ALKAKI DA RUWAN ZUMA27( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa Ta 27
Siffar Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam
Ruwayoyi sun bayyana cewa, manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam
kyakkyawan mutum ne, mai kwarjini.
Mutum ne kuma mai matsakaicin
tsawo, fari, amma ba fari tas ba. Yana
da fadin kirji, da kai mai matsakaicin
girma, da gashin kai mai tsawo. Haka
kuma tafin hannayensa da na
kafafunsa suna da girma da laushi
kamar ka shafa al-hariri. Yana da
fadin goshi da fuska mai walkiya.
Yana da kaurin lebata da wushirya ga
hakoransa masu haske. Idan ya yi
magana har wani haske yake fita daga
bakinsa. Idanunsa manya ne masu fari
kamar wata dan sha hudu. Komai a
jikinsa bai faifaye ba. Cikinsa a sade
yake da kirjinsa. Ba zaka ce ma sa
kakkaura ba, sannan kuma shi ba siriri
ne ba. Mai yawan annashuwa ne da
murmushi. Idan ka ba shi hannu ba
zai fara janye hannunsa ba har sai ka
janye naka. Yakan kalli mutum idan ya
hadu da shi a cikin murmushi da
fara’a har sai ka yi tsammanin ba shi
da masoyi kamar ka. A kafadarsa
akwai wani hatimin annabta da ya
tsiro daga naman jikinsa. Yakan kuma
sanya zobensa na azurfa a hannunsa
na dama.
Mutum ne mai tausayi ga bayin Allah
musamman masu rauni. Ba ya rama
gayya da fushi. Hakurinsa ya zarce
kiyastawa. Domin ba ya fushi sai in an
keta dokar ubangijinsa. Ga shi da
karimci da baiwa kamar iskan asubahi.
Duk wanda ya gan shi zai cika ma sa
fuska. Wanda kuwa duk ya zauna da
shi zai ce ma ka ban taba ganin irin
sa ga kyawon hali ko halitta ba.
Yana da saurin tafiya kamar wanda
yake gangarowa zuwa kwari daga
jigawa. Ba kuma ya kan waiwaya idan
yana tafiya ba sai dai ya juyo gaba
daya. Waiwaye alamun matsorata ne.
Jarumawa sun ba da shedar cewa,
idan yaki ya yi zafi a bayansa maza ke
buya.
Kawaicinsa ya fi kalaminsa yawa. Idan
ya buda baki zai yi magana mai ratsa
zuciya da sanyaya gabbai kuma
wacce kowa yake iya ganewa.
Masoyansa da makiyansa duk sun
sheda cewa, bai taba karya ba ko da a
cikin wasa. Tare da haka yakan saki
jiki ya yi raha da iyalansa ko da
almajiransa, yana kankan da kansa ta
yadda har idan bako ya zo yana cikin
almajiransa ba zai gane wane ne shi
ba sai ya tambaya. Ya kan nemi
labarin wanda bai gani ba a cikin
sahabbansa. Ya kai ziyara wurin
maras lafiya, ya halarci jana’izar
wanda ya cika, kuma ya wa iyalansa
ta’aziyya da kyakkyawar magana
wacce take rage ma su radadi da jin
zafin mutuwa.
Ya kan karbi kyauta daga mutanen
birni da na kauye, kuma ya yi godiya a
kan ta, sannan ya saka da abin da ya
fi ta.
Idan ya ja mutane sallah ba ya kan
tsawaita ba, amma idan ya tsaya yana
sallah a cikin gidansa yakan tsawaita
matuka, ya dage yana mai kankan da
kansa ga ubangiji har sai iyalansa sun
tausaya ma sa.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam bai damu da abin duniya
ba. Kuma ba ya zagi, ba ya la’anta, ba
wata kalima yasasshiya da take fita
daga tsarkakakken bakinsa. Idan ya
kyamaci abu sai dai a gani a fuskarsa.
Idan ya shiga gidansa abu na farko da
yake fara yi shi ne amfani da aswaki
don ya goge bakinsa. Saboda cikar
tsaftarsa babu kayan da yake sha’awar
sa wa kamar farare. A kullum ba shi
rabuwa da kanshin turare.
Mun tattara wannan fasali ne daga
wurare daban daban a cikin littafin:
As-Shama’il Al-Muhammadiyya na
Imam Abu Isa At-Tirmidhi kuma mun
takaita matuka.
Ya Allah! Ka dubi kaunarmu ga
wannan badadayi naka ka yi mana
rabon samun cetonsa da kuma samun
kusancinsa ranar alkiyama.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates