ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa Ta 16
Babba Dan Manyan Mutane
Wannan salsala da muka fada
tsarkakakkiya ce; dan halas bayan dan
halas. Babu wanda aka haifa ta hanya
gurbatacciya. Wannan gidan da
manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Ala Alihi Wasallam ya fito daga
cikinsa kuwa, babban gida ne mai
daraja da alfarma. Zuwa ga kakansa na
goma ne (Quraish) ake jingina kabilar
gaba daya. Kakansa Ilyas (na 16) shi
ne mutum na farko da ya fara Hadaya;
sadaukar da dabba a yanka ta don
girmama dakin Allah. Kakansa na
hudu kuwa; Qusayyu shi ne wanda ya
gina Mash’arul Haram a Muzdalifa
inda alhazai ke taruwa in sun sauko
daga Arafat domin hutawa da kuma
ambaton Allah. Sannan kuma shi ne ya
hada kan Quraishawa, ya tsara
al’amarinsu. Kuma shi ne ya fara
hidimar baki masu zuwa aikin Hajji
har ya samar da wasu ma’aikatu don
kula da su. A cikin wadannan
ma’aikatun ne ya sanya ‘ya’yansa suna
hidimar debo ruwan sha daga rijiyoyin
da ke wajen gari don shayar da alhazai
kyauta. Haka kuma suna raba abinci ga
mahajjata bayan sun tattara shi daga
hannayen mutane tun kafin isowar baki
wurin aikin Hajjin. Sannan suna
tufatar da dakin Ka’aba. A gidansu ne
kuma duk Quraishawa suke haduwa
domin tattauna mas’alolin ci gaban
al’ummarsu. Sa’annan su ke daukar tuta
idan yaki ya kama da abokan gaba. Ka
ga dai gidan ya zama shi ne masauratar
garin Makka kenan.
Kakansa na biyu kuwa; Hashim
babban mai arziki ne wanda ya sarrafa
dukiyarsa gaba daya wajen taimakon
mutane. Zanannen sunansa ma shi ne
Amru, amma an yi ma sa lakabi da
Hashim ne saboda yawan ciyar da
abinci ga bayin Allah da yake yi. Shi
ne kuma wanda ya tona rijiyoyi a cikin
garin Makka don sawwake ma
mutanen gari matsalar ruwan sha da
kuma sawwake aikin da ake yi a
gidansu na bin alhazai har a
masaukansu ana ba su ruwan sha
kyauta. Don ci gaban tattalin arzikin
jama’arsu, Hashim shi ya fadada
kasuwancin mutanen Makka daga
kasuwancin cikin gida zuwa na
kasashen waje. Ya kago abinda ake
kira “Ilaf” inda ake hada ayari sau biyu
a kowace shekara don kai haja a tallata
a kasashen waje da kuma sawo wasu
hajojin da ake bukata daga can. Allah
ya fadi wannan tafiyar tasu a cikin
suratu Quraish. Da haka ne Hashim ya
zamo jakadan larabawa a kasashen
ketare wanda yake kulla duk wata
yarjejeniya da taimakon juna ko
zaman lafiya da sauran kasashe.
(Mausu’tut Tarikh Al-Islami, na
Shalabi, (1/182).
Abdulmuttalib – Kakan manzon Allah
(S) na farko shi ne ya gaji duk
ayyukan alheri da baffansa Muttalib
yake yi. Don haka sai ya sake tona
rijiyar Zamzam bayan har an manta da
ita saboda karin sauki ga matsalar ruwa
musamman a lokacin Hajji.
Abdulmuttalib dai ba a nada shi a
matsayin sarkin garin Makka ba, ba
kuma shi ne ya fi kowa hali da zarafi a
garin ba, amma saboda yawan
karimcinsa da hidimomin da yake ma
jama’a ya saya wa kansa girma wanda
ya sa duk al’amurran garin suka koma
hannunsa. Shi ne wanda yake zartar da
kome kuma mutane suna yi ma sa da’a.
A lokacin ma da Abrahata ya zo ya
yaki garin Makka shi ne kadai wanda
ya tafi ya yi magana da shi.
An ba da labarin cewa, a lokacin da ya
tona rijiyar Zamzam Quraishawa sun
nemi ya yi tarayya da su a cikin ta,
amma ya ki yarda. Suka kuwa yi
jayayya da shi har wurin wata bokanya
don ta yanke ma su hukunci. Amma
kafin su kai garin da ita bokanyar take
sai wani abin al’ajabi ya faru. Domin
kuwa sun gamu da matsanancin qishi
da karewar guzuri. Ana haka sai suka
ga hadari ya kankama, amma da ruwa
ya sauka bai sami kowa ba sai
Abdulmuttalib. Ganin haka sai suka
hakura suka ce da shi mun yarda Allah
ya zabe ka. Tirkashi! Wannan fa shi ne
kakan manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam.
A cikin ‘ya’yan Abdulmuttalib, Abu
Talib shi ne ya gaji daukar nauyin
hidimar alhazai bayan mutuwar
Mahaifinsu. To, a lokacin da kudi suka
gaza ma sa sai ya ranci kudi Dirhami
dubu goma daga dan uwansa Abbas.
Ya kuma kashe kudin gaba daya wajen
hidimar alhazai. Bayan da ya kasa
biyan su ne ya zame ma sa tilas ya
amince ya bar wannan matsayi da aiki
mai daraja na hidima ga kanen nasa
Abbas dan Abdulmuttalib.
Ku dakace mu
Zamu ci gaba da yardar Allah

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories