ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺳﻮﺓ ﺣﺴﻨﺔ ))
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam shi ne samfurin dan Adam
wanda Allah yake son ya zame ma na
madubi, abin koyi a cikin duk
sha’anin rayuwa. Kuma a cikin
rayuwarsa ba abin da kake bukata da
zai shiryar da kai sai ka same shi. Da
haka ne ya zama addinin Allah ya
kammala ba shi bukatar sabuntawa.
Har Allah madaukakin sarki ya ba da
shelar haka a Suratul Ma’ida: 5.
Sanin haka ne ya sa malaman
Sunnah tuni suka dukufa wajen
tattara sunnoninsa na addini da na
rayuwa. Idan ka samu littafin “Zad Al-
Ma’ad Fi Hadyi Khair Al-Ibad” na
shaihun malami Al-Hafiz Ibn Qayyim
Al-Jauziyyah babban almajirin Ibn
Taimiyyah ba abin da zai kubuce ma
ka ta wannan fannin in Allah ya so.
Za ka samu tafarkinsa na cin abinci,
da zama, da tafiya, da kwanciya, da
magana, da tufafi, da alwala, da
sallah, da addu’oi da huldodin
zamantakewarsa da masoya da
makiya da ma kome da kome. Ina
gwanin wani? Ga gwanin duk
musulmin kirki.
Leave a Reply