Raddin Abduljabbar dan Taratsi Ga Mulhidan 'Yan Tijjaniyya

Assalamu Alaikum Barkanku da yau. Kaman yanda kowa ya sani ne cikin kwanakinnan muna cikin bakin ciki game da abubuwan da wasu ‘yan tijjaniyyah suka aikata na cin mutuncin manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam). Wanda hakan ya kai ga samun raddodi daga maluma na sunnah har da ma malaman Bid’ah wanda abin ya wuce tunaninsu. Kaman yanda ya gabata na gabatar muku da raddin malaman sunnah biyu Dr Sani Umar Rijiyar Lemo Da Kuma Sheikh Abdallah Gadon Kaya yau zan kawo muku raddin wani malamin Darika amma ta Qadiriyyah wato Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara. Shidai Abduljabbar Kaman yadda kowa ya sani ya shahara Da hayaniya Da Taratsi Da kuma kai harin Ta’addanci wa sahabban Manzon Allah(Sallallahu Alaihi wasallam) da kuma magabata na kwarai irinsu bukhari muslim da sauransu. Shidai ba kafar baya bane wurin Ta’addanci acikin addinin musulunci, amma duk da wannan ta’addancin tasa ya ga cewa wa’innan ‘yan Tijjaniyya sunfishi har yaga ya dace Yayi musu raddi mai zafi. Masu sauraro sai kuyi hakuri Sabida acikin raddin tasa zakuga cewa yana kawo ayoyi da kurakurai kuma Ihu da taratsi tayi yawa awurin. Hakan ta samo nasaba ne kan abinda ya gine mabiyansa kan hayaniya da Ihu. Sannan kawo ayoyi da yakeyi da kurakurai ta samo asali ne kan rashin hadda da yake fama da ita kamar yadda shi ya fada da kansa acikin wasu karatuttukansa. Kada na cikaku da bayanai domin sauke wannan raddi DANNA NAN. Ayi sauraro lafiya wassalamu alaikum.

SHARHI AKAN WAKAR "NI DAI BARHAMA NAKE BAUTAWA, DAN SHI YA HALICCENI"

SHARHI AKAN WAKAR “NI DAI BARHAMA NAKE BAUTAWA, DAN SHI YA HALICCENI”
Daga Muhammad Rabiu Umar
Dalilin Yin Wakar “Ni Dai Barhama Nake Bautawa, Don Shi Ya Halicce Ni”
A yan kwanakin nan wata waka da wani mawaki ya yi mai take “Ni dai Barhama nake bautawa, don shi ya halicce ni” ta jawo cece-kuce a tsakanin mutane, kuma da yawa daga cikin mutane sun yi mamakin a ce wai musulmi ne ya yi wannan wakar, wanda daga baya-bayan nan gwamnatin Kano ta hanyar hukumar tace finafinan ta bada sammacin a kamo wannan mawaki.
Amma alal-hakika duk wanda ya san irin akidar da take cikin manya-manyan littattafan darikun sufaye – musamman yan tijjaniyya – to ba zai yi mamakin jin irin wannan waka ta fito daga irin masu wannan darika.
Idan muka dauki babban littafin darikar tijjaniyya mai suna “Jawahirul Ma’ani” zamu ga cike yake da akidar “Komai Allah ne” ma’ana duk wani abu da yake duniyar nan Allah ne, kuma in an bauta masa babu laifi, Allah aka bautawa, ga kadan daga cikin abin da ya zo akan haka : Shehu Tijjani ya ce :
“فما في ذوات الوجود كله إلا الله سبحانه وتعالى تجلى بصورها وأسمائها، وما ثمّ إلا أسماؤه وصفاته” (جواهر المعاني : 1/259).
Ma’ana “Babu abin da yake cikin zatin dukkan samammu gaba dayansu sai Allah Subhanahu Wa Ta’ala, shi ne ya bayyana a surarsu da sunayensu. Babu wani abu sai sunayensa da siffofinsa” (Jawahirul Ma’ani 1/259).
Wannan magana tana nuna cewa duk wani abin da yake samamme a wannan duniya to ba komai ba ne face Allah ne, saboda Allah ne ya bayyana a cikin dukkan komai da sunayensa da siffofinsa.
A wani wurin ya ce :
“إن جميع المخلوقات مراتب للحق…فإن الوجود عين واحدة لا تجزؤ فيها على كثرة أجناسها وأنواعها ووحدتها” (جواهر المعاني : 2/92).
Ma’ana : “Dukkan ababen halitta wasu yanki ne na Allah….saboda da dukkan samamme abu daya ne, babu wani yanki-yanki a cikinsa, duk da jinsinsa mai yawa da nau’o’insa da hadewarsa” (Aljawahir 2/92).
Wannan bayani yana nuna cewa duk wata halitta Allah ce ita, kuma komai da muke gani abu daya ne, wanda shi ne Allah!.
Ya sake cewa :
“فكل عابد أو ساجد لغير الله في الظاهر فما عبد ولا سجد إلا لله تعالى، لأنه هو المتجلي في تلك الألباس، وتلك المعبودات كلها تسجد لله تعالى…وقوله “لا إله إلا أنا” يعني لا معبود غيري وإن عبد الأوثان من عبدها فما عبد غيري” (جواهر المعاني : 1/184)
“Duk wani mai bauta ko mai sujjada ga wanin Allah a zahiri, ba wanda ya bautawa ko ya yi wa sujjada sai Allah Ta’ala, saboda shi ne yake bayyana a cikin wadannan abubuwa, kuma duk wadannan abubuwa da ake bautawa suna sujjada ne ga Allah (S.W.T)….sannan fadin Allah “Babu abin bautawa sai ni” yana nufin babu wani abin bautawa, wanda ba ni ba, ko da kuwa masu bautar gumaka sun bauta masu, ba su bautawa wani ba” (Jawahirul Ma’ani 1/184).
Wannan kadan kenan daga cikin mummunar akidar dake cikin wannan babban littafin na darikar tijjaniyya. To yanzu dan uwa mai karatu wanda ya karanta wadannan maganganu, kuma ya yi imani da su, ya yarda da cewa wanda ya yi su, waliyyi ne daga cikin waliyyan Allah, kuma duk abin da yake fada Annabi ne (S.A.W) yake fada masa, a farke a cikin barci, to yaya ba zai ce “Barhama Yake Bautawa ba”!.
Wata kila mai karatu ya ce, to ba Barhama ba ne ya koyar da haka, don haka me ya sa shi mai wakar bai ce “Shi Tijjani yake bautawa ba” sai ya ce Barhama.
Dalili, shi kansa Barhama din wato shehu Ibrahim Inyass haka shi ma ya koyar ya kuma kira muridansa da mabiyansa a kan haka, a cikin littattafansa, ga kadan daga cikin abin da ya fada a kan haka :
Yana cewa :
فإنّ الشّيخَ مظـهرُ ذات ربِّي وعينُ العَين عينُ أبي العباس. (( ديوان تحفة أطايب الأنفاس )) (ص86).
Ma’ana : Lallai hakika shehu shi ne Mazharin zatin Ubangijina. Kuma Hakikanin zati, shi ne zatin Abul Abbasi (wato shehu Tijjani).
Anan zamu ga Inyass yana cewa shehu Tijjani shi ne Allah, kuma duk wani zati na wani abu, ba komai ba ne face zatin shehu Tijjani, don haka komai shehu Tijjani ne, shi kuma Allah ne!!.
A wani wuri cewa ya yi :
خليفةُ الله في أرضٍ لذلك مَن رآكمُ قد رَأى ربَّ البريَّات
Ma’ana : “Khalifan Allah a bayan kasa, don haka duk wanda ya ganku, to lallai ya ga ubangijin halitta”. (Duba littafinsa Diwanu Tuhafatil Adayibil Anfas).
Subhanallahi, don ka ji mai karatu duk wanda ya ga shehu Tijjani to ya ga Allah, Ma’ana da Allah da Shehu Tijjani duk abu daya ne!!!.
Wannan kadan kenan daga cikin akidun da suke cikin littattafan wadannan sufaye, kuma a kansu ne suke kokarin renon mabiyansu, wanda har akwai wata tarbiyya da ake wa muridi, wadda bayan ya yi ta, sai zama Allah, kuma komai ya zama Allah a wurinsa, Sheikh Dahiru Mai gari (Allah Ya Yi masa Rahama) ya yi rubuta akan wannan tarbiyya da darika, ya tabbatar da wadannan abubuwa.
Don yan uwa in ana so a magance ci gaba da faruwar irin wadannan wakoki to dole ne sai an wancakalar da wadancan littattafai, kuma an dawo kan koyarwar Alkur’ani da Hadisi a bisa fahimtar magabata na Kwarai. Allah ya tsare mana Imaninmu Ameen.

Takaitattun Tarihin zantukan Sufayen Farko

Bismillahirrahmanirraheem.
Shin wai masu ikrarin sufanci a zamaninmu na yanzu shin sufayen ne da gaske ko kuma ‘yan cuwa cuwa ne? Ya dace ‘yan uwa mu fahimci abinda mukeyi kada mudinga ruduwa da shirme mu daukeshi a matsayin addini. Addini na littafin Allah addini na hadisan manzon Allah(s.a.w). Zan hakaito mana wasu daga cikin kalamai na sufaye na farko domin mu gwada wannan kalamai da kuma halin da wasu masu karyar sufanci suke ciki.
Shin da farko a takaice meye sufanci da ginu akai? Ta ginu ne kan gudun duniya, da bautar Allah. sufi yakan kaurace wa jama’a ya koma kan dutse yayi zamansa yayi ta bautar Allah. Haka abin ya fara yana tafiya. Kafin tafiyar tazo ta samu matsalar da ‘yan bid’ah suka ruda ta. Duk da dai ita sufancin bata da asali a addini, kuma malamai sunyi bayani akai. Amma zan rubuto kalaman ne saboda mabiya sugane ainihin sufanci na da din.
Da Farko ga bayanin Da junaid yayi, wanda in ana magananan sufanci ne dole a sanya su aciki. Domin su kusoshi ne.
قال جنيد رحمه الله: طريقتنا هاذا مقيد بالكتاب والسنة. من لم يحفظ الكتاب ولم يحفظ الحديث فلا يقربن طريقتنا.
Junaid Allah ya gafarta masa yace: WANNAN DARIKA TAMU AN KAYYADE TANE AKAN LITTAFIN ALLAH DA KUMA HADISIN MANZON ALLAH, DUK WANDA BAI KIYAYE LITTAFIN ALLAH BA, KUMA BAI KIYAYE HADISAN MANZON ALLAH BA TOH KADA YA KUSANCI DARIKARMU….
Sannan Ga kuma abinda Sahl al tustari yake cewa:
أصول طريقتنا خمسة.
1.التزام بالكتاب والسنة.
2.الإقتداء بنبي الأمة.
3.أكل الحلال.
4.العفو عن من ظلمك.
5.لزوم التوبة.
Yace: asalin hanyar mu Guda biyar ne:
1.ka lazumci littafin Allah da sunnar annabi(s.a.w).
Toh dun Allah yanzu ina masu kiran kansu sufaye ina sunnar annabi? Sai dai abaki. Abinda ake nufi da lazumta shine: ya zama koda yaushe kana mai aikatashi, da zarar kaji ance annabi yace kaza, ko yayi kaza, kaima ka aikata shi. Ance annabi na son aswaki, kaima kaso aswaki, ance annabi na barin gemu, kaima bar gemu, ance annabi na sallan dare, kaima tashi kayi, ance annabi na azumin litini da alhamis,kaima daure kayi. Ance annabi baya barin tufafinsa yaja kasa, kaima dage naka, irin wa’innan su ake kira sunnah, da zarar ankawo maka hadisi inagatacce, ta dace da son zuciyarka bata dace ba karbeta. Amma
rawa, kida da fada a baki, ba ita ke nuna bin sunnar annabi ba. Wani malami yake cewa:
ومن محبته صلى الله عليه وسلم. انتصار سنته.
Yace yana daga cikin son manzon Allah(s.a.w) taimakon sunnarsa… Ina masu kururuwan son annabi? Ba yiwa annabi waka da rawa shi ke nuna son annabi ba. A’a, ka taimaki sunnarsa, ka yada addinin da yazo dashi. Ka bi duk abinda yace ka kaurace wa abinda yayi hani akai….wannan itace hakikanin son annabi, amma bawai fada da baki ba.
2.na biyu yace, yin koyi da Annabi(s.a.w)..
Ya zamto duk abinda zakayi kana koyi da annabi ne. Kafin ka zama sufi na gaskiya sai ya zamto duk abinda zakayi kana koyi ne da annabi(s.a.w) ba zaka kirkiri wata kalar ibadah dabam ba irin ta annabi ba, ba zakayi sallah ba irin ta annabi ba. Ba zakayi zikiri ba irin ta annabi ba.
3.na uku yace: cin halal. Duk wani sufi na gaskiya zakaga ya toge kan cin halal. Babu ruwanshi da haram..
4.asali na hudu yace, yafiya ga wanda ya zalunce ka.. Duk sufi na gaske babu ruwanshi da hayaniya, duk abinda aka mishi yafewa yakeyi. Ba zai zalunceka ba, kuma inka zalunce shi sai ya yafe.
5. Sai na biyar yace: lazumtar tuba.. Duk sufi zaka sameshi a kullum mai lazumtar tuba ne… Mai kankan da kai zuwa ga Allah…
Wa’innan sune kalaman sahl al tusturi. Dun Allah ‘yan’uwa ku kula da irin wannan zantuka na hamshakan malaman sufanci na gaske… Idan aka dauki wa’innan ka’idoji aka sanya akan masu ikrarin sufanci na yanzu za’a samu sufi ko guda daya? Ko daya babu. Sannan meyasa basu fitar da irin wannan kalaman suna tallata wa mabiyansu? Dun Allah ga aiki na baiwa duk wani dan’uwa mabiyin darikah..
1. Ya dauki wannan ka’idojin wanda kusoshin sufanci suka fada, ya daurashi kan shehinsa, ko malaminsa, yaga inba shehinsa ko malaminsa na kan ramin halaka ba, yanzu dun Allah suwaye masu fada da kitaab wa sunnah? ‘yan dariku, gashi kuma sahl ya fara kawo cewa darikarsu tana rataye ne da kitaab wa sunnah.
2. Na biyu.. Meyasa ba’a bude majalisi na littafai wanda sufayen zamani suka rubuta? Irin littafin jawaahiru ma’ani, Meyasa? Shin sun qunshi gaskiya kuwa? Su duba duk wani malamin sunnah in ya buga littafi ana bude majalisi a karanta abinda ya rubuta.. Amma ku tambayi kanku meyasa ba’a karanta naku?….
Daga karshe duk maison gane hakikanin tasawwufanci, to ya binciki wallafe wallafen wa’innan bayin Allah. Irinsu sahl al tusturi, ibrahim ibn adham, irinsu junaid. Da abdulkadir jailani. Domin shima abdulkadir jailani ahlussunnah ne. Duk masu maqalewa dashi a tafarkin darika karya sukeyi… ‘yan’uwa matasa mabiya darikah. Wallahi inkunason gaskiya ku binciki littafan wa’innan maluman da kuma tarihinsu, wa’inda sune jagorori a harkar sufanci,kusha mamaki. Wallahi sai kun gudu kunbar wannan shirme da kukeyi da sunan addini… Zaku tabbatar an rudeku.. Mu mun karanci sufancin zamani da aqeedunsu, sai muka gujesu. Kaima dan’uwa ka karanci aqeedar ahlussunnah mana a rubuce muga ko. zaka kisu? Kadaina amfani da malam wane yace, ko wane ya aikata kaza. A’a karanta a rubuce ka fahimta, wannan itace hakikanin gaskiya.ina aka samu wai malami ya zauna a gida bayi da aikin komai wai sai roka wa mutane Allah. Shin wannan abu na da asali a addini? Malam baka fita jihadi, baka fita wa’azi, kai kenan kullum ka tsubbace kanka wuri daya? Shin haka annabi ya rayu ta wannan hanya? Ina aka samu raba wa mutane darika? Shin akwai wani nassi da ya tabbatar da haka? Ina aka samu kirkirar bid’ah da sunan mai kyau? Yaa dace jama’ah ayi lura, yanzu lokaci ya wuce da za’ayi ta mana nuku nuku. Komai ya fito fili mun gane. Maison gaskiya yaci gaba da bincike Allah zai nuna masa.. Jama’a ayi hakuri in na tsawaita…. Allah yasa mugane, Allah ka shiryar damu Hanya madaidaiciya. Wanda kuma ranshi ya baci da zantuka na, yayi hakuri. Ni inayi ne saboda kauna da nakeyi wa ‘yan’uwa wanda suka kauce wa hanya. Wassalaamu alaikum wa rahmatullah.