BAYANI A KAN BUKIN MAULIDI KASHI NA DAYA: (1)(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga karatu Online

Yau Juma’a 2/3/1435 H 3/1/2014 M
tsakaninmu da ranar goma sha biyu
ga watan Rabii’ul Awwal kwana 10 ne
kacal, sannan kamar yadda aka sani
ne cewa wannan rana ta 12/3/ ita ce
ranar da wasu daga cikin masu
ikirarin Musulunci ke bukin ranar
haifuwar Annabi Muhammad mai
tsira da amincin Allah cikinta saboda
neman lada da falala a wurin Allah,
duk kuwa da cewa rikon wannan rana
a matsayin Idi bidi’a ce wurin dukkan
Maluman Musulunci! Allah Sarki!
Haka dai Shaidan yake badda mutane
cikin mamaki wani lokaci! Allah
Madaukakin Sarki yana cewa cikin
Suratu Faatir aya ta 8:-
(( ﺃﻓﻤﻦ ﺯﻳﻦ ﻟﻪ ﺳﻮﺀ ﻋﻤﻠﻪ ﻓﺮﺍﻩ ﺣﺴﻨﺎ ﻓﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ
ﻳﻀﻞ ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻭﻳﻬﺪﻱ ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻓﻼ ﺗﺬﻫﺐ ﻧﻔﺴﻚ
ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺣﺴﺮﺍﺕ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻢ ﺑﻤﺎ ﻳﺼﻨﻌﻮﻥ )).
Ma’ana: ((yanzu wanda aka kawata
masa mummunan aikinsa har ya gan
shi wani abu Mai kyau “yana daidai
da waninsa?” saboda haka lalle Allah
yana batar da wanda yake so, kuma
ya shiryar da wanda yake so, kada
ranka ya halaka a kansu saboda
bakin ciki. Lalle Allah Masani ne ga
abin da suke sana’antawa)).
Ni a nan, a bisa dogara da ayah ta
104 a cikin Suratu Ali Imrana inda
Allah Madaukakin Sarki Ya ce:-
(( ﻭﻟﺘﻜﻦ ﻣﻨﻜﻢ ﺃﻣﺔ ﻳﺪﻋﻮﻥ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻭﻳﺄﻣﺮﻭﻥ
ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ﻭﻳﻨﻬﻮﻥ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ
ﺍﻟﻤﻔﻠﺤﻮﻥ )).
Ma’ana: ((A samu wata al’umma
daga cikinku da za ta yi kira zuwa ga
alheri, sannan ta umurni da abin da
Shari’ah ta sani, kuma ta yi hani ga
abin da Shari’ah bata sani ba. To su
wadannan Al’umma sune masu
rabauta)). Da kuma dogara kan aya
ta 78, da 79 cikin Suratul Maa’idah
inda Allah Madaukaki ya yi maga a
kan Banuu Isaraa’iil ya ce:-
(( ﻟﻌﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﺍﺳﺮﺍﺋﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﻟﺴﺎﻥ
ﺩﺍﻭﺩ ﻭﻋﻴﺴﻰ ﺍﺑﻦ ﻣﺮﻳﻢ ﺫﻟﻚ ﺑﻤﺎ ﻋﺼﻮﺍ ﻭﻛﺎﻧﻮﺍ
ﻳﻌﺘﺪﻭﻥ . ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻻ ﻳﺘﻨﺎﻫﻮﻥ ﻋﻦ ﻣﻨﻜﺮ ﻓﻌﻠﻮﻩ ﻟﺒﺌﺲ
ﻣﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻔﻌﻠﻮﻥ )).
Ma’ana: ((An la’anci wadanda suka
kafirta daga Banu Isaa’iil a bisa
harshen Daawuuda da Isa Dan
Maryam, saboda irin yadda suka yi
sabo, suka kasance suna ketare
iyaka. Suka kasance ba sa hana juna
yin mummunan aikin da suke
aikatawa. Wallahi abin da suka
kasance suna aikatawa ya yi muni)).
Intaha. Da kuma dogara kan hadithin
da Imam Muslim ya ruwaito hadithi
na 49 inda Annabi mai tsira da
amincin Allah yake cewa:-
(( ﻣﻦ ﺭﺃﻯ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﻨﻜﺮﺍ ﻓﻠﻴﻐﻴﺮﻩ ﺑﻴﺪﻩ ﻓﺎﻥ ﻟﻢ
ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻠﺴﺎﻧﻪ ﻓﺎﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻘﻠﺒﻪ ﻭﺫﻟﻚ
ﺍﺿﻌﻒ ﺍﻻﻳﻤﺎﻥ )).
Ma’ana: ((Wanda duk ya ga munkari
daga cikinku sai ya jirkita shi da
hannunsa, in kuma ba zai iya ba, sai
ya jirkita shi da harshensa, in kuma
ba zai iya ba sai ya jirkita shi da
zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin
Imani)). Intaha. Da kuma dogara kan
maganar Sahabin Annabi Abdullahi
Dan Mas’ud Allah ya kara masa
yarda, wacce ta zo cikin littafin Ibnu
Wadh,dhah shafi na 11 da littafin
Ali’itisaam na Imamush Shaatibii
1/107 inda ya ce:-
(( ﺍﺗﺒﻌﻮﺍ ﻭﻻ ﺗﺒﺘﺪﻋﻮﺍ ﻓﻘﺪ ﻛﻔﻴﺘﻢ )).
Ma’ana: ((Ku bi -abin da Annabi ya
zo da shi- kada ku kirkiri bidi’ah,
domin an gama muku kome -na
addini-)). Dankuma dogara har yanzu
a kan maganar shi Sahabi Abdullahi
Dan Mas’uud wacce ta zo cikin
littafin Ibnu Wadh’dhah shafi na 11
da kuma Sunanud Daarami 1/68-69
a inda ya ce lokacin da ya wuce wani
mai wa’azi a cikin masallaci yana ce
wa mutane: ku yi Subhanallah kafa
goma, ku yi la’laha illalah kafa goma,
sai ya ce da su:-
(( ﻭﻳﺤﻜﻢ ﻳﺎ ﺃﻣﺔ ﻣﺤﻤﺪ ﻣﺎ ﺍﺳﺮﻉ ﻫﻠﻜﺘﻜﻢ ! ﻫﺆﻻﺀ
ﺻﺤﺎﺑﺔ ﻧﺒﻴﻜﻢ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﺘﻮﺍﻓﺮﻭﻥ
ﻭﻫﺬﻩ ﺛﻴﺎﺑﻪ ﻟﻢ ﺗﺒﻞ ﻭﺃﺗﻴﺘﻪ ﻟﻢ ﺗﻜﺴﺮ ﻭﺍﻟﺬﻱ ﻧﻔﺴﻲ
ﺑﻴﺪﻩ ﺍﻧﻜﻢ ﻟﻌﻠﻰ ﻣﻠﺔ ﻫﻲ ﺃﻫﺪﻯ ﻣﻦ ﻣﻠﺔ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻭ
ﻣﻔﺘﺘﺤﻮﺍ ﺑﺎﺏ ﺿﻼﻟﺔ . ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻳﺎ ﺃﺑﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﻣﺎ
ﺍﺭﺩﻧﺎ ﺍﻻ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻗﺎﻝ ﻭﻛﻢ ﻣﺮﻳﺪ ﻟﻠﺨﻴﺮ ﻟﻦ ﻳﺼﻴﺒﻪ ﺍﻥ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺍﻥ ﻗﻮﻣﺎ
ﻳﻘﺮﺀﻭﻥ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻻ ﻳﺠﺎﻭﺯ ﺗﺮﺍﻗﻴﻬﻢ ﻭﺍﻳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﺍﺩﺭﻱ
ﻟﻌﻞ ﺍﻛﺜﺮﻫﻢ ﻣﻨﻜﻢ ﺛﻢ ﻭﻟﻰ ﻋﻨﻬﻢ )).
Ma’ana: ((kaitonku ya ku al’ummar
Muhammad mamakin saurin
halakarku! Wadannan Sahabban
annabinku ne mai tsira da amincin
Allah ga su nan da yawa, wadannan
tufafinsa ne ba su gama yagewa ba,
wadannan butocinsa ne ba su gama
fashewa ba. Ina rantsuwa da Wanda
raina yake hannunsa lalle ne ku ko
dai kuna kan wani addini ne da ya fi
addinin Muhammad shiriya ko kuwa
ku masu bude kofar bata ne. Sai
suka ce wallahi baban Abdurrahman
babu abin da muke nufi sai alheri.
Sai ya ce ai da yawa mai son alheri
ba zai taba samun sa ba. Lalle
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah ya gaya mana cewa akwai wasu
mutane da za su rika karanta
Alkur’ani amma kuma ba zai wuce
makogoronsu ba, Ina rantsuwa da
Allah watakila mafi yawansu daga
cikinku suke. Daga nan sai ya juya ya
bar su)). Intaha. Da kuma dogara kan
maganar babban Taabi’ii Hasanul
Basarii wacce ta zo cikin littafin Ibnu
Wadh’dhah, da littafin Alitisam na
Shaatibii 1/111 inda ya ce: ((Mai yin
bidi’ah ba zai Kara kokari cikin
azuminsa na bidi’ah ba, ko sallarsa
ta bidi’ah ba, face hakan ya nisantar
da shi daga Allah)). Intaha.
Dogara kan wadannan ayoyi da
hadithai da maganganun Sahabbai da
Taabi’ai da kuka ji su yanzu ne ya sa
muke gargadin Al’ummar Musulmi,
muke hana su rikon ranar haihuwar
Manzon Allah Mai tsira da amincin
Allah a matsayin ranar Idi, muke
musu gargadin rikon bukin maulidi a
matsayin wani abu na addini da ake
neman lada da shi a wurin Allah
Madaukakin Sarki!
Saboda abu ne tabbatacce wurin
Maluman Musulunci cewa Annabi
Mai tsira da amincin Allah bai yi
bukin maulidi ba, Sahabbai ba su yi
bukin maulidi ba, Taabi’ai ba su yi
bukin maulidi ba, Taabi’ut Taabi’in ba
su yi bukin maulidi ba. Duk kuwa
abin da ba zama addini ba a zamanin
Sahabbai, da Taabi’ai, da Taabi’ut
Taabi’in tare da kasancewar sababin
yin sa a lokacin nasu’ da kuma ikon
yin sa daga gare su yana nan’ amma
kuma babu Wanda ya yi shi daga
cikinsu, to lalle wannan abin babu ta
yadda za a yi ya zamanto addini
karbabbe a wurin na bayansu har
zuwa tashin Kiyama.
Yan’uwa Musulmi! Lalle shi rikon
ranar maulidi a matsayin Idi, da
maida shi ranar buki, ba a fara yin
shi ba cikin wannan Al’umma sai
cikin karni na hudu na hijirar Annabi
Mai tsira da amincin Allah’ watau sai
a cikin shekara ta dari uku da settin
da biyu (362). Sannan mutumin da
ya fara yin wannan buki na maulidi
shi ne wani sarki dan Shi’ah
Fadimiyyah Mai suna Almu’izzu li
Dininl Lah a garin Alkahira’ kamar
yadda yake rubuce cikin littattafan
Musulunci da tarihi, da wasunsu,
kuna iya duba wadannan littattafan:-
ﺍﻟﻤﻮﺍﻋﻆ ﻭﺍﻻﻋﺘﺒﺎﺭ ﺑﺬﻛﺮ ﺍﻟﺨﻄﻂ ﻭﺍﻻﺛﺎﺭ ﻟﻠﻤﻘﺮﻳﺰﻱ
١ / ٤٩٠، ﻭﺻﺒﺢ ﺍﻷﻋﺸﻰ ﻓﻲ ﺻﻨﺎﻋﺔ ﺍﻹﻧﺸﺎﺀ
ﻟﻠﻘﻠﻘﺸﻨﺪﻱ ٣ / ٤٩٨، ﻭﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻻﺣﺘﻔﺎﻝ ﺑﺎﻟﻤﻮﻟﺪ
ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻟﻠﺴﻨﺪﻭﺑﻲ ﺹ٦٩، ﻭﺃﺣﺴﻦ ﺍﻟﻜﻼﻡ ﻓﻴﻤﺎ
ﻳﺘﻌﻠﻖ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺒﺪﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﻟﻤﺤﻤﺪ ﺑﺨﻴﺖ
ﺹ٤٤، ٤٥، ﻭﺍﻟﻤﺤﺎﺿﺮﺍﺕ ﺍﻟﻔﻜﺮﻳﺔ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻋﻠﻲ
ﻓﻜﺮﻱ ﺹ٨٤، ﻭﺍﻹﺑﺪﺍﻉ ﻓﻲ ﻣﻀﺎﺭ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﻉ ﻟﻠﺸﻴﺦ
ﻋﻠﻲ ﻣﺤﻔﻮﻅ ﺹ١٢٦، ﻭﺍﻟﺘﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻌﺒﺎﺳﻲ ﻭﺍﻟﻔﺎﻃﻤﻲ
ﻟﻠﺸﻴﺦ ﺍﺣﻤﺪ ﻣﺨﺘﺎﺭ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﻱ ﺹ٢٦١، ٢٦٢ .
Almawaa’izu wa Litibaar na Maqriizii
1/490, da Subhul A’ashaa na
Qalqashandii 3/498, da Taariikhu
Lihtifaali Bil Maulidin Nabawii na
Sanduubii shafi na 69, da Ahsanul
Kalam fi ma yataallaqu bis Sunnati
wal Bidi’ati minal Ahkam na
Muhammad Bakhiit shafi na 44,45,
da Almuhadharaatul Fikriyyah na Ali
Fikrii shafi na 84, da Al’ibdaa fi
Madharri Libtidaa na Ali Mahfuuz
shafi na 126, da Taarikhul Abbaasii
wal Faatimii na Ahmad Mukhtaar
Al’abbadii shafi na 261,262.
MALUMAN MUSULUNCI DABAN
DABAN SUN HANA YIN BUKIN
MAULIDI:
Yan’uwa Musulmi! Lalle da yawa
daga cikin maluman Musulunci sun
gargadi Al’umma sun hana su yin
bukin maulidi da rikon shi a matsayin
wata ibadah da za a nemi lada wurin
Allah da ita, kuma sun bayyanar da
cewa yin bukin maulidi bidi’a ce
kuma bata.
Daga cikin wadannan malamai akwai
manya manyan malumanmu na
mazhabar Malikiyyah, kamar Ibnul
Hajj wanda ya rasu a shekarar hijira
ta 732 watau yau da rasuwarsa
shekaru 702 ke nan da suka wuce, da
kuma Umarul Faakihaanii wanda ya
rasu a shekarar hijira ta 734 watau
yau da mutuwarsa shekara 700 ke
nan da suka wuce, da kuma
Ibraahimush Shaatibii wanda ya rasu
a shekarar hijira ta 690 watau yau da
rasuwarsa shekara 744 ke nan da
suka wuce, da kuma uwa-uba Sheik
Uthmanu Dan Fodiyo wanda ya rasu a
shekarar hijira ta 1234 watau yau
shekara 201 ke nan da rasuwarsa.
Amma Sheik Ibnul Hajj ga abin da
yake cewa cikin littafin Almudkhal
2/2, da 2/10-11 :-
(( ﻭﻣﻦ ﺟﻤﻠﺔ ﻣﺎ ﺍﺣﺪﺛﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻣﻊ ﺍﻋﺘﻘﺎﺩﻫﻢ
ﺍﻥ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻛﺒﺮ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ ﻭﺍﻇﻬﺮ ﺍﻟﺸﻌﺎﺋﺮ ﻣﺎ
ﻳﻔﻌﻠﻮﻧﻪ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﻗﺪ
ﺍﺣﺘﻮﻯ ﻋﻠﻰ ﺑﺪﻉ ﻭﻣﺤﺮﻣﺎﺕ ﺟﻤﻠﺔ ﻓﻤﻦ ﺫﻟﻚ
ﺍﺳﺘﻌﻤﺎﻟﻬﻢ ﺍﻟﻤﻐﺎﻧﻲ ﻭﻣﻌﻬﻢ ﺁﻻﺕ ﺍﻟﻄﺮﺏ( ( ﺍﻟﻰ ﺍﻥ
ﻗﺎﻝ : )) ﻭﺍﻥ ﺧﻼ ﻣﻨﻪ ﻭﻋﻤﻞ ﻃﻌﺎﻣﺎ ﻓﻘﻂ ﻭﻧﻮﻯ ﺑﻪ
ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﺩﻋﺎ ﺍﻟﻴﻪ ﺍﻻﺧﻮﺍﻥ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﻛﻞ ﻣﺎ ﺗﻘﺪﻡ
ﺫﻛﺮﻩ ﻓﻬﻮ ﺑﺪﻋﺔ ﺑﻨﻔﺲ ﻧﻴﺘﻪ ﻓﻘﻂ ﺇﺫ ﺍﻥ ﺫﻟﻚ ﺯﻳﺎﺩﺓ
ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﻟﻴﺲ ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﻤﺎﺿﻴﻦ ﻭﺍﺗﺒﺎﻉ
ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﻞ ﺃﻭﺟﺐ ﻣﻦ ﺍﻥ ﻳﺰﻳﺪ ﻧﻴﺔ ﻣﺨﺎﻟﻔﺔ ﻟﻤﺎ
ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻷﻧﻬﻢ ﺍﺷﺪ ﺍﺗﺒﺎﻋﺎ ﻟﺴﻨﺔ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻟﻪ ﻭﺳﻨﺘﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻟﻬﻢ ﻗﺪﻡ ﺍﻟﺴﺒﻖ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺒﺎﺩﺭﺓ ﺍﻟﻰ ﺫﻟﻚ ﻭﻟﻢ
ﻳﻨﻘﻞ ﻋﻦ ﺍﺣﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﺍﻧﻪ ﻧﻮﻯ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﻧﺤﻦ ﻟﻬﻢ ﺗﺒﻊ
ﻓﻴﺴﻌﻨﺎ ﻣﺎ ﻭﺳﻌﻬﻢ )).
Ma’ana: ((Yana daga cikin jumlar
abin da suka kirkira na bidi’o’i tare
da akidar cewa hakan yana daga
cikin manyan ibadodi, kuma yana
daga cikin alamomin Musulunci mafi
fita fili: abin nan da suke aikatawa
cikin watan Rabii’ul Awwal na bukin
maulidi. Shi dai maulidi ya tattari
abubuwan haramun da yawa a
dunkule, daga cikinsu akwai wake-
wake da suke yi tare da Kayan kade-
kade …. To amma idan yin maulidi
ya wifinta daga yin wake-wake tare
da kayan kade-kade mai yin maulidin
ya yi abinci kawai ya yi nufin maulidi
da shi ya kira yan’uwa zuwa cin
abincin, to, yin hakan ya zama bidi’ah
saboda niyyar maulidin da ya yi,
domin niyyar maulidin kari ne a cikin
Addini ba ya kuma daga cikin
ayyukan Salaf Magabata ba, bin
Magabata kuwa shi ne ya fi dacewa,
kai shi ne ma wajibi da a ce mutum
zai kara wani abu sabanin abin da
suka kasance a kansa, domin su
Magabata su ne suka fi kowa yin koyi
da Manzon Allah, kuma su ne suka fi
kowa girmama shi da girmama
sunnarsa, kuma su suke da kafar
rigaya wajen takawa zuwa ga abin da
yake alheri ne, babu kuma mutum
daya da ya ciro yin niyyar maulidi
daga dayansu, mu kuwa sauran
Musulmi mabiya ne gare su, dukkan
abin da ya wadatar da su na addini
shi ne zai wadatar da mu)). Intaha.
Sannan Imamul Faakihaanii ya ce
cikin Risalarsa ta maulidi mai suna
Almurid fil Kalaami alaa Hukmil
Maulid :-
(( ﻻ ﺍﻋﻠﻢ ﻟﻬﺬﺍ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﺻﻼ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﻭﻻ ﺳﻨﺔ ﻭﻻ
ﻳﻨﻘﻞ ﻋﻤﻠﻪ ﻋﻦ ﺍﺣﺪ ﻣﻦ ﻋﻠﻤﺎﺀ ﺍﻻﻣﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻫﻢ
ﺍﻟﻘﺪﻭﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻟﻤﺘﻤﺴﻜﻮﻥ ﺑﺂﺛﺎﺭ ﺍﻟﻤﺘﻘﺪﻣﻴﻦ ﺑﻞ
ﻫﻮ ﺑﺪﻋﺔ ﺍﺣﺪﺛﻬﺎ ﺍﻟﺒﻄﺎﻟﻮﻥ ﻭﺷﻬﻮﺓ ﻧﻔﺲ ﺍﻋﺘﻨﻰ ﺑﻬﺎ
ﺍﻻﻛﺎﻟﻮﻥ ﺑﺪﻟﻴﻞ ﺍﻧﺎ ﺍﺫﺍ ﺃﺩﺭﻧﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﺨﻤﺴﺔ
ﻗﻠﻨﺎ ﺍﻣﺎ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻭﺍﺟﺒﺎ ﺍﻭ ﻣﻨﺪﻭﺑﺎ ﺍﻭ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﺍﻭ
ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ ﺍﻭ ﻣﺤﺮﻣﺎ ﻭﻫﻮ ﻟﻴﺲ ﺑﻮﺍﺟﺐ ﺇﺟﻤﺎﻋﺎ ﻭﻻ
ﺑﻤﻨﺪﻭﺏ ﻻﻥ ﺣﻘﻴﻘﺔ ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺏ ﻣﺎ ﻃﻠﺒﻪ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻣﻦ
ﻏﻴﺮ ﺫﻡ ﻋﻠﻰ ﺗﺮﻛﻪ ﻭﻫﺬﺍ ﻟﻢ ﻳﺄﺫﻥ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻭﻻ
ﻓﻌﻠﻪ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻻ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻮﻥ ﻭﻻ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﺍﻟﻤﺘﺪﻳﻨﻮﻥ
ﻓﻴﻤﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﻭﻫﺬﺍ ﺟﻮﺍﺑﻲ ﻋﻨﻪ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻋﻨﻪ
ﺳﺌﻠﺖ ﻭﻻ ﺟﺎﺋﺰ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﻻﻥ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﻉ ﻓﻲ
ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻟﻴﺲ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﺑﺈﺟﻤﺎﻉ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻓﻠﻢ ﻳﺒﻖ ﺍﻻ ﺍﻥ
ﻳﻜﻮﻥ ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ ﺍﻭ ﺣﺮﺍﻣﺎ( ( . ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ban san wata hujja da za
ta halatta yin maulidi ba a cikin
Alkur’ani da Sunnah, kuma ba a
nakalto yin bukin maulidi koda daga
mutum daya ba cikin maluman
Al’umma wadanda su ne abin koyi a
cikin Addini , kuma su ne ke riko da
maganganun magabata, kai, abin da
dai yake ciki shi ne: shi dai maulidi
wata biri’ah ce da marasa aikin yi
suka kirkira kuma sha’awar son rai
ce da masu cin dukiyar mutane cikin
karya suka runguma, saboda shi dai
bukin maulidi idan muka shimfida shi
a kan hukunce-hukuncin nan guda
biyar sai mu ce: ko dai ya zama
wajibi, ko kuwa ya zama mustahabbi,
ko kuwa ya zama mubaahi, ko kuwa
ya zama makruuhi, ko kuwa ya zama
haraamun, to in mun yi hakan za mu
ga cewa shi dai ba wajibi ba ne bisa
Ijmaa’in Malamai, shi kuwa ba
mustahabbi ba ne domin abin da ake
nufi da mustahabbi shi ne abin da
Shari’ah ta ce a yi ba tare da an zargi
Wanda ya ki yi ba, shi kuwa maulidi
Shari’ah ba ta ce a yi shi ba, kuma ni
a sanina Sahabbai, da Taabi’ai, da
malamai masu riko da Addini ba su yi
shi ba, wannan shi ne jawabina a
gaban Allah a kan bukin maulidi in
har aka tambaye ni. Kuma ba zai
halatta ba a ce Maulidi ya zama
mubaahi saboda kirkiran wani abu
cikin addini ba zai zama mubaahi ba
a bisa Ijmaa’in Musulmi, saboda haka
babu abin da ya rage face maulidi ya
zama makruuhi ko kuwa haramun)).
Intaha.
Sannan Imamush Shaatibii ya ce -a
lokacin da yake yin bayanin ma’anar
bidi’ah- cikin littafinsa mai suna
Alitisam 1/50,53 :-
(( ﻋﺒﺎﺭﺓ ﻋﻦ ﻃﺮﻳﻘﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻣﺨﺘﺮﻋﺔ ﺗﻀﺎﻫﻲ
ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻳﻘﺼﺪ ﺑﺎﻟﺴﻠﻮﻙ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺍﻟﻤﺒﺎﻟﻐﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻌﺒﺪ
ﻟﻠﻪ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ …. ﻳﻌﻨﻲ ﺍﻧﻬﺎ ﺗﺸﺎﺑﻪ ﺍﻟﻄﺮﻳﻘﺔ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ
ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺍﻥ ﺗﻜﻮﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﺔ ﻛﺬﻟﻚ ﺑﻞ ﻫﻲ
ﻣﻀﺎﺩﺓ ﻟﻬﺎ ﻣﻦ ﺃﻭﺟﻪ ﻣﺘﻌﺪﺩﺓ …. ﻣﻨﻬﺎ ﺍﻟﺘﺰﺍﻡ
ﺍﻟﻜﻴﻔﻴﺎﺕ ﻭﺍﻟﻬﻴﺌﺎﺕ ﺍﻟﻤﻌﻴﻨﺔ ﻛﺎﻟﺬﻛﺮ ﺑﻬﻴﺌﺔ ﺍﻻﺟﺘﻤﺎﻉ
ﻋﻠﻰ ﺻﻮﺕ ﻭﺍﺣﺪ ﻭﺍﺗﺨﺎﺫ ﻳﻮﻡ ﻭﻻﺩﺓ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﺍ ﻭﻣﺎ ﺃﺷﺒﻪ ﺫﻟﻚ( ( . ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Bidi’ah wata kirkirarriyar
hanya ce cikin addini mai kama da
addinin gaskiya ana nufin kaiwa
matuka matuka cikin bautar Allah da
yin ta .., ina nufin ita bidi’ah tana
kama da hanyar Shari’ah ba tare da
ta kasance hanyar Shari’ah ta hakika
ba, kai a gaskiya ma tana karo ne da
hanyar Shari’ah ta fiskoki da yawa …
Daga cikinsu akwai lazimtar wasu irin
siffofi ayyanannu, kamar zikirin da
ake yi a bisa tsarin haduwa a kan
sauti daya’ da kuma rikon ranar
haihuwar Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah a matsayin idi, da abin
da yake Kama da haka)). Intaha.
Sannan Shehu Uthmanu Dan Fodiyo
ya ce cikin littafinsa mai suna
Ihyaaus Sunnah wa Iqmaadul Bid’ah
shafi na 104 :-
(( ﻓﺎﻥ ﻗﻠﺖ ﻣﺎ ﺣﻜﻢ ﻣﺎ ﻳﻔﻌﻞ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ
ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻭ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺴﺎﺑﻊ ﻣﻦ
ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻣﻦ ﺍﺟﺘﻤﺎﻉ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻟﻠﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﻄﻌﺎﻡ ﺍﻟﺬﻱ
ﻳﻌﻤﻠﻮﻧﻪ ﻟﺬﻟﻚ؟ ﻗﻠﺖ : ﺍﻧﻪ ﺑﺪﻋﺔ ﻣﻜﺮﻭﻫﺔ ﺍﻥ ﺧﻼ
ﻋﻦ ﻛﻞ ﻣﻌﺼﻴﺔ . ﻭﻗﻴﻞ : ﺍﻥ ﺍﻟﺼﻮﺍﺏ ﺍﻥ ﻋﻤﻞ
ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻟﺸﺮﻳﻒ ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺍﻟﺤﺴﻨﺔ ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺑﺔ
ﺍﺫﺍ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻣﻌﺼﻴﺔ . ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺎ ﻳﻌﺘﺎﺩﻩ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ
ﺍﻟﺰﻣﺎﻥ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﺧﺘﻼﻁ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻤﻌﺎﺫ
ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﺍﺣﺪ ﺑﺠﻮﺍﺯﻩ( ( . ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Idan ka ce: Mene ne
hukuncin abin da mutane suke yi a
cikin watan Rabii’ul Awwal a ranar
maulidi ko kuwa a ranar bakwai ga
maulidi na taruwar jama’a saboda yin
zikiri da cin abincin da aka yi
tanadinsa saboda hakan? Sai in ce:
Wannan bidi’ah ce makruuhiyah in
yin maulidin ya wofinta daga dukkan
sabon Allah. Amma kuma wasu sun
ce: Abin da yake daidai shi ne shi
bukin maulidin Annabi yana daga
cikin bidi’o’i masu kyau matukar dai
ya wofinta daga ko wane sabon
Allah. To amma abin da mutane suka
Saba yin shi a maulidi a wannan
zamani na cakuda tsakanin maza da
mata a’uuzu billahi da wani mutum
zai ce halal ne)). Intaha.
Wannan shi ne abin da malumanmu
na mazhabar Malikiyyah suka fada
game da bukin maulidi.
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah
wanda ya rasu a shekarar hijira ta
728 watau shekaru 706 ke nan da
suka wuce shi ya yi maganar maulidi
ya kuma tabbatar da cewa maulidi
bidi’ah ce, ya rubuta cikin littafinsa
mai suna Iqtidhaa’us Siraa’til
Mustaqiim 2/123-124 :-
(( ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻣﺎ ﻳﺤﺪﺛﻪ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻣﺎ ﻣﻀﺎﻫﺎﺓ
ﻟﻠﻨﺼﺎﺭﻯ ﻓﻲ ﻣﻴﻼﺩ ﻋﻴﺴﻰ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺍﻣﺎ ﻣﺤﺒﺔ
ﻟﻠﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻗﺪ
ﻳﺜﻴﺒﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻤﺤﺒﺔ ﻭﺍﻻﺟﺘﻬﺎﺩ ﻻ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺒﺪﻉ
ﻣﻦ ﺍﺗﺨﺎﺫ ﻣﻮﻟﺪ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﺍ
ﻣﻊ ﺍﺧﺘﻼﻑ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻣﻮﻟﺪﻩ ﻓﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﻟﻢ ﻳﻔﻌﻠﻪ
ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻣﻊ ﻗﻴﺎﻡ ﺍﻟﻤﻘﺘﻀﻲ ﻟﻪ ﻭﻋﺪﻡ ﺍﻟﻤﺎﻧﻊ ﻣﻨﻪ ﻟﻮ
ﻛﺎﻥ ﺧﻴﺮﺍ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﺧﻴﺮﺍ ﻣﺤﻀﺎ ﺍﻭ ﺭﺍﺟﺤﺎ ﻟﻜﺎﻥ
ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ ﺍﺣﻖ ﺑﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺎﻧﻬﻢ ﻛﺎﻧﻮﺍ
ﺍﺷﺪ ﻣﺤﺒﺔ ﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻟﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﺍﺣﺮﺹ ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻛﻤﺎﻝ
ﻣﺤﺒﺘﻪ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﻪ ﻓﻲ ﻣﺘﺎﺑﻌﺘﻪ ﻭﻃﺎﻋﺘﻪ ﻭﺍﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ
ﻭﺇﺣﻴﺎﺀ ﺳﻨﺘﻪ ﺑﺎﻃﻨﺎ ﻭﻇﺎﻫﺮﺍ ﻭﻧﺸﺮ ﻣﺎ ﺑﻌﺚ . ﺑﻪ
ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ﺑﺎﻟﻘﻠﺐ ﻭﺍﻟﻴﺪ ﻭﺍﻟﻠﺴﺎﻥ ﻓﺎﻥ ﻫﺬﻩ
ﻃﺮﻳﻘﺔ ﺍﻟﺴﺎﺑﻘﻴﻦ ﺍﻷﻭﻟﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻳﻦ ﻭﺍﻷﻧﺼﺎﺭ
ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﺗﺒﻌﻮﻫﻢ ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ( ( . ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Haka nan abin da sashin
mutane ke kirkira ko dai saboda koyi
da Kiristoci cikin bukin Kirsimeti’ ko
kuwa saboda son Annabi mai tsira da
amincin Allah da girmama shi, zai
yiwu Allah ya ba su lada a kan nuna
kokari da soyayya’ amma ba zai ba
su lada a kan bidi’o’in rikon maulidin
Annabi mai tsira da amincin Allah a
matsayin idi ba duk da yake ma masu
tarihi sun yi sabani a kan wace rana
ce da wani wata ne aka haife shi! Shi
dai bukin maulidi babu wani daga
cikin magabata da ya yi shi duk kuwa
da cewa dukkan dalilan da ake
bayarwa na yin bukin a yanzu akwai
su a wancan lokacin ma, kuma babu
wani abu da zai hana su yin bukin
inda yin shi alheri ne. Lalle ne da yin
bukin maulidi tsantsar alheri ne to da
Salaf Magabata su suka fi cancantar
yin sa a kanmu, saboda sun fi mu
son Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah da girmama shi, kuma
sun fi kowa son aikata alheri. Lalle
cikar soyayya da girmamawa ga
Annabi tana cikin bin shi ne da yi
masa da’ah da bin umurnin shi, da
raya sunnar shi ciki da waje, da yada
abin da aka aiko da shi, da yin jihadi
da zuciya, da hannu, da harshe a kan
hakan wannan ita ce hanyar
Magabata na farko daga cikin
Muhajirai da Ansarawa da wadanda
suka bi su da kyautayi)). Intaha.
Yan’uwa Musulmi! Wannan shi ne
matsayin bukin maulidi daga bakunan
wadannan gagga-gaggan maluman
Musulunci, tare ma kuma da cewa
Maluman tarihi da siiirah sun yi
sabani game da ranar haihuwar shi
Annabi mai tsira da amincin Allah, a
inda wasu suka ce:
1- An haife shi ne a ran biyu ga
watan Rabii’ul Awwal.
2- Wasu kuwa suka ce an haife shi
ne a ran takwas ga watan Rabii’ul
Awwal.
3- Wasu kuwa suka ce an haife shi
ne a ran goma ga watan Rabii’ul
Awwal.
4- Wasu kuwa suka ce an haife shi
ne a ran goma sha biyumga watan
Rabii’ul Awwal.
5- wasu kuwa suka ce an haife shi
ne a ran goma sha bakwai ga watan
Rabii’ul Awwal.
6- Wasu kuwa suka ce an haife shi
ne a ran ashrin ga watan Rabii’ul
Awwal.
7- Wasu kuwa suka ce an haife shi
ne a ran goma sha biyu ga watan
Ramadhan.
Domin ganin wannan sabanin sai ku
dubi littafin Taariikhul Islam na
Imamuz Zahbii a Juz’in Siirah shafi
na 25-27, da kuma littafin
Albidaayatu wan Nihaayatu na
Alhaafiz Ibnu Katheer 2/662.
Yan’uwa Musulmi! Kauli daidai har
bakwai a kan ranar haihuwar Annabi
mai tsira da amincin Allah babu
kuma wani wanda ya isa ya ce:
wannan kauli shi ne hakikanin
gaskiya wancan kaulin kuma ba
gaskiy ba ne, saboda abu ne da ya
faru kafin zuwan Musulunci kuma
bayan shi Musulunci ya zo bai
tabbatar da ranar haihuwar ba ta
hanyar wahayi saboda rashin
muhimmancin yin hakan a cikin
Addini.
Ke nan ware wata rana daga cikin
ranakun nan da aka ambata da
riyawar cewa ita ce ranar da aka haifi
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah akwai nau’i na karya da shedan
zur a cikin yin hakan. Allah ya tsare
mu da son zuciya.
Wannan shi ne kashi na farko game
da bayananmu a kan bukin maulidi,
kashi biyu na tafe in sha Allahu
Ta’ala, kuma zai yi bayani ne game
da shubuhohin da yan bidi’ah ke
ambatawa domin tabbatar da bidi’ar
maulidi.
Allah Ya nuna mana gaskiya gaskiya
ce ya ba mu ikon bin ta Ya kuma
nuna mana karya karya ce Ya ba mu
ikon kin ta.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

5 responses to “BAYANI A KAN BUKIN MAULIDI KASHI NA DAYA: (1)(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)”
  1. ABBA Avatar

    allah y taimaka malam

  2. iliya aliyu Avatar
    iliya aliyu

    MU JAHILIN MALAMI WANDA KE SHIRIN BATARDA MUTANE BAZAI CE MANA BABU HUJJAR ASO MANZON ALLAH(S.A.W)KO MAULUDI MU SAURARE SHIBA DOMIN KUWA KOMIN ILIMINSA DA RUKO DA AKIDARSA BAI KAI IBN TAIMIYYA,IBN KATHIR BA;
    KUMA DA YAWA MALUMA SUNYI BAYANI NA ILIMI AKAN MAULUDI .
    MU INDAI AKAN MAULUDI NE BAMU SHAKKAR UBAN KOWA.
    JAMA,A KUSA HANKALI DA TUNANI CIKIN BAYANIN WANNAN JAHILIN MALAMIN,CEWA YAYI AN FARA MAULUD TUN CIKIN KARNI NA HUDU KUMMA HARYANZU BA’A DAINABA SAIMA HABBAKA DA YAWAITA YAKEYI, KUTAMBAYE KANKU WAI KA TABA GANIN KARYA YA DORE?

  3. SADIQ AHMAD ABUBAKAR Avatar
    SADIQ AHMAD ABUBAKAR

    Aslm.malam muna karuwa da irin wadannan binciken kuma malam ayi hakuri ata mana rubutu akan abunda yake da masaloli,don kofewa mukeye muna karuwa, a sudan muke karatu.ALLAH YA SAKA DA ALHERI.

  4. […] BAYANI A KAN BUKIN MAULIDI KASHINA DAYA: (1)(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo). […]

Leave a Reply

Categories
Latest updates