Ko Kasan Daga Ina Aka Gano Maukibi?(Sheikh Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Ko Kasan Daga Ina Aka
Gano Maukibi?
Duk da cewa duk mai
hankali ya san cewa
taron maukibi da yan
darikar Kadiriyya suke fita a Kano duk shekara-
shekara zuwa
makabarta, tare da kide-
kide da raye-raye, a
cakude maza da mata,
ba addini ba ne, wannan ba zai hana mu kara
wayar da kan mutane
ba, idan ka duba littafin
da wani dan kadiriyya
mai suna Alhaji Ibrahim
Isa Makwarari ya rubuta mai suna : “Maukibin
Kadiriyya, Tarihinsa,
Nasarorinsa, da
Matsalolin da ya gamu
da su” zaka ga inda yake
fadin asalin inda Ma Nasiru Kabara ya gano
Maukibi. Ga abin da yake
fada a shafi na 42 – 43
“An fara gudanar da irin
wannan taro ne na
maukibi a nan Kano a shekarar 1951 bayan
dawowar Sheikh
Muhammad Nasiru
Kabara daga kasashen
Bagadaza da Tunis da
Masar, inda ya ziyarci manyan mukaddamai da
khalifofin darikar
kadiriyya, kuma ya samo
ijazar shugabanci daga
gidan shehul sajjada
Muhammad Tahir khalifan Sidi Abdulkadir
Jilani na wannan
lokaci…Komawar malam
ke da wuya sai ya sanar
da sahabbansa ya kuma
gabatar musu da abin da ya gano a duniya na
yadda Kadirawa suke
bikin tunawa da Sidi
Abdulkadir jilani a duk
ranar goma sha daya ga
watan Rabi’u Thani na kowacce shekara, nan
take sauran
mukaddamai suka yi
na’am kuma aka
kaddamar da yin irin
wancan taro na Maukibi”.
To dan uwa ka ji inda
Maukibi ya samo asali,
kuma ka ga shekarar da
aka fara shi 1951, yanzu
don Allah wannan abu ya zama addini??.

4 responses to “Ko Kasan Daga Ina Aka Gano Maukibi?(Sheikh Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)”
 1. Nura Lawal Dankama Avatar
  Nura Lawal Dankama

  Minene aibinshi? Ko akwai aya ko hadisin da yayi hani da maukibi?

 2. Garba Abdullahi Avatar
  Garba Abdullahi

  MALAM NURA LAWAN… GA AMSARKA, MENENE MATSAYIN ABINDA AKA QIRQIRA AKA SASHI CIKIN ADDINI A MATSAYIN IBADA WANDA BASHI DA ASALI CKIN ADDININ?

 3. yusuf Avatar

  hmmm ma Rabiu kasake dubawa karkasa baki akan abun da baka da ilmi akai

 4. salisu Avatar
  salisu

  kai jahili kaje kayi karatu kafin ka shiga rigimar addini.baka san komai ba.mudai baza muyi izala ba. ka mayar musu da kudinsu mu muna layin shugaba .kai dai kaje kayi munafuncinka.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: