Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad
Al-Kadhibi – Wani malami dan kasar
Bahrain da Allah ya ganar da shi
gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi’a.
TSAFI A ADDININ SHI’AH:
Akwai wani shahararren malami a
yankinmu na Qudhaibiyya wanda ya yi
fice wajen magance matsalolin
marasa lafiya da warware matsalolin
mutane ta hanyar karanta Alqur’ani da
addu’oi. Mutane suna ganin sa a
matsayin malamin kirki mai yawan
karamomi. A lokacin da na koma
tafarkin Sunna sai aka kai ma sa qara
ta ana neman ya yi wani abu a kan
haka. Da farko sai ya neme ni cikin
lalama da rarrashi yana nuna min
taren sa da mahaifina sannan ya
kwance ma ni jakar ilimin da yake
taqama da shi in da ya bude Alqur’ani
kai tsaye ya dan ja wasu ‘yan addu’oi
sannan ya ba ni ya ce in karanta. Sai
ga ayar da a cewar sa wai tana
umurni na da in yi gaggawa in koma
Shi’a. Ya ce, to ka gani Allah yana
son ka da rahama da komawa kan
tafarkin gaskiya. Don haka, wannan
aya a yau za ta rinqa bin ka duk in da
ka shiga. Abin mamakin da ya biyo
baya shi ne, a ran nan duk in da na
shiga sai na ji ana karanta wannan
aya. Tun ba mu rabu da shi ba aka
buda Radio sai ga ta ana karantawa.
Da na je gida kuma ina buda Talabijin
haka. Da abin ya ba ni mamaki sai na
dauko Alqur’ani na buda, kwatsam sai
idona suka fada a kan ta. A gaskiya
wannan siddabaru na sa ya so ya
rikita ni matuqa har sai da na kasa
bacci a wannan dare ina tunani. Daga
bisani sai na ji ana yadawa cewa,
wannan boka ya ba da busharar zan
koma addinin Shi’a sai na ce a raina
“Kifi na ganin ka mai jar koma”! Da
Allah ya tashi tona asirinsa sai ya
bayyana ma ni jahilcinsa baro-baro in
da na yi ma sa tambayoyi da suka
rikitar da shi a gaban jama’a kuma ya
kasa amsawa. Daga qarshe sai da ya
nemi mararraba da ni bayan kuwa a
da ya matsa ma ni lamba ba dare ba
rana. Allah ya yi gaskiya da ya ce:
“Masihirci ba zai yi rabo ba a duk in
da ya je.”
Suratu Daha: 69. Da kuma in da
buwayayyen sarkin ya ce: “Lalle
makircin Shaidan ya kasance mai
rauni.” Suratun Nisa’:76.
Irin wadannan mutane sai su ba ka
mamaki. Me ya makantar da su daga
ayoyin Allah da hadisan manzon Allah
qarara da suka hana sihiri, suka
kafirta mai yin sa? Don me sai sun yi
amfani da sihiri har wajen kira zuwa
ga abin da suka dauka shi ne
musulunci? Babu wata hujja da za a
gamsar da wanda ya yi ridda daga
addinin Shi’a sai ayi amfani da sihiri
don jawo hankalinsa?! Ga fa riwayoyi
nan birjik a littafanmu ma su nuna
haramci da hatsarin wannan abu.
Annabi Sallallahu Alaihi Wa’alihi
Wasallam ya ce, “Ku nisanci ababe
bakwai masu halakarwa. Na farkon su
Shirka, na biyu Sihiri”.
Haka kuma an karbo daga Ja’afar As-
Sadiq Alaihis Salam daga kakansa Ali
Alaihis Salam cewa, duk wanda ya
koyi sihiri kadan ko mai yawa to, ya
kafirta.
Har wayau daga sayyidi Ali Alaihis
Salam yana cewa, “Duk wanda ya je
wajen mai duba ya tambaye shi kuma
ya gaskata shi to, ya kafirta da abin
da aka saukar zuwa ga annabi
Muhammad Sallallahu Alaihi Wa’alihi
Wasallam.”
TA’ASSUBANCIN ‘YAN SHI’A:
Ta’assubanci da ra’ayin riqau wasu
halaye ne da ke sa mutum ya yi abin
da bai dace ba. Ba zan taba mantawa
da wasu ababe biyu masu nuna
wannan ba. Na farkon ya faru ne a
kaina. Dayan kuma a kan wani dan
qaramin yaro da bai ko isa yin
magana ba tukuna.
Bayan da labari ya yadu cewa, na
koma Ahlussunna wata rana na hadu
da wata tsohuwa daga cikin
jama’armu da ake kiran ta Mamar
Ibrahim. Na yi ma ta gaisuwar
girmamawa kamar yadda aka saba har
ma na karvbi kayan da take auke da
su don in taimaka ma ta. Bayan mun
yi gaisuwar arziki sai ta tambaye ni,
daga ina na fito? Na nuna ma ta
masallaci cewa, daga wurin salla na
fito. Kawai sai na ga ta fusata, ta tofa
yawu a fuskata tana la’anta ta tana yi
ma ni baqar addu’a, wai daman ta ji
labarin na karkace na koma Sunna
amma da farko ba ta yarda cewa
gaskiya ne ba!
Labari na biyu kuwa wani dan qaramin
yaro ne mai suna Umar da kakarsa ta
je da shi wajen makoki, ya je yana
wasa sai ya yi tuntube ya fadi. A garin
rarrashinsa da ba shi haquri wata
mata ta zo tana shafa kansa tana ce
ma sa “sannu. Ya sunanka?” shi
kuma yana fadin “Umal” don bai iya
fadin sunan ba. Da ta yawaita
tambayar sa kuma ba ta gane amsar
da yake fadi ba sai kakarsa ta ce “ya
gaya ma ki sunansa Umar”! Ai kuwa
jin haka kawai sai matar nan ta
wuntsilar da shi tana la’antar sa tana
cewa, tafi can! Allah ya la’ane ka, ya
la’ani Umar da wanda ya sa maka
suna Umar da duk wanda ma ya kira
dansa da suna Umar. Kakar yaron sai
ta zura ido tana ta kallon ikon Allah!.
Cigaba a darasi na shida
Leave a Reply