Ubbada Bin Samit ya rawaito hadisi daga Manzon Allah yace:
Duk wanda ya farka da dare yace: “Lailaha illa-llah wahdahu la sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai’in ƙadir. Alhamdulillah, wa subhanallah, wa La’ilaha illallah wallahu akbar wala haula wa la ƙuwwata illa billah”
لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد، وهو على كل شيء قدير، الحمد لهَ، وسبحان الله، ولا إله إلا الله، والله أكبر، ولا حول ولا قوة إلا بالله
Sannan yace Allah ka gafarta min, ko yayi wata Addu’a Allah zai amsa masa. idan yayi alwala yayi Sallah to za’a amsa masa Sallar sa.
Sahihul Bukhari: 1154
Wannnan hadisi yana nuna mana mahimmancin zikiri musamman wannan zikiri da Annabi ya koyar. Idan mutum ya farka sai ya karanta wannan addu’a. Ko ya roƙi Allah buƙatun sa. Ko ya tashi yayi Salla.
Allah yasa mudace
Leave a Reply