Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam Da Darajojinsa
Fitowa Ta 28
Sanin Matsayin Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam
A cikin wannan fasali muna son ne mu
dan tsakuro wasu daga cikin darajojin
da ubangijinmu madaukaki ya ba
manzonsa a cikin Alkur’ani:
1. Manzon Allah fitila ne kamar yadda
Allah ya kira shi da kansa:
(( ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺇﻧﺎ ﺃﺭﺳﻠﻨﺎﻙ ﺷﺎﻫﺪﺍ ﻭﻣﺒﺸﺮﺍ ﻭﻧﺬﻳﺮﺍ *
ﻭﺩﺍﻋﻴﺎ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﺈﺫﻧﻪ ﻭﺳﺮﺍﺟﺎ ﻣﻨﻴﺮﺍ ))
Suratul Ahzab: 45-46
(( ﻳﺎ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻗﺪ ﺟﺎﺀﻛﻢ ﺭﺳﻮﻟﻨﺎ ﻳﺒﻴﻦ ﻟﻜﻢ ﻛﺜﻴﺮﺍ
ﻣﻤﺎ ﻛﻨﺘﻢ ﺗﺨﻔﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﻳﻌﻔﻮ ﻋﻦ ﻛﺜﻴﺮ، ﻗﺪ
ﺟﺎﺀﻛﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻧﻮﺭ ﻭﻛﺘﺎﺏ ﻣﺒﻴﻦ * ﻳﻬﺪﻱ ﺑﻪ ﺍﻟﻠﻪ
ﻣﻦ ﺍﺗﺒﻊ ﺭﺿﻮﺍﻧﻪ ﺳﺒﻞ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﻳﺨﺮﺟﻬﻢ ﻣﻦ
ﺍﻟﻈﻠﻤﺎﺕ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻨﻮﺭ ﺑﺈﺫﻧﻪ ﻭﻳﻬﺪﻳﻬﻢ ﺇﻟﻰ ﺻﺮﺍﻁ
ﻣﺴﺘﻘﻴﻢ))
Suratul Ma’ida: 14-16
2. Kuma kafin Allah ya aiko shi sai da
ya wanke masa kirjinsa, ya dauke ma
sa jin nauyin wahalar kira zuwa ga
addini, sannan ya daukaka ambatonsa.
Suratus Sharh: 1-4
3. Allah da kansa ne ya fara yi ma
wannan manzo salati, sannan sai
mala’ikunsa. Bayan haka ne ya ce mu
ma mu sa baki a cikin wannan aiki
mai albarka. Suratul Ahzab: 56
4. Babu wani mahaluki da Allah ya
rantse da rayuwarsa in ba manzon
Allah ba, kamar yadda Ibnu Abbas (R)
ya fada. Suratul Hijr: 72
Ban da wannan kuma Allah ya yi ta
shan rantsuwa a kan al’amarinsa.
Misali, a Suratul Qalam Allah ya rantse
cewa annabinsa ba mahaukaci ba ne.
Suratu Nun: 1-5
A Suratud Dhuha kuma ya rantse cewa
bai fita batunsa ba kamar yadda wasu
suka zata saboda jinkirin wahayi da
aka samu. Suratud Dhuha: 1-3.
A Suratun Najm allah ya rantse don
kare annabinsa daga kasancewa a kan
bata ko furuci da son zuciya kamar
yadda mushrikai suke rayawa. Suratun
najm: 1-5.
A Suratu Yasin Allah ya rantse da
Alkur’ani cewa Muhammad Sallallahu
Alaihi Wasallam yana cikin manzanni.
Suratu Ya Sin: 1-3
5. Kai, ba wata addu’a fa da manzo ya
daga hannunsa ya yi zuwa ga Allah
sai ka ga ya yi gaggawar karba ma sa.
Wani lokacin ma idan ya yi fata tun
bai roka ba Allah yake ba shi. Kamar
yadda ya faru ga labarin sauya alkibla,
in da Madaukakin sarki ya ce:
(( ﻗﺪ ﻧﺮﻯ ﺗﻘﻠﺐ ﻭﺟﻬﻚ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻓﻠﻨﻮﻟﻴﻨﻚ ﻗﺒﻠﺔ
ﺗﺮﺿﺎﻫﺎ، ﻓﻮﻝ ﻭﺟﻬﻚ ﺷﻄﺮ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﺍﻟﺤﺮﺍﻡ ..))
“Hakika muna ganin jujjuyawar
fuskarka zuwa sama. To, za mu juyar
da kai zuwa ga alkiblar da kake so.
To, ka juyar da fuskarka zuwa
masallaci mai alfarma..” Suratul
Baqarah: 144:
Leave a Reply