ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa ta 12
Shekarar Giwaye
Shekarar haifuwar fiyayyen halitta ita
ake ce ma shekarar giwaye. Abinda ya
faru a wannan shekarar kuwa (shekara
ta 571M) shi ne, an yi wani sarki a
garin San’a’a ta kasar Yemen wanda
ake kiran sa “Abrahatal Ashram”. Ya
mulki wannan garin ne a bayan da ya
rinjayi “Aryat” wani nadadden sarki
daga fadar Najashi na kasar Habasha.
Wannan juyin mulki da ya yi kuwa ya
fusata Najashi ainun, al’amarin da ya
rikita Abrahata ya sa shi ‘yan kame-
kame don neman kubuta daga
sharrinsa. A kan haka ne ya aike masa
da sakon cewa, zai gina wani babban
dakin ibada a bisa tafarkin addininsa
mai kuros (Coci) wanda ba a taba jin
labarin irin sa ba. Ya dauki alkawarin
idan ya kammala wannan Coci zai juya
hankalin larabawa da suke yin
tururuwa suna bi ta kasarsa don
ziyartar dakin Allah da ke Makka.
Abrahata ya gina wannan Cocin ya
kuma kawata ta matuka bayan ya kashe
makudan kudade. A zatonsa idan
larabawa suka gan ta hankalinsu zai
raja’a gare ta su bar Ka’aba. Da
wannan shi kuma sai ya samu daukaka
ma kansa da birninsa na San’a’a. Ya
janyo karin kasuwanci da ciniki ta
hanyar ‘yan ziyara sai ya bunkasa
tattalin arzikin kasarsa. Ga shi kuma
idan haka ta samu ya kubuta daga
sharrin Najjashi tun da ya juya
hankalin larabawa zuwa bautar
Almasihu. Da haka sai ya yi fatar ya
jefi tsuntsu hudu kenan da dutse guda.
(Mausu’at At-Tarikh Al-Islami, na Dr.
Ahmad Shalabi, 1/119-120). To, amma
ga alama ko tsuntsu guda bai samu ba.
Domin kuwa ko da suka ahamo
wannan Coci tayi kaca-kaca da najasa!
To wa zai yi ibada a daki maras tsarki,
wanda ba shi da alfarma da za ta kare
shi daga wulakanci?! Ai kuwa gogan
sai ya shaci fushi, ya yi rantsuwa sai ya
rusa Ka’abar da ke Makka tun da yake
larabawa ake tuhuma da wannan ta’adi
da aka yi wa Coci. Ya shirya runduna
wacce larabawa ba su taba jin irin ta
ba. A cikin ta har da giwaye. Ya kuma
jagoranci rundunar da kansa. Kafin
isowar sa birnin Makka labari ya game
sassa. Kuma duk wani yunkuri da
larabawa suka yi domin yin arangama
da shi da hana shi isa Makka sai da ya
ci tura. Amma fa sun yi amanna cewa,
Allah shi ne mai wannan dakin kuma
ba zai kyale shi ba. Misali, a kan
hanyarsa ta zuwa Makka, kabilun
larabawa da dama sun tare Abrahata
kuma suka yake shi amma ya tarwatsa
su. Tun daga kasar Yemen wani
sadauki da ake kira Zu-Nafar ya ci
karo da shi tare da rundunarsa amma
tuni giwaye suka tattaka su. Kabilun
Khas’am; Shahran da Nahis su ma sun
tura na su jarumawa aka fatattake su.
Da rundunar Abrahata ta iso Ta’if sai
suka bace hanya. Kuma duk wanda
suka tambaya sai ya ki dora su a kan
hanya. Sai da suka samu wani
shakiyyin mutum ana ce da shi “Abu
Rigal” shi ya yi ma su jagora amma
Allah bai yi masa jinkiri ba, domin ba
su yi nisa ba mala’ikan mutuwa ya
sharbe shi. Shi ne wanda larabawa ke
jifar kabarinsa har in da yau ke magana
a wani kauye da ake kira Mugammas a
hanyar Ta’ifa zuwa Makka. (As-Sirah
An-Nabawiyyah, na Ibn Hisham
1/58-60).
Allah sarkin sarauta! Ashe dai ko ina
akwai marasa arziki a cikin duniya.
Lokaci da Abrahata ya isa Makka sai
mutanen garin duk suka taru wurin
dakin Allah suka makalkale gare shi
suna kai kara ga ma’abocinsa. Sa’annan
suka fice daga garin suna jiran faruwar
ikon Allah gwanin sarki.
A lokacin da ayarin Abrahata ya sauka
wajen gari, Abdulmuttalib ya samu
ganawa da shi in da ya nemi a mayar
ma sa da rakumansa guda 200 da
wannan runduna ta mamaye. A cikin
ta’ajjubi Abrahata ya tambaye shi,
rakumanka ne suka fi maka
muhimmanci ko wannan daki da ka
gaji ibada a cikin sa daga kaka da
kakanni?! Sai Abdulmuttalibi ya kada
baki ya ce ma sa: “Ba haka ba ne.
Rakuma mallakina ne, shi ya sa nake
neman abina. Shi kuma wannan daki
yana da mai shi kuma zai kare shi. Ba
zai bari kome ya same shi ba. Kangara
irin ta kafirci ta sa Abrahata duk da jin
wannan magana bai karaya ba balle ya
fasa abinda ya yi niyya. Amma ya
mayar ma da Abdulmuttalibi duk
dukiyarsa da aka riga aka kwace can da
farko.
An ba da labarin cewa, su wadannan
giwaye sun turje a bayan garin Makka
duk lokacin da aka fuskantar da su
zuwa garin. Amma idan aka karkata su
zuwa hanyar komawa sai su zura da
gudu. Kaico! In da akwai basira da
kafirai sun gane wannan ishara. Amma
ina! Da suka ci gaba da nacewa a kan
shiga garin ne sai Allah ya aiko ma su
wasu irin tsuntsaye masu manyan
kawuna wadanda ba a taba ganin irin
su ba, suna dauke da duwatsun wuta
suna jifar su da su. Duk wanda suka
samu kuwa ba shi kai labari. Da haka
suka tarwatse rundunar kowa ya san
inda dare ya yi ma sa. Shi kam uban
tafiyar; Abrahata faduwa ya yi a
tagayyare duk jikinsa ya lalace. Suka
dauke shi suka koma da shi gida
yatsunsa suna sancewa guda guda, ya
cika a nakkashe, Allah ya wulakanta
shi. (As-Sirah An-Nabawiyyah, Ibn
Hisham 1/58-60 da Fathul Bari
12/210-216).

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates