Tambaya: Assalamu alaikum. Don Allah Malam mutum ne ya aje rago da niyyar zai yi layya sai Allah ya yi masa rasuwa, ko ya halatta a yi mai layyar bayan mutuwarsa? Wassalamu alaikum.
Amsa: Wa’alaikumus-Salam Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh. Wanda ya ajiye rago da niyyar yin layya sai ya mutu kafin yayi to Za’ayi masa layya da wannan rago da ajiye.
An tambayi Ibnul Qasim Game da mutumin da zai sayi dabbar layya sai ya mutu kafin ya yanka, shin magadansa zasu yanka a madadinsa?
Sai yace: Abinda yafi kyawu shine Magadansa zasu yanka a madadinsa idan sun ga dama. Idan suka ƙi sukayi rowa to dukiyar su ce. Amma idan an riga an yanka to ba za’a siyar da naman ba, magada zasu rabata a matsayin gado.
A duba Albayanu wattahsil: Shafi na 372
Wannan itace fatawar Imamu Malik kamar Yadda Muhammad Ibnu Rushd yayi ta’aliƙi a ƙarƙashin wannan magana ta Ibnul Qasim.
Wannan yake nuna cewa abinda ya dace magada suyi shine su yi wannan layya a madadin wannan mamaci nasu, kuma ladan zai same shi da izinin Allah. Allah shine mafi sani
Domin tura taka tambayar danna nan
Leave a Reply