Baya halatta mutum ya nemi ya mutu sabida wata cuta da ta sameshi

Danna nan domin shiga karatu Online

Anas Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

لا يَتَمَنَّيَنَّ أحَدُكُمُ المَوْتَ مِن ضُرٍّ أصابَهُ، فإنْ كانَ لا بُدَّ فاعِلًا، فَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ أحْيِنِي ما كانَتِ الحَياةُ خَيْرًا لِي، وتَوَفَّنِي إذا كانَتِ الوَفاةُ خَيْرًا لِي

البخاري: ٥٦٧١

Kada wani daga cikinku yayi kwaɗayin mutuwa sabida wata cuta da ta auka masa, inya zamto babu yadda ya iya sai yayi toh yace: Allah ka rayani in ya zamto rayuwar itace tafi alheri gareni, ka kuma kasheni in ya zamto mutuwa itace tafi alheri a gareni.

Bukhari: 5671

Wannan hadisi na hani ga Musulmi ya ɗebe tsammani daga rahamar Allah har hakan ya kaishi ga kwaɗayin mutuwa, a kullum mutum ya zamto mai haƙuri da kuma Sallama komai zuwa ga Allah, idan yayi haka Allah zai sama masa mafita, sannan kuma zai samu lada mai girma ranan tashin Al-Qiyama. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates