MAICECE MU'UJIZA ? (DARASI NA FARKO){Mal.Aminu Ibrahim Daurawa}

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Abubuwan mamaki da zai iya
faruwa ta hannun dan Adam, gaba
daya kashi goma ne.
Na daya Mu’ujiza ko aya daga
Annabawa.kamar sandar Annabi
musa, ko raya matacce da warkar
da makaho da kuturu ga Annabi
isa, ko bubbugowar ruwa ta
hannun Annabi Muhammad saw.
Na biyu, Irhasat, abin mamaki
dake faruwa ta hannun Annabi
kafin aikoshi da manzanci, kamar
duwatsu da suke yiwa Annabi saw
sallama idan ya wuce ta gabansu
kafin aiko shi.
Na uku, karama, wanda take
faruwa, ta hannun waliyan Allah
kamar sayyadina Umar (ra ) ya
kirawo wani tabii mai suna sariya,
daga tsawon fiye da kilometer
1000, ya kuma jishi ba tare da
amfani da wayar sadarwa ba.
Na hudu Alma’una, shine wata
gudunmawa ta gaggagawa da
Allah yake yiwa wani bawansa
daya shiga wani matsatsi ko
damuwa, kamar yadda yazo a
cikin sharhin akidatul- dahawiyya
na shaik Usaimin, cewa wani
bawan Allah,tsoho ya dorawa
jakinsa kaya, sai jakin ya mutu
kafin zuwa gida sai ya roki Allah
ya rayashi domin ya isar masa da
kayansa zuwa gida, jakin ya tashi,
sai bayan sun isa gida sannan ya
mutu.
Na biyar tsafi wanda yake faruwa
ta hannun matsafa, kamar
matsafan lokacin Annabi musa, da
sukayi fito- na- fito dashi Allah ya
bashi nasara akan su.
Na shida, siddabaru ko rufa-ido,
wanda zakaga masu wasa da
miciji sukeyi, kamar kaga mutum
ya shiga cikin jaki ta jela ya fito ta
baki, ko ya zura allura ta kofar
hanci daya ,ya fito da ita ta kofa
daya.
Na bakwai, Ihana, (wato wulakanci
da kunyatarwa)wanda yake
faruwa ta hannun wanda yayi
daawar Annabta ta karya, kamar
Musailamul kazzab, lokacin da
yaji cewa wani mai ciwon ido yazo
wajen Manzon Allah saw yayi
masa Addu’a ya warke, shima sai
yace akawo masa mai ciwan ido
zaiyi masa Addu’a, da aka kawo
mai ciwon idon,yanayi masa tofi
sai idon ya rufe, ya dena gani
gaba daya.
Na takwas, istidraji, shine abin
mamaki da yake faruwa ta hannun
wanda yayi daawar uluhiyya, wato
matsayin Allantaka, kamar Dujal
wanda zaizo da abubuwan
mamaki, yace ayi ruwa ayi, yace
kasa ta tsage, yaje makabarta
yace matattu su tashi, kuma aga
sun tashi, irin wannan shi ake kira
shigo- shigo ba zurfi, ko talala, ko
jarrabawa, daga Allah domin yaga
zaa bishi, ko zaabi dujal mai ido
daya, wanda da shine Allah da
gaske yaya ya zama mai ido
daya?
Na tara, abubuwan mamaki ta
hanyar koyo, da kwarewa ko wata
baiwa, mutum yana iya zuwa da
abin mamaki wanda sauran
mutane za suyi mamaki, kamar
yadda muke gani, cikin shirye-
shirye na wasanni ko wata bajinta
ta hawa igiya ko nutso a ruwa, ko
kokawa ko daga wani abu mai
nauyi, da sauransu.
Na goma kayan kere- keren
zamani na kimiya da fasaha,
wadanda suke ta fitowa, a baya
babu su, na kayan sadarwa, da
abubuwan hawa,da sauransu, duk
abinda zaka gani daga dan Adam
na mamaki baya fita daga
wadannan abubuwa goma,
Wanda za muyi magana akai itace
mu’ujiza wanda kalmace ta larabci
tana nufin gajiyarwa, wato abinda
ya zama gagara koyo, ko gagara
misaltau, abinda yafi karfin wani
dan Adam wanda ba Annabi ba,
yazo dashi, don haka mu’ujiza
tana nufin wani abin mamaki da
daure kai, wanda Allah yake
gudanar dashi ta hannun Annabi
wanda zai tabbatar da cewa,
sakon da suke dauke dashi daga
wajen Allah yake, kuma ga dalili
akan haka wanda bai yarda ba
shima, yayi irin abinda sukayi ko
yazo da sheda akan haka.
Mu’ujiza ta kasu kashi uku, ko
tana shiga layi uku, duk wata
mu’ujiza ta Annabi, tana zama ko
nuna ilmi, ko wadata, ko iko da isa
wanda yafi karfin tunanin dan
Adam.
Dukkan mu’ujizozin da zamu kawo
na Annabi akan wannan layin
suke, ko, ilmi ko wadata, ko
kudura wato iko da isa.

2 responses to “MAICECE MU'UJIZA ? (DARASI NA FARKO){Mal.Aminu Ibrahim Daurawa}”
  1. Aminu lawal bature dtm Avatar
    Aminu lawal bature dtm

    Allah akbar Allah ya kara daga darajar malam

  2. Umar Aliyu Clever Avatar

    Ameen, Allah ya saka malan

Leave a Reply to Umar Aliyu CleverCancel reply

Latest updates
Categories