ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Majalisi Na 63( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam Ya Yi Baran-baran Da
Mushrikai
A karo na biyu, sai mushrikai suka
sake nada kwamiti wanda ya kunshi
mutane hudu; Al-Aswad bn
Abdilmuttalib da Walid bn Al-
Mughirah da Umayyatu bn Khalaf da
kuma Asi bn Wa’il. Sai aka ce su je
su sasanta da manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam a kan su
hadu a bauta ma Allah tare da shi,
shi kuma ya zo su bauta ma gumaka
tare. A nan ne Allah madaukakin
sarki ya saukar da “Qul ya ayyuhal
kafirun..” Surar da ta raba ragi kwata-
kwata tsakanin musulmi da mushrikai
wajen sha’anin ibada.
Wannan shi ya tuna min da
kawancen yan Shi’ar Najeriya da
kiristoci in da su – kiristocin – suka
fara halartar bikin maulidi a tare da
su a birnin Zariya tun shekarar 2012.
Daga bisani a wannan shekara ta
2014 sai kowane bangare ya shirya
maulidi irin na dan uwansa. ‘Yan
Shi’a suka yi maulidin annabi Isah
(AS) a yayin da su kuma kiristoci
suka yi maulidin annabi Muhammad
(SAWW) duk da sunan hadin kai da
zaman lafiya. Wannan kwadon (ko
kuma rummace) shi ne Allah ya hana
manzonsa ya amince da shi tsakanin
sa da mushrikai. Addinin Allah hanya
daya ce rak. Ko a karbe ta ko a bi
tafarkin jahannama. A kan wannan
batu ne kuma Allah ya saukar da
wasu ayoyi a Suratu Yunus (aya ta
15 da ta 41) da kuma Suratul An’am
(aya ta 56-57).
Duk da haka mushrikai ba su hakura
da kokarinsu na ganin sun shawo kan
musulmi su daina bin kiran
musulunci ba. Sai suka tashi wasu
mutane guda biyu; Nadhr bn Al-
Harith da Uqbatu bn Abi Mu’ait suka
je Madina don su gana da yahudawa
ya’alla ko a samo bakin zaren yadda
za a warware kiran musulunci. Su
kuma daman yahudawa ba wai
gaskiyar ce suka jahilta ba, sai dai
taurin kai ne yake tattare da su.
Domin daman su sun baro kasa mai
albarka ne “Sham” suka tare a
Madina bisa ga sifar garin da suka
gani a cikin At-Taura cewa, manzon
Allah na karshe zai kafa gwamnatinsa
a cikinta. Don haka, idan husuma ta
shiga tsakanin su da larabawa sukan
ce, annabi ya kusa bayyana wanda
zamu taimake shi mu yake ku. Duk a
tsammaninsu za a sake aiko annabin
ne daga cikin ‘yan gidansu “Bani
Isra’ila” kamar yadda aka saba. To,
da Allah ya tashi aiko annabinsa na
karshe sai ya kauce ma gidansu ya
dauko annabi Muhammad daga gidan
baffansu; jikan Isma’ila ba na Ishaqa
ba (dukkansu ‘ya’yan annabi Ibrahim
ne Alaihimus Salam). Su kuma sai
suka ce ba za su bi shi ba don da
aka yi haka an raina gidansu.
Mushrikai sun je neman fatawa a
Madina gurin Yahud, kasancewar su
masu ilmin littafin da Allah ya saukar.
Suka ce, ku fada mana don Allah wai
tsakanin mu da Muhammad wa yake
bisa gaskiya? Kuma idan mu ne kan
gaskiya ku ba mu makarinsa. Ku fada
mana tambayoyin da zamu yi ma sa
na addini mu kure shi!
Sai Yahudu suka ce da su, ai
addininku ko alama ba a hada shi da
nasa. Kun fi shi kusa da gaskiya.
Sannan sai suka ba su tambayoyin
kurewa da suka nema. Nadhru da
Uqbatu sun dawo da tambayoyinsu
guda uku suna murna suka hada
wani sabon kwamiti aka je aka
tambayi manzon Allah (S) aka
tambaye shi. Sai ya ce da su ku bari
sai gobe zan ba ku amsa. Gobe ta
wuce, jibi ma haka. Har aka kwana
goma sha biyar Jibrilu (AS) bai zo ba
bale ya fada ma sa amsa. Da aka kai
haka sai suka fara yi ma sa izgili
suna cewa, daman mun san kai ba
annabin gaskiya ba ne. Manzon Allah
(S) ya shiga damuwa matuka a kan
haka. Sannan Allah ya saukar da
Suratul Kahf wadda ta amsa dukan
tambayoyinsu daya bayan daya, kuma
Allah ya caji manzonsa da cewa zai
ba da amsa gobe ba tare da ya ce “in
Allah ya so” ba. Dalilin da ya janyo
aka yi ma sa wannan jinkiri wajen ba
shi amsa.
Babban darasi a nan, su manyan
bayin Allah ba ayi ma su sassafci a
kan kananan abubuwan da suke
karantar da mutane. A cikin
karantarwar annabawa dole ne kowa
ya sallama wa Allah; ya yarda shi
bawa ne. Kuma ba abin da ya isa ya
yi a cikin mulkin ubangiji sai bayan
amincewar sa. Don haka kome
musulmi yake son yi dole ne ya hada
da cewa, in Allah ya so.
Duk da gamsasshin amsoshin da
Allah da kansa ya ba mushrikai a
cikin wannan sura har yanzu ba su
amince ba. Suna nan kan bakarsu;
sai sun ga baya ga addini.
To, wane irin mataki kuma suka sake
dauka? Mu hadu a darasi na gaba in
rai ya kai, kuma mai sama ya nufa.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates