LADABI DA BIYAYYA HALAYE NE ABIN KOYI GA MUTANEN KIRKI(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

LADABI DA BIYAYYA HALAYE NE
ABIN KOYI GA MUTANEN KIRKI:
‘Yan uwa na masu albarka, mu
sani fa yin ladabi ga wanda ya fika,
da rusunawa abokin mu’amala, da
yin sassauci ga abokin zama, da
dabi’ar saukin kai duk ba tsoro
bane, halin kamala ne, da dattaku
da nuna yakamata.
Hakika halin kirki da dabi’ar
nagarta abin koyi ne da ban
sha’awa, kuma dukkan iyaye
zuriyar su na gadon halayen su,
pls kai wani hali kake son gadarwa
iyalan ka?
Ina amfanin ka zamo mai
tsanantawa wajen kausasawa da
munanawa kowa? Ko nuna rashin
kunya da kin girmama manya? Tir
da rayuwar wanda furucin sa da
halayen sa suke cutar da mutane.
Addinin islama ya shiryar damu
turbar halin karimci da mutumta
juna, don haka ake son nuna halin
nagarta ga kowa ta hanyar koyi da
rayuwar Annabi saw.
Yana daga alamun riko da addidi
da cikar hankali ka zamo mutumin
kirki, mai nuna halin girma wajen
rintse harshe, kamewa daga zage-
zage, kuma ka nisanci munanan
halaye ko wulakanta mutane. Ka
zamo mai girma kowa musamman
iyaye, shugabanni, malamai da
duk wanda ya fika. Kuma ka zamo
mai sauki ga wadanda ke
abokanka, ko wadanda ke kasa da
kai.
Hakika dukkan aiyuka suna tare da
niyya don haka kayi kokarin yin
komi don neman yardar Allah,
kada da’ar ka ga mutane ta zamo
don kwadayi ko nufin yaudara.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories