DARASI NA TARA (9)SHUBUHOHIN SHI’A A MAHANGAR SHARI’A(Malam .Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

DARASI NA TARA (9)
Bismillahir Rahmanir Rahim
Jama’ar wannan zaure namu mai
albarka muna muku barka da
wannan rana mai albarka, kuma
muna rokon Alla (S.W.T) ya
sadamu da dukkan alkhairan dake
cikinta kuma ya tsaremu da dukkan
sharrin dake cikinta. Cigabada
darasinmu na littafin mu na
“SHUBUHOHIN SHI’A A
MAHANGAR SHARI’A” na Hamza
Uba Abubakar Kabawa gabatarwar
Muhammad Aminu Ibrahim
Daurawa : –
SHUBUHOHIN SHI’A A KAN
UMARNIN DA ALLAH (S.W.T)
YABAWA MANZON ALLAH
(S.A.W) NA ISAR DA SAKO DA
BAYANIN HAKIKANIN WANNAN
SAKON.
Shubuha ta shida da ‘Yan Shi’a
masu limamai goma sha biyu suke
yadawa, don su yaudari mutane ita
ce, da’awar da suke yi cewa: –
lokacin da Allah (S.W.T) ya saukar
da fadinSa ga Manzon Allah
(S.A.W): – “Ya kai wannan Annabi
ka isar da abin da aka saukar
maka daga Ubangijinka” . Sai
Manzon Allah (S.A.W) ya yiwa
mutane huduba a wani guri da ake
kiransa da suna Gadir Khum ya ce:
– “Ya ku mutane ba ni ne na fi
cancanta ku soni ba, fiye da
kawunanku? Sai Sahabbai suka
ce: – haka ne. Sai Manzon Allah
(S.A.W) ya ce: – “Wanda duk na
kasance Maulansa (Masoyi) to
Aliyu ma Maulansa ne, ya Ubangiji
ka so mai sonsa (Aliyu) ka yi gaba
da mai gaba da shi, ka taimaki
wanda ya taimake shi, ka
wulakanta wanda ya wulakanta
shi”. A wani lokacin ‘Yan Shi’a
sukan kara da wata kissa ta wani
mutum mai suna Harith dan
Nu’uman Alfihri cewa, Yazo ya ce
da Manzon Allah (S.A.W), Yanzu
ya ma’aikin Allah, ka umarce mu
da shika-shikan musulunci guda
biyar mun yarda. Kuma hakan bai
isa ba har sai da ka fifita dan
amminka a kan mu?
Sai mutumin ya fita yana cewa “ya
Allah idan wannan abun gaskiya
ne daga gurin ka yake ka yi mana
ruwan dutse daga sama ko ka zo
mana da azaba mai radadi daga
gurinka”. Wannan mutumin bai
karasa inda taguwarsa take ba, har
sai da Allah ya jefe shi da dutse
daga sama, dutsen ya Fada kansa
ya fita ta duburarsa. Sannan sai
Allah ya saukar da ayar farko ta
suratul Al-Mi’iraj wato fadin Allah
(S.W.T) “Mai tambaya yana
tambaya dangane da azaba mai
afkuwa…….” .
Jawabi a kan wannan shubuha shi
ne ta fuskoki kamar haka:
1. Gaba daya wannan kissar ta
karya ce babu ita, kuma bata
tabbata ba cikin ingantattun
littattafai na tafsiri da Hadisi da Sira
(Tarihi) wadanda ake dogaro da su
wajen kafa hujja. Abin da yake
nuna haka shi ne wannan ayar ta
sauka ne tun a Makka kafin hajjin
ban kwana da shekaru masu
yawa .
2. Duk cikin Sahabbai babu wani
mutum mai suna Harith dan
Nu’uman Alfihiri kamar yadda
malaman tarihi suka tabbatar .
3. Ayar da aka ce wannan mutumin
ya karanta, ta cikin suratul Anfal
wato fadin Ubangiji (S.W.T) “ya
Allah idan wannan abun gaskiya
ne daga gurin ka yake ka yi mana
ruwan dutse daga sama ko ka zo
mana da azaba mai radadi daga
gurinka” an saukar da ita ne tun a
Makkah.
Babban malamin nan na Tafsiri
Hafiz Ibn Kathir ya hakaito
maganganun malamai guda biyu,
dangane da wanda ya fadi wannan
maganar.
Magana ta farko ita ce : – Abu
Jahlin shi ne ya fadi wannan
maganar.
Magana ta biyu ita ce: – Nabru dan
Harith shi ya fadi wannan
maganar.
Wadannan mutane kuwa, dama
can kafirai ne an kuma kashesu ne
tun a yakin Badar. Ballantana a ce
wani daga cikinsu ya gayawa
Manzon Allah (S.A.W) cewa: –
Yanzu ya ma’aikin Allah, ka
umarce mu da shika-shikan
musulunci guda biyar mun yarda.
Kuma hakan bai isa ba har sai da
ka fifita dan amminka a kan mu?
Shi kuwa yakin Badar an yi shi ne ,
a shekara ta biyu bayan Hijira.
Hudubar Gadir Khum kuwa
Manzon Allah (S.A.W.) ya yi ta ne,
lokacin dawowarsa daga Hajjin
ban kwana, sha takwas ga watan
Zul-hijja shekara ta goma bayan
Hijira.
4. Tun bayan mutanen Abrahata
da Allah (S.W.T) ya jefe su da
duwatsu na wuta, ya hallakasu
kamar yadda labarinsu ya zo a
cikin suratu Al-Fil. Babu wani
mutum a cikin wannan al’ummar ta
Manzon Allah (S.A.W) da malamai
suka rawaito cewa, an jefe shi da
dutsen wuta daga sama. Da kuwa
akwai, da Malamai sun hakaito ta.
5. Ayar da take cewa “Ya kai
wannan Annabi ka isar da abin da
aka saukar maka daga
Ubangijinka” . Bata da wata alaka
da maganar shugabanci ko
halifanci baki daya.
Saboda umarni ne da ya shafi isar
da dukkan lamarin Addini Allah
(S.W.T). Shi yasa har karshen
rayuwar Manzon Allah (S.A.W)
yake isarwa da al’umma dukkan
lamarin addini. Kuma koda a hajjin
bankwana, sai da ya tamba yi
Sahabbai cewa: Shin na isar da
sako? Sahabbai suka ce tabbas ka
isar da sako. Sai Manzon Allah
(S.A.W) ya daga kansa sama ya
ce: ya Allah ka shaida.
(6) Wannan ayar dake cikin Suratul
Ma’ida, ta sauka ne tun farkon
shigowar Manzon Allah (S.A.W)
garin Madina. Kamar yadda ya
tabbata a cikin Hadisi cewa: – “A
farkon Hijira Sahabbai sun
kasance suna gadin Manzon Allah
(S.A.W.), har sai da Allah ya
saukar da Fadinsa: – “Ya kai
wannan Annabi ka isar da abin da
aka saukar maka daga
Ubangijinka har izuwa Fadin Allah-
Allah ne zai kare ka daga sharrin
mutane.”
Sai Manzon Allah (S.A.W) ya
sallami dukkan masu tsaronsa,
saboda samun cikakkiyar kariya
daga Allah (S.W.T), kamar yadda
Allah (S.W.T) ya yi masa alkawari.
(7) Annabawan Allah (S.W.T) baki
dayansu sun isar da dukkan sakon
da Allah (S.W.T) ya umarcesu da
su isar, ba tare da sun boye komai,
ko sun ji tsoron wani ba.Wannan
ita ce shaidar da Allah (S.W.T) ya
yi musu a cikin Al-kur’ani. Shi yasa
Allah (S.W.T) ya ba su cikakkiyar
kariya, don ya tabbatar da sun
sauke wannan nauyi da amana.
Amma abin mamaki sai ga ‘Yan
Shi’a suna siffanta limamansu da
tsoron mutane, yaudararsu da
kuma ha’intarsu ta hanyar bayyana
musu abin da ba shi ne hakikanin
gaskiya ba, da sunan wani abu wai
shi takiyya.
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita
ce ina siffar ma’asumancin da suke
da’awar cewa limamansu suna da
ita?
Saboda a ka’ida ma’asumanci ba
ya taba haduwa da takiyya.
limaman Shi’a kuwa sun rayu ne
kacokan a halin takiyya a
da’awarsu.
(8) Dukkan malamai sun hadu a
kan cewa bai halatta ga wani
mutum, ya yi addu’ar Allah (S.W.T)
ya ba shi Annabta ba, tun bayan
aiko Manzon Allah (S.A.W.).
Sabanin limanci, da malamai suka
hadu a kan halaccin rokon Allah
(S.W.T) ya sanya mutum limami na
masu tsoron Allah (S.W.T). Bari ma
dai yin irin wannan addu’ar, aiki ne
na manyan ba yin Allah (S.W.T) na
gari. Kamar yadda Allah (S.W.T)
yake siffantasu da cewa: – “Su ne
masu addu’a suna cewa ya ka
bamu mata da ‘ya’ya wadanda
zasu zamo mana sanyin ido ka
kuma sanya mu limamai na masu
tsoron Allah”.
Sai wannan yake nunawa a fili
cewa Annabta daban, limanci
daban.
Sabanin da’awar da ‘Yan Shi’a
suke yi cewa, limanci da annabta
abu daya ne.
(9) Imani da Manzon Allah (S.A.W)
tare da yin biyayya a gare shi, wani
abu ne da ba ya canjawa. Dai dai
ne Manzon Allah (S.A.W) yana
raye ko bayan komawarsa ga Allah
(S.W.T). Shi yasa malamai suka
hadu a kan cewa mutum yana
shiga musulunci ne da Kalmar
shaidawa babu abin bauta da
gaskiya sai Allah (S.W.T), Annabi
Muhammad (S.A.W) ma’aikin Allah
(S.W.T) ne.
Da wannan kalma ne mutum yake
zamowa musulmi, wanda jininsa
da dukiyarsa suka kubuta. Haka
wannan hukuncin yake tun daga
zamanin Manzon Allah (S.A.W.)
har izuwa yau.
Sabanin ‘Yan Shi’a da suke
da’awar cewa mutum ba ya zama
musulmi har sai ya yi imani da
limamansu goma sha biyu, koda
kuwa ya yi imani da Allah (S.W.T)
da Manzon Allah (S.A.W) da
Mala’iku da littattafan da Allah
(S.W.T) ya saukar da ranar lahira
da kaddara ya kuma aikata shika-
shikan musulunci guda biyar.
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita
ce: – idan har yin imani da limamai
guda goma sha biyu rukuni ne na
imani, me yasa a cikin Al-kur’ani
babu aya ko daya da ta yi bayani
karara a kan wajabcin yin imani da
limamai goma sha biyu, kamar
yadda Al-kur’ani yake cike da
bayani a kan wajabcin yin imani da
ragowar rukunan imanin?
(10) Yau fiye da shekara dubu da
dari biyu ‘Yan Shi’a ba su da
limami da zai koyar da su addini.
Tambaya a nan ita ce me yasa
‘Yan Shi’a suke dogara da
maganganun limamansu da suka
mutu a halin zamaninsu ya shige
kuma limamin wannan zamani har
yanzu bai bayyana ba?
Idan ‘Yan Shi’a suka ce, suna
dogara da maganganun
limamansu ne saboda su
Ma’asumai ne.
Sai mu ce: – idan limaman Shi’a
Ma’asumai ne kamar yadda suke
da’awa, shin masu rawaito
maganganunsu ma Ma’asumai ne?
Idan suka ce suma Ma’asumai ne.
Sai mu ce ashe ma’asuman na
Shi’a sun zarce goma sha biyu
kenan.
Idan suka ce a’a ba Ma’asumai ba
ne.
Sai mu ce ashe kenan zasu iya
karawa ko su rage ko su canja
maganganun limaman Shi’a.
Idan kuwa haka ne, to ‘Yan Shi’a
sun fi kowa asara, tunda har yanzu
ba su da limami na gaskiya
ma’asumi, wanda zai tantance
musu addininsu.
Idan suka ce limamunsu na sha
biyu ya yarda da ingancin littafin
Usulul Kafi, ya tabbatar da cewa ya
isarwa mabiyansu.
Sai mu ce: – Idan har hakan ya
tabbata, me yasa bai tantance
ingantattun hadisan ciki ba?
Idan suka ce duk hadisan ciki sun
inganta.
Sai mu ce wannan ya ci karo da
abin da manyan malaman Shi’a
suka tabbatar cewa, littafin Usulul
Kafi cike yake da hadisai na karya.
(11) Iya abin da ya inganta a
wannan Hadisin shi ne Fadin
Manzon Allah (S.A.W): – “Wanda
duk na kasance Masoyinsa to Aliyu
ma ya zamo Masoyinsa” kamar
yadda ya zo a ruwayar Imamu
Ahmad daga Hadisin Buraida.
Amma karin cewa: “Ya Allah kaso
mai sonsa ka yi gaba da mai gaba
da shi, zuwa karshe” akwai
malaman da suka yi magana a
kansa.
(12) A kaddara ma cewa Hadisin
ya inganta baki dayansa, to ba shi
da alaka da Halifanci ko limanci na
Sayyadina Ali (R.A) kamar yadda
Shi’a suke da’awa.
Saboda Hadisin yana magana ne a
kan wajabcin nuna soyayya ga
Sayyadina Ali (R.A). Abin dake
nuna hakan shi ne – Manzon Allah
(S.A.W) ya hada tsakanin soyayya
da kiyayya a cikin lafazin Hadisin.
Ita kuwa soyayya wajibi ce a nuna
ta ga dukkan muminai
gwargwadon imaninsa, kamar
yadda dalilai na Alkur’ani da Hadisi
suka tabbatar da hakan.
Ballantana nuna soyayya ga
mutum irin Sayyadina Ali (R.A)
wanda imaninsa da falalarsa da
matsayinsa suke a fili babu mai
inkarinsu.
Shi yasa ya tabbata a Hadisi cewa:
– “Babu mai son Sayyadina Ali
(R.A) sai Mumini babu mai kinsa
sai munafiki”
Kamar yadda ya tabbata cewa: –
“Son muta nan Madina alama ce ta
imani kamar, yadda kinsu yake
alama ta munafinci”
Kari a kan haka shi ne , ita asalin
kalmar “Maula” an samo ta ne
daga tushen kalmar “Walaya” Idan
aka karanta da yiwa wawun fataha
wacce take nufin soyayya da
taimakekeniya. Ba wai daga asalin
tushen kalmar “Wilaya” take ba
Idan aka karanta da yiwa wawun
kisra wacce ma’anarta shi ne
shugabanci.
Da kuwa daga asalin kalmar
“Wilaya” ne, sai Manzon Allah
(S.A.W) ya ce: “Man kuntu Walihi
fa Aliyun Walihi” ba zai ce “Man
kuntu maulahu fa Aliyun Maulahu
ba”
Wannan zai fito fili idan aka kalli
sababin da yasa Manzon Allah
(S.A.W) ya fadi wannan maganar.
Sababin kuwa shi ne Hadisin
Buraida wanda a cikinsa yake
bayanin yadda Sayyadina Ali (R.A)
ya raba ganimar yaki, sai ya zabi
wata kyakykyawar kuyanga daga
Khumusi har ya kusance ta. Sai
Buraida yake cewa sai na ji
haushin Sayyadina Ali (R.A).
Lokacin da na bawa Manzon Allah
(S.A.W) labarin abin da ya faru, sai
ya ce: – “Ya kai Buraida yanzu ka
dinga jin haushin Sayyadina Ali
(R.A)?
Sai Buraida ya ce: – lallai na ji
haushinsa.
Sai Manzon Allah (S.A.W.) ya ce:
-“Ya Buraida kada ka yi gaba da
Sayyadina Ali (R.A), saboda rabon
da zai samu na Khumusi ya fi
wannan kuyangar” a wata riwayar
ta Ahmad da Nisa’i, sai Manzon
Allah (S.A.W.) ya ce: – “wanda duk
na kasance masoyinsa to lallai
Sayyadina Ali (R.A) ya zamo
masoyinsa”. Ma’ana dukkan mai so
na, to wajibi ne ya so sayyadina Ali
(R.A).
Don haka Hadisin hujja ne a kan
‘Yan Shi’a da suke dogara wajen
tabbatar da shugabancin
Sayyadina Ali (R.A), domin ba shi
da alaka da lamarin shugabanci.
Dadin dadawa ayar da ‘Yan Shi’a
suke kafa hujja da ita a kan
wajabcin shugabancin Sayyadina
Ali (R.A) wato Fadin Ubangiji
(S.W.T) “Hakika masoyinku kawai
shi ne Allah da Manzonsa da
wadanda suka yi imani, masu
tsayar da Sallah da bayar da
zakka, masu yawan yin ruku’i”
Tana magana ne a kan wajabcin
nuna soyayya ga Allah da
Manzonsa da dukkannin muminai
kamar yadda jerin ayoyin ya nuna,
tun daga Fadin Ubangiji (S.W.T)
“Ya ku wadanda kuka bayar da
gaskiya kada ku riki Yahudawa da
Kiristoci a matsayin masoya” izuwa
Fadinsa “Wanda duk ya nuna
soyayya ga Allah da Manzonsa da
wadanda suka yi imani to hakika
rundunar Allah su ne masu galaba”
Idan ‘Yan Shi’a suka ce akwai
Hadisi da yake nuna cewa wannan
ayar ta sauka ne a kan Sayyadina
Ali (R.A), lokacin da ya bayar da
zakkar zobe, a halin yana cikin
ruku’i.
Sai mu ce malamai sun hakaito
maganganu guda biyar a kan
sababin saukar wannan ayar.
Maganganun su ne kamar haka: –
Ta daya: – Ayar ta sauka ne a kan
Sayyadina Ali (R.A)
Ta biyu: – Ayar ta sauka ne a kan
Sayyadina Abubakar (R.A) saboda
shi ne ya yaki wadanda suka yi
ridda
Ta Uku: – Ayar ta sauka ne a kan
Sayyadina Ubadata dan Samit,
Lokacin da ya barranta daga
kawancen da ya kulla da
Yahudawa.
Ta Hudu: – Ayar ta sauka ne a kan
kabilar Abu Musa Al-Ash’ari (R.A)
Ta Biyar: -Ayar tana magana ne a
kan dukkan muminai. Wannan
maganar ita ce wacce malamai
suka fi rinjayarwa, saboda ana
izina ne da lafazi gamamme ba
sababi mai kebancewa ba, kamar
yadda yake ka’ida a gurin
malaman tafsiri.
Banda wannan ma malamai sun
hadu a kan rashin ingancin Hadisin
Sayyadina Ali (R.A) na bayar da
zakka yana cikin Sallah. Kari a kan
haka malamai sun kawo dalilai
masu yawa a kan rashin alakar
ayar da Halifanci wanda wannan
‘dan littafin ba zai yiwu a kawo su a
ciki ba, don gudun tsawaitawa.
Amma dukkan mai son karin
bayani a kan haka ya duba
littattafan Tafsiri kamar Ibn Kathir
da Ibn Jarir da Tafsirin Imamu Al-
Razi da makamantansu.
(13) Wata tambaya dake da alaka
da wannan Hadisin ita ce: – su
waye suke gaba da Sayyadina
Aliyu (R.A) da Ahlu Al-Baiti?
Sa nannan abu ne cewa Ahlu Al-
Sunnah basa gaba da Sayyadina
Aliyu (R.A) ko wani daga Ahlu Al-
baiti, cikin Bani Hashim da Banil
Muddalib da Matan Manzon Allah
(SAW) da ‘ya’yansa da jikokinsa
da danginsa baki daya.
Littattafansu cike suke da ambaton
girmansu da rawaito falalarsu da
mutunta su, da nuna soyayya gare
su da rawaito Hadisansu da
fatawoyinsu da yin salati a gare su.
Kamar yadda garuruwan Ahlu Al-
Sunna da gidajensu, suke cike da
sunayen Ahlu Al-baiti kamar Aliyu,
Fadima, Hasan da Husaini da
sunayen Matan Annabi da
danginsa na Uwa da Uba irin abin
da ba zaka samu a garuruwan
‘Yan Shi’a da littattafansu ba.
Saboda su ‘Yan Shi’a sun zabi
wasu mutane ne ‘yan kalilan suka
ce su kadai ne Ahlu Al-Baiti, suka
yi watsi da ragowar suka kafirta su.
Domin cikin wadanda suka ce su
ne kadai suka rage a cikin
musulunci bayan wafatin Manzon
Allah (SAW) babu wani daga cikin
Ahlu Al-Baiti.
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita
ce: – wane irin so ake so a nunawa
Ahlu Al-Baiti fiye da irin son da
Allah da Manzonsa suka nuna da a
yi musu?
Idan so ake a nuna mu su soyayya,
wacce ta wuce gona da iri, ta
yadda zamu mayar da su tamkar
wasu alloli muna bauta mu su, to
tabbataccen abu ne cewa Ahlu Al-
Sunna, Allah kadai suke bautawa
ba tare da sun hada shi da kowa
ba. Wannan kuwa shi ne abin da
Allah ya turo dukkan Annabawa da
shi.
Wani abu mai mahimmanci da ya
kamata a sani shi ne – Bayan
Sayyadina Ali (R.A) ya hau gadon
Khalifanci, sakamakon kissan gillar
da a kaiwa Sayyadina Usman
(R.A), al’ummar musulmi sun kasu
kashi uku a kan fitintunun da suka
biyo baya na cikin gida kamar
haka: –
Na farko: – Wadanda suka yiwa
Sayyadina Ali (R.A) mubaya’a ciki
kuwa har da wadanda suka kashe
Sayyadina Usman (R.A).
Na Biyu: – Wadanda ba su yi masa
mubaya’a ba, kuma suka yake shi
kamar muta nan sham.
Na Uku: – Wadanda sun yi masa
mubaya’a, amma ba su goyawa
kowane bangare ba yaba a
yakokin da aka yi.
Wadannan su ne galibin manyan
Sahabbai, kamar Ibn Umar,
Usamatu dan Zaid, Sa’ad dan Abi
Wakkas da Imran dan Husaini da
Abubakarata da Muhammad dan
Maslamata (R.A), wanda Manzon
Allah (S.A.W) ya ce: fitina ba zata
cutar da shi ba.
Duk cikin wadannan bangarori
guda uku, masu ra’a yi na uku su
ne wadanda ra’a yin su ya fi da
cewa da masalahar al’umma kuma
shi ne ra’a yin da Hadisai
ingantattu suka goyi baya.
Abin da yake tabbatar da haka shi
ne , bangarorin da suka yaki juna
tsakanin Sayyadina Ali (R.A) da
Nana Aisha da Mu`awiya Allah ya
kara musu yarda, sai da suka
dawo suna yin nadama a kan
haka. Saboda daman sun yi yakin
ne don masalahar al’umma, amma
masalahar bata samu ba. A
maimakon haka, al’amura suka
kara rikicewa.
Nana Aisha (R.A) ta kasance, idan
ta tuna da abin da ya faru na yakin
Jamal ta kan yi kuka har sai
hijabinta ya jike da hawaye. Kamar
yadda aka hakaito daga Sayyadina
Ali (R.A) yana cewa: – “Madalla da
matsayin da Abdullahi dan Umar
da Sa’ad dan Abu Wakkas (R.A)
suka tsaya a kai. Idan daidai ne to
lalle ladansa yana da yawa. Idan
kuwa kuskure ne to lalle laifinsa
kadan ne”. A wani gurin kuma
cewa ya yi da dansa “Ya kai
Hasan, ya kai Hasan, lallai
mahaifinka bai san cewa wannan
lamari zai kai ga munin haka ba.
Mahaifinka ya yi burin a ce ina ma
tuni ya mutu shekara ashirin kafin
faruwar wannan lamari”
Hakama Dalha da Zubair (R.A)
dukkanninsu sun hadu a kan kada
a yi yaki a tsakanin bangaran
mutanen Sayyadina Ali (R.A) da
bangarensu, sai dai kaddara ta
riga fata.
Amma abin sha’awar shi ne , duk
cikin bangarorinnan guda uku basa
kafirta juna, kuma babu wanda
yake musun falalar dan uwansa.
Kamar yadda shi ma Sayyadina Ali
(R.A) ba ya musun falalar ragowar
Sahabbai, bai kuma taba kafirta su
ba. Hasali ma dai dai da mutanen
Sham da suka yake shi bai taba
cewa sun kafirta ba.
Daga cikin ‘Yan Shi’a masu
da’awar biyayya ga Sayyadina Ali
(R.A) aka fara samun wadanda
suka yi masa bore, suka fara kai
masa hari, suka kuma kafirta shi.
Daga karshe kuma su ne suka
zamo Ajalinsa.
Daga cikinsu ne aka fara samun
masu cewa: – Sayyadina Ali (R.A)
Allah ne, shi kuwa Sayyadina Ali
(R.A) ya dinga konasu da ransu a
cikin wuta wannan magana kuwa
har Malaman Shi’a sun hakaito ta
daga Ja’afar Al-Sadik .
Masu da‘awar bin nasa dai, wato
‘Yan Shi’a, su ne suka ki yi masa
biyayya ya rasa yadda zai yi da su,
har sai da ta kai yana la’antarsu,
yana siffanta su da yaudara da
ragwanci da rashin tunani ya dinga
burin ina ma a ce mabiya
Sayyadina Ma’awiyya dan Abu
Sufyanu (R.A) su ne mabiyansa.
Duk wadannan maganganu
tabbatattu ne kuma ingantattu
daga Sayyadina Ali (R.A) cikin irin
hudubobinsa da aka rawaito a
babban littafin nan da ‘Yan Shi’a
suke tinkaho da shi wato Nahjul
Balaga.
Hasali ma, duk bala’in da ya samu
Ahlu Al-baiti tun daga kan
Sayyadina Aliyu da Husaini (R.A)
da wadanda suka biyo bayansu,
‘Yan Shi’a ne, suka jefa su ciki.
Alal misali su ne suka rubutawa
Sayyadina Husaini (R.A) wasika
kimanin dubu suka yaudare shi,
suka nuna suna tare da shi, sai
bayan da yazo gurinsu, duk suka ki
fitowa su taimake shi, suka hada
kai da azzalumai, a karshe suka yi
masa kisan gilla daga baya kuma
suka fito suna kukan karya. Kamar
yadda bayani zai zo a kan wannan
nan gaba.
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita
ce, su waye makiya Ahlu Al-baiti
da Sayyadina Ali (R.A) na hakika ?
Wadanda suka jefa shi cikin bala’i
iri-iri tare da ‘ya’yansa, har ta kai
yana tsine musu, yana rokon Allah
ya musanya masa wasu mafiya
alheri kuma daga karshe suka
zamo ajalinsa, ko kuwa Ahlu Al-
sunna masu girmama shi?
Duk da cewa akwai maganar da
malamai suka yi a kan ingancin
Nahajul Balaga, amma mun yi
amfani da shi ne , domin ‘Yan Shi’a
sun yi imani da wannan littafi fiye
da yadda, suka yi imani da
Alkur’ani. Saboda su sun dauke shi
a matsayin wani littafi wanda babu
kuskure a cikinsa.
Amma shi kuwa Alkur’ani a gurin
‘Yan Shi’a, suna kallonsa ne a
matsayin wani littafi da aka canja
ma’anoninsa aka kuma yi kari da
ragi a cikinsa, kamar yadda
Yahudu da Nasara suka canja
Attaura da Injila wato “Bible”.
Dadin dadawa suna danganta
Jahilci da kuskure ga Allah, amma
ba su taba danganta hakan ga
limamansu ba.
Kamar yadda suka rawaito daga
Imamu Al-Ridha yana cewa: –
“Allah bai turo wani Annabi ba fa
ce sai ya haramta shan giya, ya
kuma tabbatar da akidar Bada”
wato danganta jahilci ga Allah.”
10) Sayyadina Ali (R.A) ya fada
cewa:- “Hakika kungiyoyi guda
biyu za su halaka a sababi na.
Kungiya ta farko su ne wadanda
suke zurfafawa wajen nuna min
soyayya, har hakan ya kai su ga
bin tafarki na karya.
Kungiya ta biyu su ne wadanda
suke zurfafawa wajen gaba da ni,
har hakan ya kai su ga bin tafarki
na karya.
Mafiya alherin mutane cikin abin
da ya shafe ni su ne wadanda suke
tsaka-tsaki. Ku zamo cikin
wadannan jama’a, ku kasance tare
da su, saboda taimakon Allah
(S.W.T) yana tare da jama’a” .
Hakika duk wanda ya kalli wannan
jawabi na Sayyadina Ali (R.A)
sannan ya auna kungiyoyin da
suke sabani a kan sha’anin
Sayyadina Ali (R.A), zai fahimci
abubuwa kamar haka.
Na daya Kungiyar farko da za su
halaka a sababin Sayyadina Ali
(R.A) su ne ‘Yan Shi’a masu da’
awar sonsa.
Saboda su ne suka allantar da shi,
suka fifita shi a kan dukkan
Annabawa suka ba shi matsayin
da ya wuce duk wani abin halitta.
Wannan kuwa ya ci karo da abin
da ya tabbata a cikin Al-kur’ani mai
girma da ingantattun Hadisai da
haduwar malamai cewa Allah shi
kadai ne abin bauta, Annabawansa
kuma sun fi kowa daraja da
matsayi.
Kungiya ta biyu da suka halaka a
sababin Sayyadina Ali (R.A) su ne
Khawarijawa da Nasibiyya,
wadanda ko dai suke kafirta shi, ko
kuma suke kallonsa a matsayin
munafuki ko azzalumi.
Wannan kuwa ya ci karo da abin
da ya tabbata a cikin Al-kur’ani mai
girma da ingantattun Hadisai da
haduwar malamai na tabbacin
imaninsa da wajabcin girmama shi
da nuna masa soyayya.
Mafiya alherin al’umma kan
sha’anin Sayyadina Ali (R.A) su ne
Ahlu Al-Sunna, wadanda suka ba
shi matsayi dai-dai da na shari’a.
Ba su allantar da shi ba irin yadda
‘Yan Shi’a suka allantar da shi. Ba
su kuma kafirta shi ba irin yadda
Khawarijawa suke kafirta shi.
11) Nuna soyayya wacce ta wuce
gona da iri, ta kauce daga kan tsari
na shari’a ba ta da maraba da
kiyayya. Dalili kuwa shi ne Allah
(S.W.T) ya bamu labarin cewa duk
wani wanda ya nuna soyayya ga
wani mutum, irin son da ya wuce
ka’ida ranar Alkiyama wannan
soyayyar sai ta zama gaba.
Misali a nan shi ne duk irin da’awar
nuna soyayya da girmamawa da
kiristoci suke nunawa ga Annabi
Isa (A.S) hakan ba zai amfane su
da komai ba ranar Alkiyama, za su
shiga makoma daya ne da
Yahudawa makiya Annabi Isa
(A.S).
Don haka da’awar da ‘Yan Shi’a
suke yi ta nuna soyayya ga
Sayyadina Ali (R.A) da Ahlu Al-
Baiti ba zata amfane su da komai
ba ranar Alkiyama, makomarsu
daya da Khawarijawa da Nasibiyya
masu gaba da shi.
12) Akwai malaman Shi’a da yawa
kamar Jabir Aga’i da suke tuhumar
Manzon Allah (S.A.W) cewa shi ne
sababin fadawar Al’umma cikin
Sabani da kashe-kashe ta yadda
har ya koma ga Allah (S.W.T) bai
bayyana waye halifansa ba. Sai
wannan yake nunawa a fili cewa
da’awar da ‘Yan Shi’a suke yi ta
ayyana Sayyadina Ali (R.A.) a
matsayin halifa a Gadir Khum bata
da tushe da asali.
13) Manzon Allah (S.A.W.) ya yi
hudubobi masu yawa bayan
hudubar da ya yi a Gadir Khum,
amma duk cikin wadannnan
hudubobi bai sake ambatar
Sayyadina Ali (R.A) ba.
A maimakon hakan sai Manzon
Allah (S.A.W) ya dinga ambaton
Sayyadina Abubakar (R.A.), yana
nuna irin falalarsa da matsayinsa
da fifikonsa a kan dukkan
Sahabbai.
Ya bayyana shi a matsayin wanda
ya fi kowa amfanar da Manzon
Allah (S.A.W.) ta bangaren
dukiyarsa da ransa.
Ya sa aka toshe kofar kowa da
take cikin masallacinsa, in banda
kofar Sayyadina Abubakar (R.A).
Ya bayyana cewa da zai riki wani
badadi ba Allah ba to da ya riki
Sayyadina Abubakar (R.A).
Ya sanya shi a matsayin halifansa
wajen yiwa mutane Sallah, ta
yadda yaki yarda da kowa ya
jagoranci mutane in banda
Sayyadina Abubakar (R.A). Har ta
kai da lokacin da ya ji muryar
Sayyadina Umar (R.A) ya tayar da
Sallah a matsayin limami, sai ya
ce: -“Sam sam ba zata sabu ba
Allah da Manzonsa ba su yarda da
kowa ba sai Sayyadina Abubakar
(R.A)”
Duk wadannan hudubobi sun faru
ne lokacin da Manzon Allah
(S.A.W.) yake cikin rashin lafiyar
ajali, kafin komawarsa izuwa ga
Allah (S.W.T).

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “DARASI NA TARA (9)SHUBUHOHIN SHI’A A MAHANGAR SHARI’A(Malam .Aminu Ibrahim Daurawa)”
  1. nasirus sunnah sokoto Avatar
    nasirus sunnah sokoto

    Alhamdulillah

  2. […] Source: DARASI NA TARA (9)SHUBUHOHIN SHI’A AMAHANGAR SHARI’A(Malam .Aminu Ibrahim Daurawa) […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories