MAI HANKALI ZAI FARA DA GYARAN KANSA NE SANNAN SAI NA KUSA SAI KUMA NA KUSA HAR IYA KARFINSA(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

A ka’ida mutum mai hankali zai
fara gyaran kuransa ne, kafin ya
gyara kuren waninsa, watau zai
amfanar da kansa kafin ya amfanar
da waninsa.
Imam Muslim ya ruwai hadithi na
997 daga Jabir cewa:-
(( ﺃﻋﺘﻖ ﺭﺟﻞ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﻋﺬﺭﺓ ﻋﺒﺪﺍ ﻟﻪ ﻋﻦ ﺩﺑﺮ، ﻓﺒﻠﻎ
ﺫﻟﻚ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﻓﻘﺎﻝ: ﺍﻟﻚ
ﻣﺎﻝ ﻏﻴﺮﻩ؟ ﻓﻘﺎﻝ: ﻻ. ﻓﻘﺎﻝ: ﻣﻦ ﻳﺸﺘﺮﻳﻪ ﻣﻨﻲ؟
ﻓﺎﺷﺘﺮﺍﻩ ﻧﻌﻴﻢ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻌﺪﻭﻱ ﺑﺜﻤﺎﻧﻤﺎﺋﺔ ﺩﺭﻫﻢ،
ﻓﺠﺎﺀ ﺑﻬﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺪﻓﻌﻬﺎ
ﺍﻟﻴﻪ، ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ﺍﺑﺪﺍ ﺑﻨﻔﺴﻚ ﻓﺘﺼﺪﻕ ﻋﻠﻴﻬﺎ، ﻓﺎﻥ ﻓﻀﻞ
ﺷﻲﺀ ﻓﻼﻫﻠﻚ، ﻓﺎﻥ ﻓﻀﻞ ﻋﻦ ﺍﻫﻠﻚ ﺷﻲﺀ ﻓﻠﺬﻱ
ﻗﺮﺍﺑﺘﻚ، ﻓﺎﻥ ﻓﻀﻞ ﻋﻦ ﺫﻱ ﻗﺮﺍﺑﺘﻚ ﺷﻲﺀ، ﻓﻬﻜﺬﺍ
ﻭﻫﻜﺬﺍ )).
Ma’ana: ((Wani mutum daga
kabilar Uzrah ya yanta wani bawa
nasa yancin da zai fara aiki bayan
mutuwarsa, sai labarin hakan ya
kai ga Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah, sai ya ce: kana da
wani dukiyan ne banda shi
(wannan bawan)? Sai ya ce: a’a.
To sai (Annabi) ya ce: wa zai sayi
wannan bawan daga gare ni? Sai
Nu’aimu Dan Abdullahi Ba’adawe
ya saye shi da Dirhami dari
takwas. Sai Manzon Allah ya zo da
su ya mika su gare shi, sannan ya
ce: Ka fara da kanka tukun ka yi
wa kanka sadaka, idan wani abu
ya rage, sannan ka ba wa iyalanka,
in ka ba wa iyalanka sannan wani
abu ya rage, to sai ka ba wa
yan’uwanka makusanta, in ka ba
wa yan’uwanka makusanta sannan
wani abu ya rage, to sai ka ba wa
wannan ka ba wa wancan)).
Intaha.
Sannan Ibnu Abi Shaibah ya
ruwaito cikin Musannaf 7/33 cewa
Nakha’ii ya kasance yana cewa in
za ka yi addu’a to sai ka fara da
kanka tukun)).
Har yanzu ya ruwaito a wannan
shafin cewa: Said Dan Yasaar ya
ce: Na zauna gurin Abdullahi Dan
Umar, na ambaci wani mutum,
sannan na ce: Allah ya yi masa
rahama, sai ya bugi kirjina ya ce:
Ka fara da kanka tukuna)).
Sannan Imam Attayaalisii ya
ruwaito cikin Musnad dinsa 4/35
cewa Abdullahi Dan Amru ya ce:-
(( ﻓﻘﻠﺖ: ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﺎ ﺗﻘﻮﻝ ﻓﻲ ﺍﻟﻬﺠﺮﺓ
ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ؟ ﻓﻘﺎﻝ: ﻳﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ! ﺍﺑﺪﺍ ﺑﻨﻔﺴﻚ ﻓﺎﻏﺰﻫﺎ،
ﻭﺍﺑﺪﺍ ﺑﻨﻔﺴﻚ ﻓﺠﺎﻫﺪﻫﺎ)).
Ma’ana: ((Sai na ce: Ya Manzon
Allah! Me kake cewa game da
Hijira da Jihadi? Sai ya ce: Ya
Abdllah! Ka fara da kanka tukun ka
yaki kanka, ka fara da kanka tukun
ka yi jihadin kanka)). Intaha.
KARIN HASKE
Wadannan nassosi suna gwada
mana cewa: Lalle mutum mai
hankali zai fara gyaran kuransa ne
kafin ya gyara kuren waninsa, idan
a gidanku ana yin kure ba ka yin
shiru ka ki yin magana, amma
kuma in a gidan wasu ake yi ka yi
magana! A’a za ka gyara kuren
gidanku sannan kuma ka gyara
kuren gidajen wasu gwargwadon
hali.
Idan kana cikin wani Club ne, ko
wata Kungiya ce, ko wasu jama’a
ne sannan ka ga wani kure da ake
yi a cikinsu, ba ka cewa tunda
jama’arka ce ba za ka yaki kuren
da ke cikinsu ba, a’a za ka yi musu
wa’azi ka yaki wannan kure nasu
gwargwadon hali, wannan shi ne
Musulunci, kuma wannan shi ne
Sunnah, saboda haka ne Annabi
mai tsira da amincin Allah ya yi.
Ibnul Athiir ya ce cikin littafinsa
Usdul Gabah1/10, da Maawardii
cikin littafinsa A’alaamun
Nubuwwah 1/275, cewa Ibnu Ishaq
ya ce:-
(( ﺑﻌﺜﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻟﻪ ﺃﺭﺑﻌﻮﻥ ﺳﻨﺔ ﻓﺄﻗﺎﻡ ﺑﻤﻜﺔ ﺛﻼﺛﺔ ﻋﺸﺮ
ﺳﻨﺔ ﻭﺑﺎﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻋﺸﺮﺍ. ﻭﺍﻧﻪ ﻛﺘﻢ ﺃﻣﺮﻩ ﺛﻼﺙ ﺳﻨﻴﻦ
ﻓﻜﺎﻥ ﻳﺪﻋﻮ ﻣﺴﺘﺨﻔﻴﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻥ ﺍﻧﺰﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ :
ﻭﺃﻧﺬﺭ ﻋﺸﻴﺮﺗﻚ ﺍﻟﻘﺮﺑﻴﻦ…)).
Ma’ana: ((Allah ya aiko shi yana da
shekaru arba’in, kuma ya zauna a
Makka shekaru goma sha uku,
sannan a Madina shekaru goma.
Ya boye lamarinsa na shekaru uku,
watau ya kasance yana yin
da’awah a boye, har dai lokacin da
Allah Madaukakin Sarki Ya
saukar da: “Ka gargadi danginka
mafiya kusa..)). Intaha.
Sannan Ibnu Kathiir ya ce cikin
littafinsa na Sirah 1/457 Aliyyu Dan
Abi Talib ya ce:-
(( ﻟﻤﺎ ﻧﺰﻟﺖ ﻫﺬﻩ ﺍﻵﻳﺔ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ” :ﻭﺃﻧﺬﺭ ﻋﺸﻴﺮﺗﻚ ﺍﻷﻗﺮﺑﻴﻦ ﻭﺍﺧﻔﺾ
ﺟﻨﺎﺣﻚ ﻟﻤﻦ ﺍﺗﺒﻌﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ” ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﻋﺮﻓﺖ ﺃﻧﻲ ﺍﻥ ﺑﺎﺩﺍﺕ ﺑﻬﺎ
ﻗﻮﻣﻲ ﺭﺃﻳﺖ ﻣﻨﻬﻢ ﻣﺎ ﺃﻛﺮﻫﻪ، ﻓﺼﻤﺖ. ﻓﺠﺎﺀﻧﻲ
ﺟﺒﺮﻳﻞ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻓﻘﺎﻝ: ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ! ﺍﻥ ﻟﻢ ﺗﻔﻌﻞ ﻣﺎ
ﺃﻣﺮﻙ ﺑﻪ ﺭﺑﻚ ﻋﺬﺑﻚ ﺑﺎﻟﻨﺎﺭ)).
Ma’ana: ((Lokacin da ayan nan ta
sauka ga Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah: “Ka yi wa
danginka na kusa kusa gargadi,
sannan ka sauko da fiffikenka ga
wadanda suka bi ka cikin Muminai”
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah ya ce: Na san cewa lalle ni in
har na bayyana wa mutanena
(sakon da ke gare ni) zan ga abin
da ba na son sa daga gare su,
saboda haka sai na yi shiru. Sai
Jibrilu amincin Allah ya tabbata
gare shi ya zo mini ya ce: Ya
Muhammad! Idan har ba ka yi abin
da Ubangijinka ya umurce ka da
shi ba, to kuwa lalle zai azabtar da
kai da Wuta)). Intaha.
Daga nan Annabi mai tsira da
amincin Allah ya hau dutsen Safaa
ya kira dangoginsa na kud-da-kud
ya bayyana musu manzancinsa, ya
bayyana musu cewa ba zai iya yi
wa kowa komi ba a gaban Allah
matukar dai bai tsarkake ibada ga
Allah Madaukakin Sarki ba. A nan
ne da yawa daga cikinsu suka
zazzage shi!!
A zamanin Annabi na Dawud a
wani gari a gabar Matsakaicin farin
Teku (Mediterranean Sea)
Isra’ilawan garin sun kasu kashi
uku: Kashi daya suka saba dokar
Allah da ke cikin Attaura wacce ta
haramta wa Isra’ilawa yin aiki ranar
asabar, suka yi ya yin su a ranar
asabar.
Kashi na biyu sai suka yi ta yiwa
masu wannan su wa’azi suna ce
masu abin da suke yi ba daidai ba
ne.
Kashi na uku kuwa ba su hana
masu yin su wannan danyen aiki
nasu ba, amma sun ce wa masu
yin wa’azin: tunda dai wadannan
sun ki karban wa’azi sun ki daina
wannan mugun aiki nasu, don me
kuke bata lokaci a kan yi wa
wadanda Allah zai azabtar wa’azi?
To amma da Allah ya tashi yin
hukunci sai ya kubutar da masu yin
wa’azi, sannan ya azabtar da masu
sabon, su kuwa wadanda suka
kasa wa’azi, kuma suka yi kokarin
gamsar da masu yin wa’azin da su
daina, saboda wadanda ake musu
wa’azin sun ki bi Allah bai ba mu
labarin abin da ya yi da su ba.

Leave a Reply

Latest updates
Categories