Ma'anar Cewa Allah Ya Halicci Annabi Adam A Surar Sa

Danna nan domin shiga karatu Online

Assalamu Alaikum warahmatullah.

Bukhari Da Muslim sun riwaito daga Abi Huraira(Radiyallahu Anhu) Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : خَلَقَ اللَّهُ آدَمَ عَلَى صُورَتِهِ طُولُهُ سِتُّونَ ذِرَاعًا فَلَمَّا خَلَقَهُ قَالَ اذْهَبْ فَسَلِّمْ عَلَى أُولَئِكَ النَّفَرِ مِنْ الْمَلائِكَةِ جُلُوسٌ فَاسْتَمِعْ مَا يُحَيُّونَكَ فَإِنَّهَا تَحِيَّتُكَ وَتَحِيَّةُ ذُرِّيَّتِكَ فَقَالَ السَّلامُ عَلَيْكُمْ فَقَالُوا السَّلامُ عَلَيْكَ وَرَحْمَةُ اللَّهِ فَزَادُوهُ وَرَحْمَةُ اللَّهِ فَكُلُّ مَنْ يَدْخُلُ الْجَنَّةَ عَلَى صُورَةِ آدَمَ فَلَمْ يَزَلْ الْخَلْقُ يَنْقُصُ بَعْدُ حَتَّى الآن

“Allah ya halicci Adam(Alaihissalam) a bisa surarsa, yana da tsawon zira’i sittin, bayan da Allah ya halicceshi sai yace masa ka tafi kayi sallama zuwa ga wa’incan jama’a na mala’iku wanda suke zaune, sannan ka saurari abinda zasu gaisheka dashi, domin itace gaisuwarka da zuri’arka, Sai Annabi Adam(Alaihissalam) yace “Assalamu Alaikum” Sai suka ce masa “Assalamu Alaika Warahmatullah” sai suka masa karin “warahmatullah” Duk wanda zai shiga Aljannah zai shiga ne a surar Adam, Halitta bai bar raguwa ba(ma’ana tsawonsu) har zuwa yanzu.
Bukhari:6227
Muslim:2841


wani hadisin kuma da muslim ya rawaito Daga abi hurairah yace: Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : ” إِذَا قَاتَلَ أَحَدُكُمْ أَخَاهُ فَلْيَجْتَنِبْ الْوَجْهَ فَإِنَّ اللَّهَ خَلَقَ آدَمَ عَلَى صُورَتِهِ

Idan daya daga cikinku ya yaki dan’uwansa(Ma’ana suka sami tsabani har yakai ga duka kamar yadda wata riwaya ta nuna cewa idan dayanku ya daki dan’uwansa) ya nisanci fuska, domin Allah ya halicci Adam a surar sa.
Muslim:2612

Toh abinda ya kawo tsabanin fahimta shine fadin Manzon Allah “Allah ya halicci Adam a surarsa”. Shin Surar Allah Manzon Allah Yake nufi ko kuma surar shi annabi Adam?
hakikanin zahirin hadisin yana nuna cewa Allah ya halicci adam ne a irin surar Allah, domin haka shine yafi fitowa fili, toh indai haka ne me haka ke nufi? sannan ya za’ayi da fadin Allah Acikin Surat Shuraa ayah ta 11 “Wani abu bai zama kamar tamkarsa”.
ليس كمثله شيئ
Malamai na Ahlussunnah sunyi sharhi daban daban kan wannan hadithi wanda duk maganansu yana nuna cewa damiri na sura dake cikin hadisin yana komawa ne zuwa Ga Allah(Madaukakin Tsarki). amma zan kawo zancen ibn baz kan wannan zance, domin inaga yayi bayani mai gamsarwa akansa, wanda ba zata bar mutum da shubuha ba.
An tambayi sheikh ibn Baz Allah ya jikansa:
“Hadisi yazo daga Manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) yana hani kan aibata fuska, Da kuma cewa Allah ya halicci Adam  akan surarsa. meye yafi dacewa mutum ya kudurce kan wannan Hadisi?”
Sai Ibn Baz Ya Amsa(a takaice)

“Wannan Hadithi ya tabbata daga manzon Allah(Alihissalam) Yace: Idan dayanku zaiyi duka toh ya nesanci fuska, domin Allah ya halicci Adam abisa surar sa, a wani lafazi na dabam, Abisa surar Rahman. amma wannan hadithin baya nuna kamanceceniya ko kuma daidaito(Ma’ana wannan hadithi baya nuna cewa kamar yadda annabi Adam yake, haka shima Allah yake).

Ma’anar Hadithin awurin malamai shine: Allah ya halicci Adam yana mai Ji, Mai gani, mai magana idan yaso, wa’innan siffofin Allah ne, Allah yana Ji, yana gani, kuma yana magana idan yaso, kuma yana da Fuska.

Sannan wannan cewa da akayi Allah yana gani yana ji yana magana, shima Adam yana gani yana Ji yana magana, baya nuna kamanceceniya da kuma daidaito.
irin surar da take ta Allah ba ita bace irin surar da take ga halittu, ma’ana Allah na Ji, na gani na magana, shima Adam haka, amma ko wanne da irin nasa surar, irin Jin Allah ba kaman na Adam ba, Haka ganinsa haka maganarsa, Allah yana da sifofinsa da suka dace dashi, kuma babu wanda yasan yaya suke, sai dai kamar yadda ya tabbatar wa kansa sifofin haka Ahlussunnah suka tabbatar masa. haka shima bawa na da tashi siffofi wanda suka dace dashi.”
Majmu’ul Fatawa 226/4


karshen zance:

Wannan hadisai da suka gabata suna nuna cewa Allah na da sifofi tasa wanda suka dace dashi, wa’innan sifofi koda ankirasu da suna irin ta dan adam kaman ace yana gani hakan baya nuna cewa irin ganinsa daya yake da irin ganin dan Adam, A’a ganinsa dabam da na dan Adam. kamar yadda gani da idon mutum tasha bambam da ta dabbobi, amma kuma duka ana kiransu ido da kuma gani, shima haka wannan yake.
wassalatu wassalamu Ala Rasulillah.


Reference: IslamQA.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates