KASAN KANKA DA KANKA ( TAMBAYOYI 50)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

Muna cikin wani zamani, da
mutane, sunfi damuwa da bayani
akan wasu fiye da kansu, sunfi
binciko laifin wasu fiye da nasu,
Sayyadina Umar Yace kuyi kanku
hisabi kafin ayi muku, Abubawan
da suke jawo tsira, Bautawa Allah
shi kadai da iklasi, akan sunnar
Manzon Allah, a cikin Akida, da
Ibada, Da mu’amalah, da Halaye
masu kyau, yi kanka tambaya,
hamsin don kasan matsayinka :
Allah yasa mu dace :
1- waye ya yika ?
2- mai yasa ya yika ?
3- kai waye ?
4- A ina kake ?
5- mai kake yi ?
6- Ina zaka ?
7- mai zai faru ?
8- mai kafi so a rayuwarka ?
9- mai kafi ki rayuwarka?
10- Duk abinda kakeyi, kana da
hujja a sharia?
11- su waye abokanka?
12- Yaya zamanka da iyayanka?
13- Yaya zamanka yake da
iyalanka?
14- Wace kungiya kakeyi don me?
15- A kwai wani yanzu haka da
bakwa shiri da shi?
16- Tsakaninka da Allah ka taba
cin amanar wani?
17 Kanayin karya?
18- Kana Dun guma ashariya?
19- Yaya zamanaka da
makotanka?
20- Wace shedar ilmi kake dauke
da ita?
21- kana salloli a Jam’i musamman
a masallaci?
22- yaya alakar ka da danginka
take ?
23- shin kana sada zumunta?
24- shin kana bayar da sadaka ?
25- shin kana karanta Alkur’ani mai
girma?
26- kana azumin litinin da
Alhamis?
27- kana sallar Shafi’i da wuturi?
28- kana zuwa asibiti domin ziyarar
marasa lafiya?
29- Kana yawan saba alkawari ?
30shin kana azumtar kwanaki
masu haske, ranar sha uku, sha
hudu, sha biyar?
31- shin kana kiyamul- laili?
32-kana umarni da kyakyawa da
hani da mummuna?
33- kana zuwa aiki akan kari kuma
ka tashi akan lokaci?
34- kana zuwa gaban malami
domin daukar karatu?
35-ka tabbatar abinda kake ci halal
ne?
36- kana kuwa damuwa da halin
da yan uwanka musulmi suke ciki?
37- kana taimaka marayu kuwa?
38- salati nawa kake yiwa Annabi
saw kullum?
39- Istigfari nawa kakeyi kullum?
40- kana zuwa makabarta domin
tuna lahira?
41- kana zuwa taaziyya da sallar
Jana’iza?
42- ka taba yin kuka saboda tsoran
Allah?
43- shin kana yiwa dukkan
musulmi sallama ko kuwa sai
wanda ka sani?
44- kanayin rantsuwa akan karya
kuwa?
45- kana shan taba ko wiwi ko giya
ko hodar iblis?
46- kana jin kade- kade, da wake-
wake?
47- kana aske gemunka?
48- ka taba karbar cin hanci?
49- kana kyautawa iyalanka?
50- kana gaba da wani kuwa?

45 responses to “KASAN KANKA DA KANKA ( TAMBAYOYI 50)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)”
 1. mallam Allah kasa mudace ameen da irin gudummawar da kake bawa addinin musulunci Allah yasaka maka da Mafi Girman alkhairi mafifici duniya da lahira

 2. Bala adamu Avatar

  Mal allah yasaka da alhairi

 3. Ahmed Tanimu katsina Avatar
  Ahmed Tanimu katsina

  Allah yasa mudach malam minene hukuncin wanda yayi zambu cikin Amince

 4. saifullahibibraheem Avatar
  saifullahibibraheem

  may ALLAH REWARD YOU AMEEN

 5. naim aminu ggknk Avatar
  naim aminu ggknk

  Assalamu alaikum, Malan Allah ya sakamaka da alkhairi ya sanya aljanna ce sakamakonka, kuma ya sa ka kara jajircewa wajen fadakar da yan uwa musulmai Allah ya karamaka ilmi da Taqwa da wadata. AMEEN

 6. Amina Salisu Avatar

  Allah(swt) ya saka ma Malam da Alkhairi mu kuma Alummar Musulmi Allah yabamu ikon aiki da koyarwar Ma’aikin Allah (saw) Ameen.

 7. albashir sani sdosa Avatar
  albashir sani sdosa

  malam Allah yasaka da alkhairi

 8. SANUSI ABBA MUSAWA Avatar
  SANUSI ABBA MUSAWA

  Mal. Allah ya saka maka da alkhairi ya qara maka lafiya ameen.

 9. habiba Avatar
  habiba

  Allah ytaimaki malam yasaka masa da
  alkhairi

 10. sani ali Avatar
  sani ali

  mal mongodi Allah yabiyaka ameen Allah yabarmu tare ameen

 11. Halima mamman Avatar

  Allah sakawa Malam da Alhairinsa amin

 12. ADO AHMAD Avatar
  ADO AHMAD

  Allah ya sakawa malam da alkhairi

 13. sumayya maigari Avatar
  sumayya maigari

  Allah yasakawa malam da alhairi yakara bashi ikon tunatar da al umma akan hanyoyi nagari

 14. Allah ya saka ma malan da alkairi

 15. Yaa'uu Avatar
  Yaa’uu

  Allah yasaka

 16. Alameen Avatar
  Alameen

  Allah ya sakawa malam da alkhairi malam meye hukuncin mai zinar hannu kuma wani hanya zai bi ya kubuta! daga alameen mai littafi

 17. ALLAH YA KARAWA MALAM DAUKA KA DA TAIMAKO AKAN AL’UMMAR ANNABI MUHAMMAD (S.W.A) AMEEN.

 18. IBRAHIM HUDU Avatar

  ALLAH (S.W.A) YA KARA BASIRA.

 19. shamsu dalha Avatar
  shamsu dalha

  Allah ya saka da alkhairi malam amin 👏

 20. Ibrahim Abdulmumini Doguwa Avatar
  Ibrahim Abdulmumini Doguwa

  Muna Dada Rokon Allah Daya Sakawa Malam Da Alkhairi, Ameen

 21. Ibrahim Abdulmumini Doguwa Avatar
  Ibrahim Abdulmumini Doguwa

  Allah Yasakawa Malam Da Alkhairi, Ameen

 22. Ibrahim Abdulmumini Doguwa Avatar
  Ibrahim Abdulmumini Doguwa

  Ameen

 23. Ibrahim Abdulmumini Doguwa Avatar
  Ibrahim Abdulmumini Doguwa

  Ya
  Allah
  Kasa
  Ayi
  ARFAT
  Lfy.
  Ya
  Allah
  Kakarbi
  Ibadun
  mu
  Kabamu
  Dacewa
  Duniya
  da
  Lahira,
  Ameen

 24. Amina Salisu Avatar

  Allah ya sakama malam da alkhairinsa ameen.

  1. muhd lawan Avatar
   muhd lawan

   SALAM, malam, name taba sakin mata sau biyu sai tayi aure har ta haihu a wajen wani ya fito ta dawo hannu name muka sake rabuwa. ko zamu sake daura aure? Allah ya taimaki malam.

 25. Nura Avatar
  Nura

  Allah Saka Wa Mallam Da Alkhairi Ameen

 26. shamsu yusuf Avatar

  ALLAH YASAKAWA MALAM DA ALKAIRI

 27. Rabson dan saurayi Avatar
  Rabson dan saurayi

  ALLAH yasaka

 28. SULEIMAN SHEHU ABUBAKAR Avatar
  SULEIMAN SHEHU ABUBAKAR

  ALLAH YA SAKAWA DUK WANDA YA BA DA GUDUMMAWA WAJEN ILMANTAR DA AL’UMMAR MUSULMI TA WANNAN SASHIN SADARWAR DA ALHERI.

 29. Abubakar lawan jamis Avatar
  Abubakar lawan jamis

  Allah ya kara lfy malan aminu ibrahin daurawa

 30. shamwilu yunusa danmarabu Avatar
  shamwilu yunusa danmarabu

  assalamu alaiku Allah yasakama Mal da alkairi amen Mal tanbayata ananshine Mal zan iya takar yarinyar da zan aura innabiya sadaki kafin adauramana aure
  wassalam Mal ahuta lfy

 31. Ibn jafar Avatar
  Ibn jafar

  Malam minene hukuncin wanda yashekara 20 zuwa 21 amma baitaba mafarkiba ma.ana dashida macce

 32. Ibn jafar Avatar
  Ibn jafar

  Mal.dafatar katashi lfy mal.miye hukuncin wanda yayi shekara 20 zuwa 21 baitaba mafarkiba ma.ana tare da macce

 33. fauza Avatar
  fauza

  Assalamu Alaikum.mallam danAllah ina da tambaya wai ko ya halarta idan mutum.na neman biyan bukata ya zubarda jinin dabba duk dan Allah ya biya masa bukatar sa

  1. Ahmad Avatar
   Ahmad

   Fatan al kairi

 34. Nafisa nazir adam Avatar
  Nafisa nazir adam

  Allah gafarta malam, menene hukuncin wanda yake gyaran girar idanu, ba wai ya aske ta gaba daya ba, yayi mata gyara ne, kamar gyaran fuska. Na gode

 35. Salisu mz Avatar
  Salisu mz

  Allh yasakawa mal. Da alkhairi, amin

 36. muhammadjinjiri Avatar

  Allah ya sakama da alkairi malam yabiya ka da gidan aljannatul firdausi

 37. ABDUL IBRAHIM Avatar

  malam inason inji tarihin sunan rahikalkaddi

 38. Aliyu abdullahi Avatar
  Aliyu abdullahi

  Salam malam menene hukanci mai saurin bacin rai da kuma fishi sanan kuma bashida hakuri daga aliyu unguwa uku matsula layin dan jos

 39. Malam ya hallata mutum mai JAR suma ya rinqa yi mata dying ma,ana ya rinata ta zama BAKA domin ya batar da jan nata ?

 40. jamilu musa Avatar

  salama alaikum yan uwana musulmi

 41. Rabiu musa kaita Avatar
  Rabiu musa kaita

  Allah ya saka da alkhairi.

 42. kabiru alhassan rabi,u Avatar
  kabiru alhassan rabi,u

  Allah yasaka da alheri malam

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: