ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Sayyadi
Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam
3
Halin da Duniya Take Ciki Kafin
Bayyanar Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam
An samu yankewar isowar saqon Allah
zuwa ga mutane tun bayan dauke
annabi Isa Alaihis Salam daga duniya
da aka yi. Domin kuwa sai da aka yi
sama da shekaru xari shida ba wani
annabin da aka aiko ma jama’a ya yi
gargaxi a cikin su. savanin inda aka
fito sa’adda annabawa suke zuwa jere;
wani bayan wani. Kai, wasu ma
annabawan a lokaci xaya ake aiko su
ko dai zuwa ga mutane daban daban ko
kuma zuwa ga al’umma xaya kamar
yadda aka aiko annabi Musa da
qanensa Haruna (AS) zuwa ga Banu
Isra’ila. Annabi Ibrahim ya kasance
annabin Allah a lokaci xaya tare da
annabi Luxu (A.S). Haka kuma ‘ya’yan
annabi Ibrahim; Isma’ila da Ishaqa suka
yi lokaci guda da shi ga annabta. Shi
ma annabi Ya’aqub ya yi lokaci xaya
da xansa annabi Yusuf (Amincin Allah
ya tabbata a gare su gaba xaya).
Wannan yankewa ta zuwan wahayi da
aka samu ta sanya duniya a cikin duhu
xib; babu haske ko kaxan a cikin ta.
Bari mu dan yi maganar qasashen
duniya na wancan lokaci wadanda suka
hada da manya manya guda biyu;
Farisa da Ruma.
1. Qasar Farisa:
Qasa ce da ta samu ci gaba sosai ta
fuskar lamarin duniya. Amma ta fuskar
addini qasar gaba xayanta fanko ce.
Suna da addinai guda biyu;
Zaradishtiyyah da Mazdakiyyah, babu
na tsinta a cikin su. Abin bautar su
babba shine wuta. Ba wanda ya san
Allah a qasar, balle ya ce yana bautar
sa. Kuma mata halas ne ga kowa a
wurin su. Mutum zai iya auren uwar da
ta haife shi ballantana qanwarsa ko
kuma ‘yar cikinsa. Banbancin
addininsu na biyu da wancan na farkon
shine su ‘yan Mazdakiyyah ban da
mata ma ko kudi kayan kowa ne ba
mai mallakar abin kansa, domin
matsayin ruwa suke da iskan shaqa a
wurin su.
2. Qasar Rumawa
Wannan kuma qasa ce da suka ce suna
bin addinin Nasara, kiristanci kenan.
Amma ina su ina addinin annabi Isah
(AS) bayan duk an canja addinin an
sanya wasa a cikinsa! Littafin ma da
Allah ya saukar ma sa an canja shi an
shigar da son zuciya da tatsuniyoyi a
cikinsa. Sun maye gurbin Tauhidi da
shirkar nan ta “Allah uku” da aka sani.
Ga kuma rikici na cikin gida da ya
dabaibaye al’ummar da ke cikin
wannan daula na yawan mazhabobin
addini marasa sassauci ga junansu.
Mahukuntan waxannan manyan
qasashe biyu da muka faxa sun shahara
da zalunci da shan jinin talaka.
Akwai wasu qananan qasashe da zamu
yi magana a kan su.
Kada ku manta ku tashi sahur da wuri
domin gobe ne wunin tasu’a idan Allah
ya nuna mana.
Mu kwana lafiya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates