MAGANGANUN MANYAN MALAMAI
A KAN SUNNAH DA MAQALE WA
MAZHABOBI (2).
Ci gaba
Mafiya shahara daga cikin
wadannan Mazhabobi wadanda
ra’ayoyinsu suka yadu cikin
duniyar musulunci su ne:
1. Mazhabar Hanafiyya: An gina ta
a kan koyarwar Imam Abu Hanifa
Nu’uman bin Thabit. An haifi Abu
Hanifa a Iraqi, kuma ya rayu
tsakanin shekara tamanin zuwa
dari da hamsin bayan hijra.
(80-150 A.H.)
2. Mazhabar Malikiyya: Dalibai da
mabiya Imam Abu Abdullahi Malik
dan Anas Al’asbahiyyu, mutumin
Madina, suka gina wannan
mazhabar. Ya rayu tsakanin
shekara ta casa’in da uku zuwa
dari da saba’in da tara bayan hijar
Manzon Allah (S.A.W.). (93-179
A.H.)
3. Mazhabar Shafi’iyya: An gina ta
ne a kan koyarwar Imam
Muhammad bin Idris As-shafi’i Al-
Qurashi. Ya rayu tsakanin shekara
dari da hamsin zuwa dari biyu da
hudu bayan hijira (150-204 A.H.),
kuma ya yi karatu a wurin Imam
Malik dan Anas.
4. Mazhabar Hambaliyya: Mabiya
da daliban Imam Abu Abdur-
Raman Ahmad bin Hambali suka
gina wannan mazhabar. Imam
Ahmad ya rayu a tsakanin shekara
ta dari da sittin da hudu zuwa dari
biyu da arba’in da daya bayan
hijira (164-241 A.H.), kuma a cikin
malamansa akwai Imam Shafi’i,
Imamul Bukhari da kuma Imam
Muslim.
Leave a Reply