Bayan yabo da kirari ga Allah, da
salati, da sallama, ga Annabi saw,
Malam ya bude da ayar da tayi
magana akan Amana da Dan
Adam ya dauka, bayan Allah ya
bijirar da ita ga sammai da kassai
da duwatsu, sunki dauka saboda
wahalarta.
1- Magana akan kadaita Allah da
bauta.
2- Dacewa da gamaiwar Addinin
musulunci ga duk duniya.
3- sakon manzan Allah saw ya
shafi kowa duk duniya.
4- Addinin musulunci, yayi kira
zuwa ga dukkan wani hali na
kwarai, da mu’amala mai kyau
5- Addinin musulunci, yana da
sauki wajan aiki, kuma yana
kunshe da rahma,
6- Addinin musulunci, yayi kira
zuwa ga bawa dukkan mai hakki,
hakkinsa.
7- Addinin Allah amana ne a
wuyan ko wanne musulmi, ya kare
shi, ya yada shi, da duk damar da
Allah ya bashi, ko wacce iri ce.
8- duk matsalolin da musulmi suka
fada dalilinsa shine, nisa da
koyarwar addinin su.
9- Shariar musulunci itace ta dace
da ko wanne lokaci da zamani da
guri, da yanayi.
10- kira ga musulmi su hada
kansu, akan Littafin Allah da
sunnar manzon Allah saw.
11- Matsalolin da musulmi suka
shiga na kaskanci da wulakanci da
cin kashi daga makiya musulunci,
duka ya faru ne, saboda rauni da
riko da koyarwar musulunci,
12- Malam yayi kira ga masu mulki
da malamai da yan boko, da yan
jarida da duk wani mai dama a
hannu da yayi amfani da ita wajan
yada addini da kareshi,
12- Malamin yayi magana gamai
da rikici tsakanin musulmi, da
makiya addini suke rura wuta ya
kamata ayi taka tsan tsan.
13- Malam yayi kira ga masu kudi
da suyi amfani da kudin su, wajan
nema da kashewa ta hanyar da ta
dace,
14- Malama yayi kira ga Alhazai da
suyiwa Allah godiya bisa niima da
Allah yayi musu ta zuwa wannan
waje.
15- Malam yayi magna akan
girman wannan rana da falalar ta.
16- malam yayi magana akan
wajabcin koyan aikin hajji da yinsa
da ilmi akan koyarwar Annabi saw.
17- Malam yayi magana cewa mu
tuna da ranar alkiyamah da
abubuwan da zai faru a wannan
rana na tsanance- tsanance, da
wuta da
aljannah ga wanda suka cancan
ta,
18- a karshe malam ya cika
khudubarsa da Addua da
musulmin duniya da samun izza da
daukaka da kuma mummmuna r
addua ga makiya addini Allah ya
trwatsa su, da kuma addua ga
Allah ya bamu kyakyawa a duniya
da lahira.
19- ya cika da salati da sallma ga
Annabisaw da iyalan gidansa da
sahabban sa, da tabiai, da
dukkuan mutane na kwarai bayn
addua ga shuwagabanni da Allah
ya taimkesu wajan jn ragamr
al’umma kuma ya basu
mashawarta na kwarai.
Leave a Reply