BAYANI A KAN MAULIDI KASHI NA [iii](Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga karatu Online

KO HALACCIN SHIRYA MUSABAKA A
KAN HADDAR ALQUR’ANI, KO
HADDAR HADITHI, KO HADDAR WANI
ILMI NA MUSULUNCI, ZAI WAJABTA
HALACCIN RIKON RANAR HAIHUWAR
ANNABI MAI TSIRA DA AMINCIN
ALLAH A MATSAYIN WANI IDI???
LARABA 7/3/1435 H 8/1/2014 M
Yana daga cikin misalan da za mu
bayar na son zuciyar wadanda suka
zaba wa kansu sabanin shiriyar
Manzon Allah cikin gudanar da
addininsu, Maganar da wasu daga
cikinsu ke yi ta cewa: In har bukin
Maulidi bidi’ah ce, to kuwa lalle
Musabaka a kan haddar Alqur’ani Mai
girma, da haddar Hadithi, da haddar
wani ilmi na Musulunci shi ma
bidi’ah ce ke nan!!!
A nan ni ina ganin cewa yawan
nisantar wadannan mutane ga
littattafan Shari’ah na maluman
Musulunci ya sa ba su ma san cewa:
Dukkan abin da halaccinsa ya tabbata
ta yanyar Ijma’in Musulmi cikin wani
zamani daga cikin zamuna, to dole
ne ya zamanto daya daga cikin
abubuwa uku:-
1- ko dai ya zamanto Mubaahi.
2- ko kuwa ya zamanto Mustahabbi.
3- ko kuwa ya zamanto Waajibi.
Ita kuwa Musabakar Alqur’ani aba ce
da Maluman Sunnah, da kuma su
kansu ‘Yan bidi’ah na Duniya suka
hadu a kan halaccinta bisa hujjar
kiyasta ta a kan Musaabakokin da
Nassi ya zo da halaccinsu. In kuwa
haka lamarin yake, to ta kaka ne za a
hada hukuncin Musaabakar Alqur’ani
da hukuncin bukin Maulidin da babu
mai yin shi ko halatta shi in banda
wasu daga cikin ‘yan bidi’ah kawai??
Imam Ibnu Qudaamah mai rasuwa a
shekara ta 620 watau da mutuwarsa
yau shekaru 815 ke nan, ya ce cikin
littafinsa mai suna Almugnii
13/404-405 :-
{ ﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﺟﺎﺋﺰﺓ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻻﺟﻤﺎﻉ، ﺍﻣﺎ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺮﻭﻯ
ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺳﺎﺑﻖ ﺑﻴﻦ
ﺍﻟﺨﻴﻞ ﺍﻟﻤﻀﻤﺮﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻔﻴﺎﺀ ﺍﻟﻰ ﺛﻨﻴﺔ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ، ﻭﺑﻴﻦ
ﺍﻟﺘﻲ ﻟﻢ ﺗﻀﻤﺮ ﻣﻦ ﺛﻨﻴﺔ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ ﺍﻟﻰ ﻣﺴﺠﺪ ﺑﻨﻲ
ﺯﺭﻳﻖ . ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ … ﻭﺍﺟﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺟﻮﺍﺯ
ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻤﻠﺔ . ﻭﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺿﺮﺑﻴﻦ :
ﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ، ﻭﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻌﻮﺽ . ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ
ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ ﻓﺘﺠﻮﺯ ﻣﻄﻠﻘﺎ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺗﻘﻴﻴﺪ ﺑﺸﻲﺀ
ﻣﻌﻴﻦ، ﻛﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﻗﺪﺍﻡ، ﻭﺍﻟﺴﻔﻦ، ﻭﺍﻟﻄﻴﻮﺭ،
ﻭﺍﻟﺒﻐﺎﻝ، ﻭﺍﻟﺤﻤﺮ، ﻭﺍﻟﻤﺰﺍﺭﻳﻖ، ﻭﺍﻟﻤﺼﺎﺭﻋﺔ، ﻭﺭﻓﻊ
ﺍﻟﺤﺠﺮ ﻟﻴﻌﺮﻑ ﺍﻻﺷﺪ، ﻭﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ؛ ﻻﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺳﻔﺮ ﻣﻊ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻓﺴﺎﺑﻘﺘﻪ
ﻋﻠﻰ ﺭﺟﻠﻬﺎ، ﻓﺴﺒﻘﺘﻪ، ﻗﺎﻟﺖ : ﻓﻠﻤﺎ ﺣﻤﻠﺖ ﺍﻟﻠﺤﻢ
ﺳﺎﺑﻘﺘﻪ ﻓﺴﺒﻘﻨﻲ، ﻓﻘﺎﻝ : ﻫﺬﻩ ﺑﺘﻠﻚ . ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻮﺩﺍﻭﺩ .
ﻭﺳﺎﺑﻖ ﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ ﺍﻻﻛﻮﻉ ﺭﺟﻼ ﻣﻦ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭ ﺑﻴﻦ
ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺫﻱ
ﻗﺮﺩ . ﻭﺻﺎﺭﻉ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﻛﺎﻧﺔ
ﻓﺼﺮﻋﻪ . ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ . ﻭﻣﺮ ﺑﻘﻮﻡ ﻳﺮﺑﻌﻮﻥ ﺣﺠﺮﺍ
ﻳﻌﻨﻲ ﻳﺮﻓﻌﻮﻧﻪ ﻟﻴﻌﺮﻓﻮﺍ ﺍﻻﺷﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﻓﻠﻢ ﻳﻨﻜﺮ
ﻋﻠﻴﻬﻢ . ﻭﺳﺎﺋﺮ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺎﺕ ﻳﻘﺎﺱ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﺍ .{
ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Musabaka halal ce cikin
sunnar Manzon Allah, da Ijma’in
Maluma. A cikin Sunnah dai Ibnu
Umar ya ruwaito cewa Annabi mai
tsira da amincin Allah ya shirya
Musabaka tsakanin dawakin da aka yi
musu “Tadhmiir” (watau wadanda
aka yi musu horon tinkarar yaki ta
hanyar karanta abinci gare su da
sanya musu tufafinsu da sauransu) a
filin da ya taso daga Haifaa har zuwa
Thaniyyatul Wadaa, haka nan ya
shirya wata Musabakar tsakanin
dawakin da ba a yi musu Tadhmiiri
ba, a filin da ya taso daga
Thaniyyatul Wadaa har zuwa Masjidu
Bani Zuraiq. Buhari da Muslim ne
suka ruwaito hadithin…Sannan
Musulmi sun yi Ijma’i a kan halaccin
Musabaka a dunkule. Sannan ita
Musabaka ta kasu ne zuwa kashi
biyu: Musabaka da ake yi tare da
sanya wasu kudi cikinta (ga duk
wanda ya yi nasara). Akwai kuma
Musabaka da ake yi ba tare da an
sanya kudi cikinta (ga duk wanda ya
yi nasara ba). To ita Musabaka da
ake yi ba tare da an sanya wasu kudi
cikinta ba wannan ta halatta ba tare
da sanya mata wani tarnaki a cikinta
ba, kamar dai Musabakar da ake yi
na tseren gudu da kafa, ko
Musabakar tseren jiragen ruwa, ko
Musabakar tsere tsakanin tsutsaye,
ko Musabakar tsere tsakanin
alfadaru, ko Musabakar tsere
tsakanin jakuna, ko Musabakar tsere
tsakanin giwaye, ko Musabakar yin
harbi da kananan masu, ko
Musabakar yin kokowa, ko Musabakar
daga dutse mai nauyi sanoda gwada
karfi, da dai nau’o’in Musabaka
dabam daban. Saboda Annbi mai
tsira da amincin Allah wata rana a
hanyar tafiye-tafiyensa ya yi
Musabakar tseren gudu da kafa
tsakaninsa da matarsa Nana A’isha
Allah Ya kara mata yarda, kuma ta yi
nasara a kansa. Sai A’isha ta ce: da
na yi kiba sai wata rana muka sake
yin Musabakar tseren gudu da kafa
sai ya yi nasara a kaina. Sai ya ce da
ni: ni ma na rama wancan ci da kika
yi mini. Wannan hadithi Abu Dawuda
ne ya ruwaito shi. Kuma Salamah
Dan Ak’wa ya yi Musabakar tsere da
kafa tsakaninsa da wani mutum a
gaban Annabi mai tsira da amincin
Allah a ranar Ruwan Zuu Qarad.
Sannan Annabi mai tsira da amincin
Allah ya yi Musabakar kokowa
tsakaninsa da wani gwanin kokowa
mai suna Rukaanah, kuma ya yi
nasara a kansa ya kada shi. Tirmizii
ne ya ruwaito hafithin. Sannan wata
rana Annabi mai tsira da amincin
Allah ya wuce wasu mutane suna
Musabakar daga dutse mai nauyi
saboda sanin wane ne ya fi karfi,
amma bai hana su yin hakan ba.
Sauran Musabakpkin sai a kiyasta su
a kan wadannan)) [da nassi ya
tabbatar]. Intaha.
Sannan Ibnu Qayyimil Jauziyyah
wanda ya mutu a shekarar Hijira ta
751 watau yau shekaru 684 ke nan
da suka wuce ya ce cikin littafinsa
mai suna Alfuruusiyyah 1/318:-
{ ﺍﻟﻤﺴﺎﻟﺔ ﺍﻟﺤﺎﺩﻳﺔ ﻋﺸﺮﺓ : ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺣﻔﻆ
ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ، ﻭﺍﻟﺤﺪﻳﺚ، ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ، ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﻠﻮﻡ
ﺍﻟﻨﺎﻓﻌﺔ، ﻭﺍﻻﺻﺎﺑﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺎﺋﻞ، ﻫﻞ ﺗﺠﻮﺯ ﺑﻌﻮﺽ؟
ﻣﻨﻌﻪ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﻣﺎﻟﻚ، ﻭﺍﺣﻤﺪ، ﻭﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ . ﻭﺟﻮﺯﻩ
ﺍﺻﺤﺎﺏ ﺍﺑﻲ ﺣﻨﻴﻔﺔ، ﻭﺷﻴﺨﻨﺎ، ﻭﺣﻜﺎﻩ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺒﺮ
ﻋﻦ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ . ﻭﻫﻮ ﺍﻭﻟﻰ ﻣﻦ ﺍﻟﺸﺒﺎﻙ، ﻭﺍﻟﺼﺮﺍﻉ،
ﻭﺍﻟﺴﺒﺎﺣﺔ، ﻓﻤﻦ ﺟﻮﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺑﻌﻮﺽ،
ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ، ﻭﻫﻲ ﺻﻮﺭﺓ
ﻣﺮﺍﻫﻨﺔ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﻟﻜﻔﺎﺭ ﻗﺮﻳﺶ ﻋﻠﻰ ﺻﺤﺔ ﻣﺎ
ﺍﺧﺒﺮﻫﻢ ﺑﻪ، ﻭﺛﺒﻮﺗﻪ . ﻭﻗﺪ ﺗﻘﺪﻡ ﺍﻧﻪ ﻟﻢ ﻳﻘﻢ ﺩﻟﻴﻞ
ﺷﺮﻋﻲ ﻋﻠﻰ ﻧﺴﺨﻪ . ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﺍﺧﺬ ﺭﻫﻨﻬﻢ ﺑﻌﺪ
ﺗﺤﺮﻳﻢ ﺍﻟﻘﻤﺎﺭ . ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻗﻴﺎﻣﻪ ﺑﺎﻟﺤﺠﺔ، ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ،
ﻓﺎﺫﺍ ﺟﺎﺯﺕ ﺍﻟﻤﺮﺍﻫﻨﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺕ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ، ﻓﻬﻲ ﻓﻲ
ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ . ﻭﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻫﻮ ﺍﻟﺮﺍﺟﺢ .{
ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Mas’alah ta goma sha
daya: Yin Musabakar haddace
Alkur’ani, da Hadithi, da Fiqhu, da
wasu Ilmummuka masu amfani, ko
gane abin da yake daidai cikin wasu
mas’alolin, shirya irin wannan
Musabaka a bisa wani kudi, shin
hakan zai halatta ko kuwa ba zai
halatta ba? Mutanen Malik, da
Ahmad, da Sha’fi’ii sun hana yin sa.
Amma mutanen Abu Hanifah da
Malaminmu (Ibnu Taimiyah) da ma
hikayar Ibnu Abdil Barr daga Sha’fi’ii
sun halatta yinsa. Shi wannan nau’i
na Musabaka ya fi yin Musabaka a
kan harkar iya sa tarko, ko kokowa,
ko ninkaya, sanoda haka wadanda
suka halatta shirya Musabaka a bisa
kudi cikin wadannan, lalle shirya
Musabaka cikin harkokin habaka ilmi
shi zai fi cancantar halatta, kuma
wannan ita ce surar Muraahanar da
Sbubakar Siddiq ya yi da kafuran
Quraishawa a kan gaskiyar labarin da
ya ba su (na cewa Ruumaawa za su
yi nasara a kan Faatisaawa bayan
shekaru kadan). Dalili ya gabata na
cewa babu abin da ya shafe ingancin
wannan Muraahanar. Kuma shi
Abubakar ya yi Muraahanar da su ne
bayan haramta yin caca. Sannan ita
tsayuwar Addini da ma tana samuwa
ne ta hanyar kafa hujja, da yin jihadi,
saboda wannan idan har Muraahanah
za ta halatta a kan abubuwan karfafa
jihadi, ke nan ta halatta a kan
abubuwan karfafa ilmi da za su
karfafa kafa hujja shi ne zai fi
cancanta, kuma wannan magana ita
ce abin rinjayarwa)). Intaha.
Yan’uwa Musulmi! Lalle da wadannan
bayanai ne daliban ilmi za su fahimci
cewa ita Musabakar haddar Alkur’ani
mai girma, ko haddar Hadithi, da
haddar wani ilmi mai amfani -tare da
sanya wani kudi ga wanda ya yi
nasara ko kuwa ba tare da sanya
wani kudi ga wanda ya yi nasara ba-
abu ne da yake halal ta hanyar hujjoji
biyu: Na farko: Ijma’i. Na biyu:
Qiyaasi. Wannan kuwa duka sabanin
maida ranar haihuwar Annabi mai
tsira da amincin Allah wani Idi ne,
wanda babu Ijma’i a kansa, babu
kuma wani Qiyaasi sahihi a kansa.
Muna rokon Allah Ya taimake mu Ya
tabbatar da dugaduganmu a kan
Sunnar Annabi mai tsira da amincin
Allah. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Categories
Latest updates