ABUN FARINCIKI DAGA WA'AZIN LOKOJA! Kashi na (1)(Jibwis Nigeria)

·

·

TSARABA. Daga bayanan
shugaba.
Shugaba Shekh Abdullahi bala lau.
Yayikira ga dukkan musulmi da su
koma ga ubangi don neman tsira
aduniya da Lahira,
Hakika Allah ya Azurta wannan
wa’azi da’aka gabatar Da dumbin
malamai na Addinin musulunci
daga wuri daban-daban . Tareda
da Alarammomi mahaddata
Alqur’ani sama da mutum Arba’in
Akwai qabilu dadama dawannanne
yasa akagabatar da wa’azi da
yaruka daban daban. Hakika Allah
ta’ala ya tara Al’umma masu
dumbin yawa da sukazo don jin
sakon Allah
Sannan shugaba yayi kira ga
kiristocin nigeria da yanki yanki da
mukedasu. Da suzo su shiga cikin
Addinin musulunci don samun tsira
agobe kiyama. Yashaidawa
dukkan Alumma da suke kasarnan
cewa kungiyar Izal tasuce.
Iyamurai, yarbawa, hausa fulani,
da dukkan qabilu da mukedasu
Afadin kasarnan.
Sannan shugaba ya hakaitomana
wasu nasarori da Akasmu yayin
ziyar da sukakai na wasu dalibai
sannan ya shaidawa Al’umma
cewa daga cikin Daliban akwai
wadanda zasu kawosu kasarnan a
watan ramadan don bada
gudumawarsu.
Yace wannan mimbari na dukkan
yan’uwa Ahlussunnanh ne.
sannan shugaba ya sake hakai
tomana Nasarorin da Sunnah tibi
yakesamu. Wanda yashige cikin
gidajen Manyan kasannan.
SUNNAH TV
SUNNAH RADIO
SUNNAH HOSBITAL
SUNNAH PHARMACY
SUNNAH UNIVERSITY
ALLAHU’AKBAR. Shugaba yace
damu daku zamu hadu muyi Insha
Allahu. Kuitamana Addu’a muma
muna muku.
Sannan shugaba yayi kira ga
Al’umma da suyi riko da Azkar
ma’ana. (ISTIGFARI) Tare da fadin
(Hasbunallahu wani’imal wakil)
shugaba yacigaba dacewa kashe
rayuka awannan lokaci yayiwa.
sannan ya’irgo wasu dagacikin
garuruwa da akayi ta kashe
rayukar musulmi. Shugaba yace
Abubuwan da zasu canza wannan
Al’amari.
Shine komawa zuwaga Allah tare
da Adalcin shuwagabanni.
Yacigabadacewa. Kisan rai
bakaramin jefa mutum yakeyi cikin
Bala’i ba, sannan yakawo ayar
Alqur’ani. Inda Alla yake cewa
WAMAN YAQUTUL MU’MINAN
MUTA’AMMIDAN… ………………..
Sannan shugaba yaba da umarnin
ga Dukkanlimamai da su kama yin
(ALQUNUT) adukkan masallatai na
Ahlussunna . Dake fadin kasarnan.
Bakuma za’adaina ba har zuwa
ramadan.
Sannan Shugaba yayikira ga
dukkan yan’uwa da suke harkan
fcb. Cewa banda zagi banda
maganganu na batanci. Mudinga
rubuta Abun da zai amfanar da
musulunci da musulmai.
Sannan yasanar da frogram da
muke dasu kafun ramadan
musmman taro na Yan’agaji.
Wanda za’agabatar za’abasu horo
tareda tsari da gaiyyoto wasu
kungiyoyi da wasu jami’ai wanda
Aikinsu yakeda Alaka dawannan.
Don basu horo.
Sannan shugaba yacigaba dacewa
Insha’allahu kungiyar izala tananan
Ahade ba rabewa har ila yaumil
kiyama. Yasake maimaita kiran da
yayi a jos. Ga Shugaban majalisar
Malamai.
Bayan zaman da shugabanni
sukayi wanda yahada dukkan
shuwagabannin jahohin kasarnan
sukanemi wanene wakilinsu na
matimakin shugaban malamai?
Sanan shuwa gabanni na kololuwa
Sukayi matsaya kan cewa mun
janye wakilinmu na mataimakin
Shugaban majalisr malamai.
Sannan kuma haduwa tagaba
Zakuji wayene wakilinmu A
wannan matsayin. Sannan
shugaba yace kowanene yayi
badaidaba Za’adaumataki ko
shine. Allahu’akbar Allah kataimaki
shuwagabanninmu ka basu karfin
gwuiwa. Adukkan harkokinsu.
Ameeen.

16 responses to “ABUN FARINCIKI DAGA WA'AZIN LOKOJA! Kashi na (1)(Jibwis Nigeria)”
 1. Musa Sa'ad Avatar
  Musa Sa’ad

  ya Allah kayi mana jagora, kabamu ikonyi dominka.

 2. Abdullahi mohammed dabai Avatar
  Abdullahi mohammed dabai

  Allah ya saka da alkairi ameen

 3. usman isa el-yazaki, kwandare Avatar
  usman isa el-yazaki, kwandare

  Allah ka kara hada kan mu Ahlisunnah baki daya

 4. musa hamid Avatar
  musa hamid

  Allah kakara hadakan ahlusnnah na duniya gabadiya,ameen

 5. Nura Lawal Dankama Avatar
  Nura Lawal Dankama

  correct your english It is Hospital not Hosbital

 6. Asdalamu alaikum wannan qungiya mai albarka muna mata fatan alhairi allh ya qara taimakawa malamammu da alkairi

 7. Abdullahi safiyanu Avatar
  Abdullahi safiyanu

  Alhamdu lillah’

 8. Alhassan abubakar Avatar

  Allah yataimaki wanda yake turn wanna

 9. Usman Isa El-yazaki Avatar
  Usman Isa El-yazaki

  Sunnah muke so

 10. Hassanat u.k Avatar

  Allah yaqara taimakon qungiyar nan d malamanta yqaramusu ilmi da fahimta amin

 11. alameen adam Avatar
  alameen adam

  ALLAH ya sakama M IBRAHIM JALO JALINGO da alkhairi akan wannan bayanin sakamakon bincike da sukayi akan wannan allurar polio .
  Ina fatan ALLAH yasa sun dace akan binciken kuma ALLAH yasa dukkan musulmi suji wannan kiran. amin

 12. Yusuf musa Avatar

  ALHAMDULILLAH MASHA ALLAH.

 13. Habibu Haruna Avatar
  Habibu Haruna

  Allah ya kara hade kan al-umar musulmai baki daya,ya kara soyayya a tsakaninmu,Allah ya taimaki shugaba ya tsareshi daga sharrin masu sharri,dashi da ‘yan majalisarsa da sauran musulmai…amiin.

 14. Muhammad chigari kumo Avatar
  Muhammad chigari kumo

  Allah yaa bada nasara kan aiyukan da ake gabatarwa

 15. MUSA ABDULLAHI RANO Avatar
  MUSA ABDULLAHI RANO

  Allah yakarbi ibadammu ya yafemana laifukanmu gaba daya

 16. Allah yataimaki musulmai ya kuma daukaka addinin musulunci amin

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: