Assalamu Alaikum.
Da yawa daga cikinmu mukan sami kanmu cikin Hali na rashin lafiya, wannan rashin lafiya ko ya zamto mai taƙaitaccen zango, kaman irin ciwon kai da yake damun mutum ya kuma kau na lokaci kaɗan. Ko kuma ciwo ne mai lazimtar jiki, wanda yake tafiya ya dawo ko kuma Ya lazimcemu ako wani lokaci. Amma da zarar mun sami kanmu cikin wannan irin ciwo yawancin mu mukan garzaya ne zuwa Chemist domin neman maganin da zai kawar mana da wannan ciwo cikin gaggawa. Toh Haƙiƙa shi kansa irin wannan ɗabi’ah a likitance bai dace ba, sabida yawancin magunguna da muke sha suna da illoli irin tasu, wanda su kansu masu yin maganin suna bayaninsu, wani lokaci kuma Masana ne suke bincike su gano illolin irin wannan magunguna. Toh matsalar ba wai kada a sha maganin bature ba. A’a. Musulunci bai hana shan maganin bature ba. Amma bai yarda a sha ba a bisa ƙa’idah ba. Ya zamto lokacin da zaka sha maganin ka tuntuɓi likita ya rubuta maka maganin da ya dace da ciwonka. toh haka shine daidai, sabida kada ka jefa kanka ga halaka wurin shan magungunan da basu da alaƙa da ciwon dake damunka kuma daga ƙarshe su haifar maka da illolin da bazaka iya kau dasu ba.
Toh bayan Magani na likita akwai wani hanya wanda maluman musulunci suka jarraba kuma suka tabbatar da tasirinsa?
Anan zamuyi bayani kan yin magani da suratul fatiha kaman yadda Imam ibnul Qayyim ya kawo a “Zadul Ma’ad, da Al-jawabul Kafi, da madariju-ssalikeen”…..
Yake cewa:
“Wani lokaci ciwo ya riskeni A makkah, kuma ban samu likita ba kuma babu magani a tare dani, sai na kasance ina jinyan kaina da suratul fatiha, kuma ina ganin tasirin ta mai ban mamaki, ina ɗiban ruwan zamzam, sai in karanta suratul fatiha acikinsa da yawa, sannan sai insha, sai insamu cikakken sauƙi, sai na kasance bayan haka ina dogara wurin yin jinya da wannan hanya, ta karanta suratul fatiha acikin ruwan zamzam, kuma ina amfana da ita sosai, har na kasance ina faɗa wa mutane wannan hanya da nakebi, kuma da yawa daga cikinsu suna samun sauƙi cikin gaggawa”
-Zadul Ma’ad 4/178
-Aljawabul Khafi 21
Sannan ya sake cewa:
Amma shaidan jarraba yin jinya da suratul fatiha ba za’a iya kididdige ta ba, a lokuta da dama anyi amfani da ita kuma ta amfanar, nima na jarraba ta kuma na faɗa wa wasu sun jarraba. Musamman lokacin zama ta a Makkah, wasu lokuta na kan sami zafi mai tsanani mai firgitarwa, har wani lokaci takan kai ga kusan hana ni motsi, a lokacin ɗawafi da waninsa, sai in karanta suratul fatiha in kuma shafa awurin, Sai inji kaman an cire ciwon baki daya. Na gwada hakan lokuta da dama, nakan kuma ɗauki Kofi da ruwan zamzam a ciki sai in karanta suratul fatiha aciki da yawa, in kuma sha, sai insamu amfani da kuma ƙarin ƙarfi wanda ban saba gani ba acikin wasu magunguna da nake amfani dasu. Amma wannan tasiri na suratul fatiha tana aukuwa ne da gwargwadon imanin mutum da kuma yaƙininsa.
– Madariju-ssalikeen 184.
Wannan bayanan Ibn Qayyim kenan.
Nima mai rubutu nasha jarraba yin jinya da suratul fatiha kuma insamu sauƙi cikin gaggawa da samu kuzari.
Amma kaman yadda kuka sani ne, Addu’a tana tasiri ne gwargwadon karfin imanin mutum, wani zaiyi addu’a yana kokwanto ko baza’a ƙarɓa ba, to wannan Addu’arsa bazata je ko ina ba, wani kuma zaiyi addu’a yana da yaƙinin za’a ƙarba, wannan Da yardan Allah addu’ar sa zata ƙarbu.
Ankarɓo Hadisi daga Aba Hurairah Allah ƙara masa yarda yace:
Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: ku roƙi Allah kuna masu yaƙinin za’a amsa muku, ku sani Allah baya karɓan addu’a daga zuciya rafkananniya, mai wasa.
Sahihin Hadisi Turmuzi ya rawaito. 3479
Yana daga cikin sharaɗin karban addu’a, ya zamto kanayin addu’an da yaƙini cewa Allah zai amsa, kaman yadda wannan hadisin ya nuna, a lokacin da kake rokonsa kada ya zamto kana kokwanto, shin Allah zai karɓi addu’annan kuwa? A’a abin da ya dace kayi shine ka ƙudurce a ranka cewa Allah ya riga ya karɓa. Sannan sai kuma kada kana addu’a zuciyanka yana wani wuri, sai ka tara zuciyarka wuri ɗaya, ka fuskanci Allah, kuma ka guji ƙetare iyaka wurin Addu’a. Wannan suna daga cikin sharuddan karɓan addu’a sai a kula dasu.
Daga yau sai kayi ƙoƙarin fara gwada wannan irin jinya, kuma Insha’Allah zaka ga cin Nasara fiye da yadda kake zato da sharaɗin kayishi da yaƙini. Inkana da wani mara lafiya da aka gwada magunguna da yawa ba’a samu mafita ba, ka gwada wannan Insha’Allah za’a sami mafita. Sannan kuma wurin yin jinyan bawai sau ɗaya ake karantawa ba. A’a so samu kullum a rinƙa yi har sai an samu sauƙi.
Wani zai iya tambaya, shin ina Ibnul Qayyim ya samo dalilin yin wannan jinya da suratul fatiha?
An tambayi Sheikh Bin Baaz Allah ya jiƙansa.
Tambaya: Shin ya halatta ga Musulmi yayi karatu ya tofa a ruwa domin yin jinya?
Amsa: Yace: Manzon Allah ya kasance idan wani ciwo ya sameshi yakanyi tofi acikin hanunsa sau uku, ya karanta suratul ikhlas, da falaƙi da Nasi, ya kuma shafa a jikinsa lokacin bacci, ya fara da kansa, da kuma fuskarsa, da kuma ƙirjinsa, kaman yadda Aisha matarsa Allah ya ƙara mata yarda ta bada labari acikin hadisi ingatacce. Sannan kuma Mala’ika Jibril ma yayi wa annabi Ruƙyah lokacin da annabi yayi rashin lafiya.
Kuma annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yayi wa Tsabit Bin Khais karatu a ruwa yayi umarni a zuba masa ruwan, kaman yadda abu dawud ya rawaito. Da dai sauran ire-iren wa’innan abubuwa da aka rawaito.
Majmu’ul fatawah wa maƙalati-sshaikh bin Baaz 8/94.
Domin ƙarin bayani da kuma samun nassin addu’oin da annabi yayi sai ku duba fatawar, akwai copy a online.
A Wannan fatawa da muka kawo ta Ibn Baaz.
ya halatta mutum yayi wa kansa Ruƙya, ko kuma yasa ayi masa, duka ya tabbata daga manzon Allah.
Kuma kaman yadda aka rawaito annabi yayi da Surori uku na ƙarshen Qur’an ya halatta ayi da wasu wanda basu ba.
Leave a Reply