FALALA ASHIRIN (20) TA WATAN RAMADAN( Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

1, A cikin sa aka saukar da
Alkurani mai girma,
Bakara 185
2, Dukkan littafan Allah mai girma,
a cikin sa aka saukar da su,
takardun Annabi Ibrahim a daran
farko na watan, Attaurar Annabi
Musa a ranar 6 ga watan, Injilar
Annabi Isa 13 ga watan, Alkur’anin
Annabi Muhammad saw, a ranar
24 ga watan, Musnad Ahmad,
shaik Albaniy ya ingantashi.
3, Ana bude Kofofin Aljannah a
cikin watan,
4, Ana rufe kofofin wuta
5, Ana daure kangararrun shedanu
6, Ana bude kofofin Rahma
7, Ana bude kofofin sama
8, mai kira yana kira, ya mai
neman alkhairi gabato, ya mai
neman sharri, kayi nisa
9, A ko wanne dare, Allah yana
yanta bayi daga wuta
10, A cikin watan akwai daran
lailatul kadri wanda yafi wata dubu,
11, Ana kankare zunubin shekara,
Annabi saw yace, Daga Ramadana
Zuwa Ramadan aka kankare zanubi
duka, mutukar an nisaci kaba’ira
12, An durmuza hancin, Duk
wanda Ramadana ya kama har ya
wuce baiyi aikin da zaayi masa
Rahma ba.
13, Umra a cikin watan Ramadan
daidai yake da aikin hajji tare da
Annabi, saw a wajan lada.
14, watan da akafi shiga I’itikaf, a
goman karshe
15, Watan da ake amsa Addu’a
16, Watan da akeson yawaita
Karatun Alkur’ani mai girma, akalla
sauka hudu, duk sati daya.
17,Watan Alkhairi da kyauta da
ciyarwa, da samun dumbin lada,
duk wanda ya ciyar da mai azumi,
zai kara samun lada kamar yayi
azumi.
18, Watan da akafi yawan kiyamul
laifi da tarawih da Tahujjud da
Asham, don kara kusanci da Allah.
19, Watan neman nasara akan
makiya, Sahabbai sukanyi amfani
da watan Ramadan, wajan addua
mai tsanani akan makiya.
20, watan sada zumunta,da
karfafa, yan uwantaka ta
musulunci,
Allah ka kaimu Ramadan, da imani
da son Allah da Manzonsa, Ka
karbi ibadun mu ka yafe mana. Ya
Hayyu Ya Qayyum.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates