Fatawoyin Rahama By Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo 5th November 2022

Danna nan domin shiga karatu Online

Shimfiɗa : Tsokaci game da faɗin Allah ” Lallai waɗanda suke musanya alƙawarin Allah da rantse-rantsensu da wani ɗan farashi ƙanƙani, waɗannan ba su da wani rabo a lahira, kuma Allah ba zai yi musu magana ba, kuma ba zai dube su (duba na rahama) ba a ranar allƙiyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai raɗaɗi” (Suratu Ali Imran: 77)

Tambayoyi da Amsoshi

  1. Shin da Gaske ne sau uku Allah yana gafarta wa Iblis amma Iblis ya ƙi karɓar gafarar da Allah ya masa?
  2. Wanda aka ba shi ajiya zai ya biya idan abin da aka bashi ajiya ya salwanta?
  3. Ya hallata mutumin da yake zaune a Kano ya ba da dala ($) ga abokin sa ya canza masa ita zuwa naira (NGN) a Abuja?
  4. Ya tabbata Annabi ﷺ ya hana cin kifi da shan nono a tare?
  5. Kwanaki nawa ne jinin biki yake ɗaukewa?
  6. Mace da jinin haila ya sameta tana tsaka da aikin Hajji – yaya za ta yi da ɗawafin Ifaadha in har lokacin dawowa gida ya yi jinin bai tsaya ba?
  7. Wanda zai yi wankan tsarki yayi Bismillah da farko, in ya zo wanke wajen najasa sai ya sake Bismillah?
  8. Ya hallata mace ta rinƙa ziyartar maƙabarta domin yin addua ga mahaifanta da suka rasu?
  9. Akwai addua ta musamman bayan Sallar Walaha!
  10. Menene hukuncin mutum ya ba da tsofaffin kuɗi tare da ƙari domin a ba shi sababbi?
  11. Hukuncin mutum ya ba da kuɗinsa ga mai sanar POS ya haɗa da nasa da yarjejeniyar za a bashi wani kaso na riba a ƙarshen wata?
  12. Wadda ta tsinci kaza ta yi cigiya ba a samu mai ita ba, in kazar ta hayyafa za ta yi sadaƙa da ‘ya’yan da kazar ta ƙyanƙyasa?
  13. Shin Ƙissar Haruta da Maruta ta inganta?
  14. Shin idan mutum ba ya sallar dare daga baya sai ya fara yi saboda wasu matsolin rayuwa-Allah ba zai karɓa masa ba?
  15. Mutum zai iya Sujjada domin neman biyan wata buƙata?
Download
Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates