Babu Alakar Siyasa Da Taronmu —Sheikh Bala Lau Shugaban Jibwis Ta Nigeria(Leadership Hausa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

SHEIKH BALA ABDULLAHI BALA LAU shi ne shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) na kasa. A makon da ya gabata ne kungiyar ta yi sanarwar shirya babban taro na shekara, wanda za a gudanar a birnin Ikko, ranar Asabar 15 ga Fabrairu, 2015, wato gobe kenan. Taron zai mayar da hankali wajen hadin kan dukkanin masu bin tafarkin Ahlus-Sunnah a Nijeriya da kasashen Yammacin Afrika.
Kan haka ne LEADERSHIP HAUSA ta nemi karin bayani dangane da gagarumin taron, inda shugaban ya bayyana manufofi da irin manyan baki da malaman da za su halarta.
Ga hirar…
Da farko za mu so mu ji makasudin shirya wannan taronku na gobe Asabar a Legas
Bismillahir rahmanir Rahim, was Sallatu was Salaam ‘ala Nabiyyina Muhammad wa ‘ala alihi wa as haabihi, wa Man Walaahu bi ihsanin ila yaumiddin. Babu shakka makasudin wannan taro shi ne hadin kan al’ummar Musulmi wuri guda su zamanto abu guda kamar yadda Allah ya ke cewa “Ku hadu a kan igiya guda ta Allah kar ku rarraba,” da kuma samun zaman lafiya mai dorewa. Al’ummar Musulmi ba su da bambanci, walau daga Kudu ka ke ko daga Arewa, Musulunci ya hada mu.
Bayan haka, akwai kungiyoyi na Ahlus-Sunnah da su ke zaune a kasashe  Yarbawa da sauran mutanenmu Ahlus-Sunnah da suke kasashen Igbo da nan Arewacin Nijeriya. Abin da muka lura shi ne kowanne daga cikin Ahlus-Sunnah muna da littafin Allah Alkur’ani da sunnar Manzon Allah, a kan shi ne minhajinmu.
Alus sunnah na kasashen Yarbawa suna da masu wa’azinsu da suke yin wa’azi a can amma ba su shigowa Arewa, haka nan ma mu a nan Arewa ba mu shiga Kudu, iyaka dai muna ‘yan’uwa Musulmai amma babu abin da ya ke hada mu.
Kamar shekara daya zuwa biyu da suka gabata muka soma tunanin kai ziyara a kasashen Yarbawa da Igbo domin samun mahada da al’ummar Musulmi za su rika haduwa wuri guda domin tattaunawa a kan matsalolinmu, sai muka yi tour (rangadi) inda muka fahimci cewa akwai bukatar samar da wata gamayya.
Haduwar farko muka nemi a yi ta a Legas, muka bukaci Ahlus-Sunnah da suke kasashen yarbawa su hadu wuri guda, dama suna da Federation of Ahlus-Sunnah akwai kungiyoyin sun kai 30 karkashin wannan. Akwai kuma Jama’atu Izalatin Bid’a wa Ikamatis Sunnah da ma ita ce uwa ga dukkan kungiyoyi, sai muka zauna da Federation muka tattauna a kan ya kamata mu yi conference.
Shi ya sa muka yi rajistar ‘Conference of Ahlus-Sunnah of Nigeria,’ wanda wannan za ta rika sulhunta dukkan Ahlus-Sunnah suna samun kyakkyawar fahimta, akwai sharrance-sharrance da ake yi wa Ahlus-Sunnah ta hanyoyi daban–daban. Akwai rashin zaman lafiya, tsaro ya tabarbare, haka kawai za ka ga an kai wa malamai hari an kashe su.
Ire-irien wannan ba zai haifar wa kasa da alheri ba. Tunanin wannan ya sa muka ga ya kamata mu zauna mu yi wani conference da zai hada mu mu tattauna.
Bayan nan kuma, mun sake kai ziyara ga shugaban Nijar lokacin da aka yi taron Kitabu was Sunnah a kasar Nijar wanda dukkan kasashen Afirka suka halarta. Shugaban Nijar ya aika da wakilai wurin taron, sannan matarsa ma tana daga cikin wadanda suka rika daukar nauyin hidimar taron.
Da aka kammala taron na jagoranci sauran al’umma don mu yi wa shugaban kasan godiya. A wurin godiyar ne muka fada masa shirin da mu ke yi na yin wan conference da zai hada Ahlus-Sunnah wuri guda.
Sai ya ce idan Allah ya yarda duk lokacin da za mu yi mu gayyace shi zai zo. Sannan ya ce duk inda Ahlus-Sunnah su ke da matsala a Yammacin Afirka mu fada masa zai shiga kai tsaye ya yi magana da shugabannin kasar don a kara fahimtar mu; domin ya lura babu wata kungiya da ke wa’azi na da’a da biyayya da zaman lafiya kamar wannan kungiya.
Bisa hakan mun samu karfafuwar gwiwa daga gare shi, shi ya sa muka gayyaci kasashen nan bakidaya na Yammacin Afirka zuwa conference din.
Akwai Ahlus-Sunnah wal-jama’ah na Togo, akwai Ahlus-Sunnah wal-jama’a na Ghana, akwai na kwadebuwa, akwai na Benin Rebublic, akwai Kitabu was sunnah da ihya’us sunnah na Nijar sannan akwai Ahlus-Sunnah wal-jama’a na Burkina Faso. Duk wadannan kasashen mun gayyace su.
Don haka lura da wannan ganin cewa a Nijeriya za a yi ya zama tilas mu gayyaci gwamnatin Nijeriya domin ta ba da sarari a kan iyaka ga Ahlus-Sunnah da za su shigo, taro ne na farko kuma ga shugaban kasar Nijar zai shigo, don haka babu mai masaukinsa fiye da shugaban Nijeriya.
Mun kuma gayyaci dukkanin manyan Nijeriya zuwa taron irin su Janar Buhari, Janar Babangida, Janar Abdulsalami da Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa da Ahmad Bola Tinubu da daukacin gwamnonin Arewa da na kasashen Yarbawa Musulmi.
Taron a fili ne za a yi, za a yi biki ne lokacin da za a bude shi, muna gayyatar kowa da kowa ya zo ya ga yadda Ahlus-Sunnah suke. Yadda ake zargin su ko yadda ake daukansu a matsayin ‘yan ta’adda ko yadda ake daukar su ba haka  ba, kowa ya zo ya gane wa idonsa. Kuma idan an kammala su ma wadannan kasashen za su shirya nasu mu je domin nuna wa duniya yadda Ahlus-Sunnah su ke tare da fitar da su daga kangin wahala.
Tun da taron na hadin kai ne, kamar yadda ka ambata, ban ji kun gayyaci sauran bangarorin Musulmi kamar Tijjaniyya da Kadiriyya, Shi’a da sauransu ba.
Alhamdulillah, idan aka ce Ahlus-Sunnah duniyar Musulmi suna daukar an kasu kashi biyu. Akwai wasu da suke kiran kansu Ahlus-Sunnah amma kuma suna aikata bidi’o’i, su ma ana sa su ne daya daga cikin kashin Ahlus-Sunnah, sannan akwai Shi’a.
‘Yan Shi’a, an san matsayinsu, littafinsu; kusan ba Alkur’ani suka dogara da shi ba, kuma suna la’antar Sahabban Manzon Allah da wasu daga cikin iyalan Manzon Allah (SAW), su kuwa Ahlus-Sunnah ba su da wannan. Saboda haka, muna kokari mu kungiyoyin Ahlus-Sunnah da muke tafiya a kan manhaji guda mu tabbatar da ba mu da wasu rabe-rabe.
Ta yaya za mu yi mu samu juna mu tattauna, ta yaya da’awar za ta kara bunkasa mu samu ci gaba, ta yaya za mu inganta makarantunmu, yaya za mu kula da masu rauni a cikinmu, yaya za mu dogara ga Allah kuma mu samu abubuwan da za su tallafa wa kungiyoynmu ba sai mun tsaya muna barace-barace ba.
Bayan mun cimma nasarar haka, su kuma sauran al’ummar Musulmi za mu hadu da su musamman ‘yan darikun sufaye a kan littafin Allah Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW). A duk lokacin da muka hadu da su a kan haka to babu fada tsakaninmu. Amma duk lokacin da ba wannan ne zai hada mu ba za a yi ta samun rikici a cikin al’umma.
Manzon Allah (SAW) ya ce, “Taraktu feekum amrain,’ Ma’ana, ‘Na bar muku abubuwa guda biyu, wadanda idan ku ka rike su, ba za ku bace ba; littafin Allah da sunnar Manzon Allah (SAW)”. Wannan shi ne abin da zai hada mu da sauran al’ummar Musulmi.
A gefe guda, akwai wadanda suke yi wa wannan taron naku fassarar gangamin siyasa. A na muku kallon magoya baya Shugaba Jonathan ne, kun fito da karfinku, domin ku share masa fagen yakin neman zabe a siyasar 2015, me Malam zai ce kan hakan?
To, mu dai ba mu da wata alaka da shi shugaban kasa a siyasance. Ba mu taba zama muka tattauna da shi ba, duk babu wannan. Sai dai kawai mun gayyace shi ne a matsayin shugaban Nijeriya kasancewar a Nijeriya za a yi taron. Kuma wane ne shugaban Nijeriya na yanzu? Idan akwai wani shugaban Nijeriya mai ci da ba shi ba, to wannan din muka gayyata.
Ba Goodluck Jonathan (tsuransa) muka gayyata ba, Shugaban Nijeriya ne dake rike da ragamar shugabanci. Bakinmu za su shigo, idan shugaban ya ce ba za a yi taron ba, ta zauna ba zai yiwu ba.
Saboda haka duk wanda ya ke kan kujera shi ne muke gayyata don ya dace da lokacin da za a yi taron. Idan da ba shi ne shugaban Nijeriya ba, ba mu da wata alaka da shi. Idan muddin shi ne shugaban Nijeriya kuma ina da alaka da shi kai ma (mai tambaya) kana da alaka da shi, haka nan kowa ma.
Har ila yau, hakki ne na shugaban Nijeriya ya kare wa Musulmi da wanda ba Musulmi ba hakkokinsu da tabbatar da zaman lafiya. Ka ga kuma wannan taron ya shafi zaman lafiya. Idan zan gayyato baki daga waje su shigo, sai Nijeriya ta ce ba za su shigo ba, a matsayina na shugaban Izala ba zan iya fada ba in ce dole sai an bar su sun shigo.
Ashe kenan ina da bukatar shugaban Nijeriya a matsayinsa na shugaba domin ya ba ni hakkina na shugabanci da yake wuyansa. Saboda haka ni shugaban Nijeriya na gayyata, idan kuma ba shi ne shugaban Nijeriya ba a kawo mun wani.
Ko Malam zai yi mana karin bayani, shin taron nan na Afirka ne kadai ko an gayyato malaman duniya?
Taro ne na al’ummar Musulmin Nijeriya tare da sauran ‘yan’uwansu na kasahen Yammacin Afirka kuma mun gayyaci ofisoshin jakadanci masu alaka da addinin Musulunci saboda haka taro ne na al’ummar Musulmi. Yanzu misali, idan al’ummar musulmi na Kamaru suka kira taro, wane ne shugabansu? Wanda ya ke shi ne shugaban kasansu dole ne ya je walau Musulmi ne ko ba Musulmi ba. Haka nan a Togo.
Lokacin da za mu je taron Nijar, shugaban kasan ya ce a bude kan iyaka domin wanda ya ke kan kujerar Musulmi ne. Saboa haka, ko Musulmi ne ko ba Musulmi ba shugaba yana da hakki kuma dole ka ba shi. A matsayinmu na jagororin Musulmi ba mu jahilci hakkin kasa ba, ba mu jahilci duk abin da aka shimfida na ka’ida ba. Don haka, duk mai cewa taron na siyasa ne to wannan lissafinsa ne kawai.
Taronmu na al’ummar Musulmi ne, kuma ba shi ne na farko ba akwai wanda muka yi na programme dinmu ‘family in difficult circumstances support scheme 2011’ a nan National Moskue. Mun gayyaci kowa da kowa a Nijeriya, mun gayyaci shugaban kasa shi kuma ya aiko mana da mataimakinsa a matsayin wakili. Haka nan ma watakila zai faru a wannan karon, ko shugaban kasa ya turo mana mataimakinsa ko wani minister, mu dai Nijeriya muka gayyata.
Ka tabo batun masu aikata Bidi’a a farkon bayaninka, sannan an fi sanin Yarbawa da kide-kide ta fuskar addini, sai ga shi taron na su, ma’ana a garinsu za a yi. Mece ce hikimar yin hakan?
Ai taro ne na farko da muke neman abin da zai hada kan Musulmin Kudu da na Arewa. Muna yin wa’azi amma bakin mu Arewa, su ma suna yi amma bakin su Kudu, to bayan da muka yi tour ne sai muka ce mu yi comference na farko da za mu zauna mu tattauna. Comference na biyu kuma arewa za a kawo shi. Haka dai za a rika jujjuya abun.
Da muka ce Ahlus-Sunnah, ai Ahlus-Sunnah ba ‘yan Bidi’a ba ne, na fada ma akwai kungiyoyin Ahlus-Sunnah na Yarbawa da suka hadu suka kafa Federation of Ahlus-Sunnah of Nijeriya. Saboda haka duk wasu bidi’o’i da mutanensu suke yi su ma suna daga cikin masu yakar wadannan bidi’o’in.
duk wani taron kasa da muke yi ko wa’azi kullum suna zuwa, suna da wakilansu da suke turawa. Mu ne dai ba mu taba zuwa musu gabadaya haka ba. Sai dai idan sun yi wata gayyata mu tura musu mutum daya ko biyu, to amma yanzu bakidaya za mu je musu. Comference na farko na hadin kai ne, comference na biyu kuma ko dai mu yi shi a Abuja ko a Kaduna ko kuma wani wuri a Arewa.
Kuna kokarin tattara mabiya Ahlus-Sunnah a karkashin inuwa guda, kuma akwai kabilu daban-daban a ciki, shin wane harshe za ku yi amfani da shi a wannan taron?
Idan mun je kasar Yarbawa mafi yawa harshen da ya hada mu da su shi ne Turanci, mafi akasarinsu suna jin Turanci, don haka da shi za mu yi amfani. Sannan mutanenmu mazauna can da suke jin Hausa, su ma za a yi musu Hausan. Hakazalika za mu yi amfani da harshen Yarbanci, haka nan ma idan ya kama za mu yi da Larabci. Wannan shi ne abin da ya kamata.
Galibi Izala ta fi mayar da hankali ne wurin kira ga Musulmi su dawo kan hanyar da ta fi zama daidai, ba a kiran sauran wadanda ba Musulmi ba su zo su shiga, wane irin salo ko mataki za ku dauka wurin sauya alkiblar da’awarku?
Eh, wanda bai sani ba shi ne zai ce kungiyarmu ba ta kira ga wadanda ba Musulmi ba su zo su shiga Musulunci. Muna da sashi musamman na da’awa. Babu abin da ba a yi, mu kan tura masu wa’azi yankunan da babu Musulmi suna musu wa’azi tare da karantar da su addinin Musulunci har zuwa yankin Neja Delta.
Ina tabbatar maka akwai ‘yan Neja Delta mutum 11 da suka karbi Musulunci a yanzu haka ma suna Jami’ar Madina suna karatu. Haka nan muna shiga rugagen Fulani domin yi musu da’awa. Wuraren da ya kamata a kai musu magunguna kuma ana kaiwa ko wani tallafi.
Wa’azin kasa da muke Tarawa wannan muna haduwa ne mu yi don kara karfi tare da yin kira ga wadanda suke kiran kansu Musulmi a kan su daina hada al’ada da addini, mu hadu wuri guda. Amma akwai wani wurin ma da muka je muka yi wa’azi duk garin sai da suka musulunta, coci-cocinsu aka mayar da su suka zama masallatai. Don haka, kungiyar tana yin abubuwa da yawa.
 
A karshe, mene ne matsayinku dangane da sabon salon kisan malaman addini a kasar nan, musamman bisa la’akari da kisan da aka yi wa Sheikh Albani?
Babban matsayarmu a kai shi ne muna ta addu’a Allah ya tona asirin wadanda suke aikata haka da su da iyayen gidansu. Kuma wannan ba zai sa malaman addini su dakatar da wa’azozin da suke yi ba, domin sun san duk wanda ya tafi a irin wannan shahada ya yi. Domin aiki ne na da’awa. Shi ya sa muke kira ga mutanenmu a duk inda suke su dukufa ga addu’o’i Allah ya tona asirin masu yin haka.
Bayan haka, muna kira a rika bai wa maluma tsaro a masallatai da makarantu, don ba za mu zauna haka nan ba. Hakazalika, muna kira ga gwamnati ta gaggauta bincike ta fitar da sakamakon musabbabin kashe Malam Albani. Gwamnati ce ta ke da hakkin kiyaye jini. Duk lokacin da aka kashe wani, mutane su mike tsaye wurin neman sanin abin da ya kashe wannan mutumin domin hakkinta ne ta kiyaye musu.
Muna kira ga gwamnati ta gaggauta bincike tare da bayyana sakamako. Ba ma nashi ba kawai har da na Sheikh Ja’afar ba a ba mu sakamakon bincikensa shekaru da dama amma shiru ka ke ji. Wannan idan aka ci gaba da yin haka, ba zai kawo wa kasa alheri ba. Akwai wadanda suka yi maganar cewa za soma kashe manya idan ana fuskantar lokacin siyasa, kenan kin daukar matakin zai sa mu gaskata maganar.
Muna kira ga al’umma a koma ga Allah a yi ta yin addu’o’i, don idan ka ce ka dogara ne ma da jami’in tsaro, to shi kansa jami’in tsaron za ka ganshi yana boyewa a bayan buhun da ya sa masa yashi ko duwatsu. Yana rike da bindiga ne amma kuma tsoro ya ke ji. A dukufa ga yin addu’o’in da Annabi ya koyar, na tabbatar idan ana yi Allah zai tona asirin wadanda suke yin barnar. Allah ya ba mu zaman lafiya amin.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

5 responses to “Babu Alakar Siyasa Da Taronmu —Sheikh Bala Lau Shugaban Jibwis Ta Nigeria(Leadership Hausa)”
  1. Sani yunus Avatar
    Sani yunus

    ALLAH yakara hada mana kan ahlussunnah na nigeria dama africa baki daya..shugaba sheikh abdullahi balalau kuma ALLAH yaqara wuce masa gaba akan kokarin dayake….ameen thumma ameen

  2. Murjanatu salihu gulma Avatar
    Murjanatu salihu gulma

    Allah subhanahu wata’ala ya kare ahlissunnah a duk in da yake

  3. Ya ALLAH ka karbi rayuwarmu muna musulmi masu IMANI!

  4. Muhammad bin haidar Avatar
    Muhammad bin haidar

    Gaskiya ne

  5. ALLAH KA HADA KAN MUSULMIN DUNIYA ALLAH KABAMU ZAMAN LFY AQASACENMU ALLAH KABAMU SHUWAGABANNI NA GARI

Leave a Reply

Latest updates
Categories