ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam 8
A can baya mun soma kawo wasu
kyawawan dabi’un larabawa da suka
cancantar da su ga zaben Allah don su
zamo tubalin da’awar musulunci.
Larabawa mutane ne masu alkawali.
Harith bn Abbad shi ne jagoran kabilar
Bakr lokacin da suka yaki Taglibawa.
Sai ya kama shugaban rundunar Taglib
wanda ake ce ma Muhalhil a hannu
amma fa bai san shi ba. Sai ya ce ma
sa nuna min Muhalhil in sake ka.
Muhalhil ya ce ma sa, tsakaninka da
Allah in na nuna ma ka shi zaka sake
ni? Ya ce, eh. Ya ce, to ni ne Muhalhil.
Harith ya ce, kash! Amma ka cuce ni.
Amma kuma haka ya sake shi saboda
saba alkawali babban abin kunya ne a
wurin su. Al-Kamil Fi At-Tarikh na
Ibn Al-Athir (1/536).
Sa’annan ba su daukar wulakanci.
Mutuwa ta fiye ma su sauki a kan
daukar raini. Labarin sarki Amru bin
Hind – sarkin Hiyra – wanda ya rasa
ransa a hannun Amr bin Kulthum a
kan ya sa uwarsa ta nemi uwar Amru
ta dauko ma ta faifai. Wannan labari ya
ishe mu misali a kan sabo da ‘yanci da
rashin daukar wulakanci na larabawa
tun kafin zuwan musulunci.
A wadannan halaye da muka fada ba
wata al’umma da ta kama kafarsu.
Haka kuma suna da tsarkin zuciya ga
duk abinda suka ba da gaskiya da shi.
Wannan ya sa suka yaki manzon Allah
(S) bilhakki sa’adda ba su fahimce shi
ba. A lokacin da kuwa gaskiya ta yi
halinta sai suka zamo su ne baraden
musulunci.
Akwai sauran dalilai. Ku dakace mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates