Batanci Wa manzon Rahama(Dr umar sani Rijiyar Lemo)

Danna nan domin shiga karatu Online

BATANCI GA MANZON RAHMA
(S.A.W): GASKIYAR LAMARI
Allah Ta’ala yana cewa a cikin
littafinsa mai tsarki: (kamar haka ne
muka sanya wa duk wani annabi
abokan adawa daga shaidanun
mutane da aljannu….). Al-An’am
aya ta112 Ya kuma cewa: (kamar
haka ne muka sanya duk wani
annabi abokan adawa daga cikin
masu manyan laifuka..). Al-Furqan
aya ta 31 Ya sake cewa a wani
gurin: (Kamar haka ne, ba wani
manzo da ya zo wa wadanda suke
gabaninsu face sun ce, matsafi ne
ko mahaukaci). al-Zariyat aya ta
52.
Duk wani da yake karanta al-
Kur’ani yake kuma fahimtarsa,
sannan kuma ya san sirar
annabawa, tun daga kan Annabi
Nuhu (A.S) har zuwa Annabin
rahma (S.A.W) to ba zai taba wani
mamakin jin cewa makiya Allah da
Manzonsa (S.A.W) sun ci zarafinsa
ba. Domin Allah ya fada mana
cewa haka abin yake tun farkon
tarihin annabci a doron kasa, har
zuwa cikamakin annabawa
(S.A.W).
Ni mamakin da nake yi shi ne na
musulmin da za su rika mamakin
faruwar hakan,, kamar ma ba su
karanta Al-Kur’ani ko ba a karanta
musu shi suna saurara. Allah ya
riga ya fadi cewa hakan zai yi ta
faruwa, kuma shin akwai wanda ya
fi Allah gaskiyar magana?! Babu.
Sirar rayuwar Annabin Rahma
(S.A.W) ta gwada mana yadda
makiyan musulunci na farko suka
yi ta masa kazafi iri-iri, suka ce
masa “marar hankali” ko “boka” ko
“matsafi” ko “mawaki”, d.s. kamar
yadda ayoyi dadama a cikin al-
Kur’ani suka karantar da mu.
Bayan wanan yahudawa da turwa
‘yan ci ranin addini (Orientalists)
suka ci gaba da irin wannan salo
na cin mutuncin manzon Allah
(S.A.W) da musulunci a cikin
littattafansu da rubuce-rubucensu.
Duk wanda ya san wani abu akan
wannan ta’asar ta su ba zai kasa
tuno makiya Annabin rahma
(S.A.W) ba irin su: – Henri
Lammens (1862-1937) marubucin
nan dan kasar Belgium. – Carl
Brockelmann (1868-1953)
mutumen Jamus (German). –
Rymond Charles (?) dan kasar
Faransa (France). – Gustave
Edmund Von Grunbum
(1909-1972) dan kasar Austria. har
ka gangaro zuwa ga irin la’annan
dan Buritaniya din nan dan aslalin
Indiya, Salman Rushdie. Duk
wadannan da ire-irensu da yawa
sun yi rubuce-rubuce masu yawa,
cike da zage-zage da kazafi da
karerayi ga Manzo Rahma (S.A.W)
. Don haka babu wani abin mamaki
don sun koma ga yin amfani da
hayoyin sadarwa na zamani da
amfani da hanyar nishadantarwa ta
fina-finai su rika isar da mugun
nufinsu da la’ananniyar manufarsu.
GAME DA SABON FIM DIN
BATANCI: Dangane da la’anannen
Fim din batanci da ya fito a kasar
Amuruka an yi shi ne don wata
mummunan manufa wacce ba a
bayyanta ba, amma duk wanda ya
lura da wadanda aka yi amfani da
su da wadanda suka jagoranci
hada Fim din da tallata shi zai
fahimci wannan boyayyar bakar
manufar da ake son cimma.
La’anannun da suka jagoranci
wannan Fim din sun hada da Moris
Sadiq wani tanbatstssen kiristan
kasar Masar dan kabilar Qibdawa
Marasa yawa a kasar. Shi wannan
la’ananne dan taliki, kwanakin
baya can wata kotu ta kasar Masar
ta zartar da hukuncin korarsa daga
zama dan Masar, saboda laifuffuka
manya-manya da aka same shi da
su. Shi ne yake kira da lalle a raba
kasar ta Masar biyu tsakanin
musulmi da ‘yan tsirarin kiristan
Qibdawa. Sannan yake mika kokon
bararsu ga daular Banu Isra’la da
cewa ta shiga Masar da yaki don ta
ceci Qibdawa daga hannun
musulmin masar.
Sannnan da tsinannen Faston nan
Jerry Jonse mazaunin Florida ta
kasar Amuruka wanda a shekar
(2010) ya yi barazanar zai kona al-
Kur’ani a cocinsa. Shi ne wanda ya
fara tallata Fim din a cocinsa tun
kafin nuna shi a gidajen silima.
Baya ga wadannan sai wanda ya
dauki nauyin Fim din kuma ya yi
director na Fim din, Sam Bacile
wani bayahuden Amuraka. Ya ce
ya kashe dalar amuruka milyan 5
da ya samo daga wasu yahudawa
100 don shirya wannan
kazamtaccen Fim na shi.
Boyayyen manufar da aka so a
cimma ita ce, haddasa tarzoma da
tashe-tashen hankula a kasar ta
Masar bayan an ga ta fara fita
daga mulkin danniya da kama-
karya da ta dade a cikinsa shekaru
masu yawa, karkashin jagorancin
‘yan barandan Yahudu da Turai.
An yi zabe kuma wadanda ake
ganin cewa masu kishin muslunci
ne sun lashe zaben. To shi ne ake
son a samu hanyar da kasar za ta
hargitse a shiga kashe-kashe da
kone-konen dukiyoyi. Aka yi amfani
da Qibdawa mazauna Amuruka
wajen tsara wannan la’anannen
Fim din, sannan aka fassara
turancin da aka yi amfani da shi
zuwa larabci na Masar. Ka ga idan
Musulmin kasar Masar suka gani
sai su harzuka su aukawa
Qibdawa da kisa da kone-kone.
Daga nan ne kuma sai sojoji
wadanda ake zargi da marawa
tsohuwar gwamnati baya su fito su
yi juyin mulki su kama malamai da
masu addini su daure da hujjar
dawo da zaman lafiya a kasa. To
ka ga hakansu ya cimma ruwa ke
nan. To amma inda Allah ya nuna
musu ikonsa sai su mutanen
Masar suka farga da wuri, su
kansu Qibdawan suka fito fili suka
yi Allah wadai da tofin-Allah-tsine
ga wannan la’annen Fim, sannan
suka fito cikin ‘yan zanga-zanga
tun a karon farko don nuna rasahin
amincewarsu da wannan Fim.
Kongiyoyin Qibdawa sama da 120
mazauna Amuruka da turai suka
fitar da bayanan Allah wadai ga
wannan Fim da masu shi. Wannan
ya taimaka kwarai wajen dakile
mummunar manufar da musu
wannan Fim suka shirya.
ME YA KAMATA MU YI: Babu
shakka manyar makiyan musulunci
na Duniya sun fahimci irin girman
da Manzon Allah (S.A.W) yake da
shi a zukatan musulmin Duniya tun
lokacin da Shedan Salman
Rushdie ya rubuta Ayoyin
shedaninsa. Sun kula da yadda
musulmi suka nuna damuwarsu da
bakin cikinsu. Don haka sai suka
fahimci cewa duk lokacin da suke
son tayarwa da musulmi hankali a
Duniya to babu abin da za su yi
kamar irin wannan cin zarafin. To
sukan yi farin ciki matuka su ga
sun tashi hankalin musulmi, ana
kashe-kashe da kone-kone, ba a
kasashensu ba, a’a a kasashen su
musulmin, tsakaninsu da wadanda
suke zaune tare da su, wadanda
su ma labari suka ji kamar kowa.
Ba su suka yi ba, kuma ba su fito
sun goyi baya ba.
Bayahude da Bature a yau ba su
da wata damuwa don an kashe
kowane ne, a ko ina ne, idan har
za su cimma wata kazamar
manufarsu, kamar yadda Amuruka
ta yi sa’adda ta kashe jakadanta
na kasar Pakistan don ta cimma
burinta na kashe Dhiya’ul Haq
shugaban Kasar Pakistan wanda
take zargi a lokacin da kishin
Mujahidun na kasar Afganistan a
shearer 1988. Don haka babban
abin da ya kamata mu yi shi ne:
1- Mu kara imani da yakini da cewa
Allah ta’ala shi ne ya aiko da
Annabinsa da shiriya da addinin
gaskiya don ya ba shi rinjaye a kan
kowane addini ko da kafirai ba sa
so. kamar yadda ya yi alkawari a
cikin suratul Taubah aya ta 33, da
Fath aya ta 28, da Saf aya ta9
Kuma Annabi (S.A.W) ya ce: (Lalle
wannan addini sai ya shiga duk
wani guri da dare da rana suka
shiga. kuma Allah ba zai bar wani
gida na yunbu ba ko na gashi face
ya shigar da shi wannan addini, da
izzar mai izza, ko kaskanci mai
kaskanci, izzar da Allah zai
daukaka musulunci da ita, da
kaskancin da zai kaskanta kafirci
da shi) Ibn Hibban.
2- Mu dage wajen koyi da halayen
Manzon Allah da kankamewa
koyarsa da aiki da sunnarsa a
al’amuran addininmu da
rayuwarmu. Wannan zai kara cusa
hashi da baki ciki da damwa a
zukatan masu son su raba mu da
addininmu. 3- Yin aiki matuka
wajen fito da tarihin Manzon Allah
da kyawawon halayensa da
dabi’unasa da rahamarsa, don
wadanda ba a so su san hakikanin
wanene Annabi Muhammadu
(S.A.W) su sani… Wanda ake yin
wannan batanci gareshi, don a
hana musu fahimtar hakikaninsa, a
haramta musu shiga cikin hasken
da ya zo da shi Duniya. 4- Mu koya
‘yayanmu da iyalanmu sirar
Manzon Allah (S.A.W) da
sahabbansa domin ya zamana su
tashi da ganin girmansu da
martabarsu, wanda hakan zai ba
su kariya daga duk wani kokari da
mikaya za su yi don su bata su a
idanunsu, su rabu da sonsu a
zukatansu.
Dan uwanku Muhammad Sani
Umar R\Lemo.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

6 responses to “Batanci Wa manzon Rahama(Dr umar sani Rijiyar Lemo)”
  1. Allah ya taimaki malam yasaka da alkhairi Ameen.

  2. umar isa Avatar

    Assalamu alaikum. alhamdulillah mallam ALLAH ya saka da alkairi. amma ga wata shawara, ba yahudawa da nasara kadai ke batanci ga manzon ALLAH (saw) ba, akwai har acikin musulmai masu batanci ga annabin tsira kamar su ibn taimiyya da da mukarraban sa harda masu bin koyarwansa wato yan izala. ibn taimiyya yayi batanci ga iyalen ma’aiki har ya kai ga cewa nana khadija jahila, nana fatima makaudaiciya mai fushi dan duniya sayyidina ali imaninsa bai ingantaba, akarshe yacae ALLAH ya jarabci manzonsa da sabo wa iyazubillahia. ayau ire-iren wanan munana na fitowa daga bakin yan izala har sun kai da gano cewa iyayen annabi na wuta. suna dogaro da hadsin hammadu mahaukaci, to mallam daurawa sukuma wadanan yan uwan naka wani mai zakace masu ko su yabon annabi suke

    1. Abdullahi Suleiman Avatar
      Abdullahi Suleiman

      Allaah Ya shirya ka akan abinda ka fada akan haqiqanin masoyin manzon Allaah Wato Ibn Taimiyya. Ka fadi A wane littafi shafi Na nawa??

    2. Muhammad usman kolo Avatar
      Muhammad usman kolo

      Sai kafadi inda kagani kuma wani littafine kuma shafinanawa

  3. Musa Ahmad Avatar
    Musa Ahmad

    Dan Allah malan ina neman karin bayani gameda falalar karanta Suratul kahfi ranar Juma’a. Jazakumullahu khair

  4. Bashir abubakar rijiyar lemo Avatar
    Bashir abubakar rijiyar lemo

    Don allah malam inada tambaya naje screening na soja lokacin azumi ya halatta na sauke azumina? nagode

Leave a Reply

Categories
Latest updates