ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa ta 13
Faruwar wannan lamari da muka fada a
baya na korar rundunar Abrahata da
Mai-sama ya yi ya dada sanya
larabawa su san girman dakin Allah, su
kuma mutunta mazauna birnin Makka.
Har ta kai ma ko ana fashi da makami
ayarin Makka zai wucewar sa salun
alun a dauke da dukiya mai dinbin
yawa amma ba wanda zai tare shi don
matsayin da mutanen ke da shi a cikin
zukatan jama’a. A cikin shekaru 40 za
ka so ka ga irin karin kwarjini da
muhibba da wannan birni na Makka
yake da shi da yawan alhazai masu
zuwa don girmama shi. Ashe dai akwai
abinda Allah ya nufa na jawo
hankalinsu zuwa ga wannan gari
domin a daidai lokacin ne alfijir yake
ketowa; fitilar da zata haskaka duniya
ta bayyana a wannan gari mai tarin
kwarjini da albarka. Rasulullahi Fi
Makka, na Dr. Yahya bn Ibrahim Al-
Yahya, shafi na 66.
Yanzu kuma lokaci ya yi da zamu
fantsama kai tsaye cikin taskar tarihi
domin mu karanta labarin wannan
haske da yadda ya game duniya.
Ku dakace mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates