Amsa:
Idan wani ya zage ka kana da abubuwa guda uku da zaka iya yi wanda shar’ah ta baka dama.
- Kayi haƙuri, ka yafe.
- Ka rama daidai zagin da aka maka ba tare da ƙari ba.
- Kaje wurin Al-ƙali domin neman haƙƙinka.
Allah maɗaukakin sarki ta yace acikin Surat- Shura aya ta 40
وجزاء سيئة سيئة مثلها فمن عفا وأصلح فأجره على
الله
Sakamakon cutarwa da akayi wa wani shine ya rama daidai yadda akayi masa, Amma wanda ya yafe kuma ya kyautata toh ladarsa na wurin Allah.
Allah kuma ya sake faɗi Acikin Suratul Baqara aya ta 194
فمن اعتدى عليكم فاعتدوا عليه بمثل ما اعتدى عليكم
Wanda yayi muku Ta’addanci to ku maida masa kwatankwacin wannan Ta’addanci da yayi muku.
Amma abinda yafi dace wa ga Musulmi shine yayi haƙuri, sai dai in ya zamto wannan mai ta’addancin da zagin bazai daina ba sai an mayar masa da martani. Toh anan Sai ya mayar masa da martani daidai. banda wuce gona da iri.
Allah yasa mudace.
Leave a Reply