Wallafar:
SHeikh Faisal Bn Ali Al- Ba’adani
Fassarar:
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da
Mal. Aliyu Rufa’i Gusau.
Muhimman hanyoyin da Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ke taron
Watan Azumi da su, sun hada da:
1.2 Yawaita Azumi a Cikin Watan
Sha’abana:
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama
kan yawaita Azumin nafila a cikin
wannan wata saboda fuskantar Watan
Azumi. Nana Aisha Raliyallahu Anha
na cewa; Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama na yawaita Azumin,
har mu yi zaton ba zai daina ba har
abada. Wani lokacin kuma ya yi ta cin
abincinsa, har sai mun zaci ba zai
sake Azumin nafila ba har abada.
Kuma ban taba ganin Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya share
wata daya cur yana Azumi kullum ba,
in ba watan Ramalana ba. Ban kuma
ga watan da yake yawaita Azumin
nafila a cikinsa ba, bayan Ramalanan,
kamar watan Sha’abana.” A wata
riwaya kuma aka ce, cewa ta yi:”… Ban
taba ganin Annabi na Azumi da yawa
a cikin wata daya ba, kamar yadda
yake yi a cikin watan Sha’abana. Ina
ganin ma yana azumtar sa ne baki
daya. Kai ko bai yi haka ba, ‘yan
kwanukan da yake sha a cikinsa kadan
ne.”
Saboda haka, a kan wannan Hadisi,
abu ne mai kyau ga kowane musulmi,
ya yawaita Azumi a cikin watan
Sha’abana. Malamai sun ce: “Azumi a
cikin watan Sha’abana kamar Sallolin
nafila ne da aka sunnanta yi kafin na
farilla. Share fage ne wato shi, wa
Ramalana. Saboda haka aka sunnanta
shi aka kuma sunnanta yin Azumin
kwana shida a cikin watan Shawwal,
kamar dai yadda ake yin nafilfili kafin
da kuma bayan Sallar farilla.”
Amma duk da haka, mafi yawan
mutane a yau sun yi ko-oho da
wannan koyarwa ta Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallama sai wanda Allah ya
taimaka. Alhali kuwa dubaiban mutane
na iqirarin bajinta da kasancewa
amale a cikin ruqumma. Wasu kuma
suna tinqaho da kasancewa masu
neman manya-manyan Sunnoni su
qanqame, a matsayinsu na masu koyi
da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.
To, mu sani dabbaqa wannan Sunnah
ta yawaita Azumi a cikin watan
Sha’abana ne kawai zai sa mu ribanci
alherin da ke cikin wannan wata mai
albarka. Allah ya yi mana mawafaqa,
amin.
1.3 Yin Bushara ga Sahabbansa:
A duk lokacin da watan Azumi ke
goshin kamawa, Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallama kan tara Sahabbansa
ya yi masu bushara da irin alhairan da
watan ke dauke da su. Yakan yi haka
ne da nufin yi wa Sahabban nasa
qaimi, don zaburar da su, su zare
dantse, kowa ya kwashi rabonsa.
Akwai Hadissai da dama da ke bayani
a kan haka, ga kadan daga cikinsu:
→ Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama
yakan ce masu: “Idan Watan Azumi ya
kama, ana bude qofofin sama’u, a
kuma rufe qofofin Jahannama kaf,
sannan kuma a daure Shaidanu.”
→Yakan kuma ce: “Da zarar daren
farko na Watan Azumi ya kama, sai a
daure shaidanu a kuma ququnce
aljannu, a rufe qofofin Wuta ba za a
bude ko daya daga cikinsu ba, a kuma
bude na Aljanna, ba za a rufe ko daya
daga cikinsu ba. Sai kuma wani mai
shela ya yi kira ya ce: “Duk mai nufin
alheri ya matso ga dama ta samu, duk
kuma mai nufin sharri ya kama kansa.
Kuma Allah ya yi alkawalin ‘yanta
wasu bayi daga shiga Wuta, kowane
dare.”
→ Yakan kuma gaya masu
cewa:“Watan nan na Azumi mai abarka
ya kama. Allah ya wajabta azuminsa a
kanku. A cikinsa ne ake bude qofofin
sama’u, a rufe na Jahimu, a kuma
daure shaidanu. Haka kuma Allah na
da wani dare a cikinsa wanda
alfarmarsa ta fi ta wata dubu. Duk
wanda bai sami alherin da ke cikinsa
ba, ya tabe har abada.” Yakan kuma
gaya masu cewa: “Haqiqa a cikin
Aljanna akwai wata qofa ana kiran ta
Rayyanu, ta nan ne masu Azumi za su
bi a ranar qiyama. Babu kuma wanda
zai shige ta bayan su. Za a kira su ne
daban ba tare da kowa ba, a bude
masu ita, a kuma mayar a rufe har
abada.”
Da wannan kuma muke kira da babbar
murya, ga masu wa’azi da
shugabannin musulmi, da cewa ya
kamata su kula da wadannan Hadissai
na bushara, su watsa su cikin duniyar
Musulunci, don mutane su san girman
Watan Azumi da irin falalar da yake
tare da ita. Su kuma koya masu yadda
za su ci moriyar wannan gajiya tasa.
Domin kuwa ta haka ne kawai farin
cikin kamawar watan za ta zama
hantsi leqa gidan kowa. Wanda za ta
sa kowa ya shagaltu da neman
masaniya da makamar ibadar. Ba
kawai a taqaita ga shirya gara da
daula ba, ta yadda har manufar
Azumin za ta kasa tabbata ga mafi
yawan mutane. Allah ya sa mu dace,
amin.
1.4 Bayanin Wasu Hukunce-
Hukuncen Azumi:
Cewa Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama na yi wa Sahabbansa
bayanin wasu hukunce-hukuncen
Azumi, abu ne da ba ya buqatar kafa
hujja domin tabbatarsa. Domin kuwa
abubuwan da wannan littafi ya qunsa
gaba daya na tabbatar da haka ne.
Iyakar abin da za mu ce a wannan
sashe shi ne, buqatar kawai da ake da
ita ga Malamai da masu da’awa a
wannan zamani namu, shi ne su
mayar da hankali ga karantar da
mutane hukunce-hukuncen na Azumi
tun kafin watan nasa ya kama. Su
kuma ci gaba da yin haka a tsawon
kwanakinsa. Kowa daga cikinsu ya yi
iyakar yinsa, ta hanyar qirqiro salailai
da dabaru daban-daban da za su
taimaka masu ga tabbatar da wannan
guri. Kai! Yin haka ma kusan wajibi ne
domin kuwa jahilci a yau ya yi wa
musulmi riga da wando. Kuma masu
fadakarwa da wayar wa jama’a da kai
a kan al’amurran addini sun qaranta,
musamman a cikin ya’ayyuhannasu.
Kai! Ko a cikin ya’auyyuhallazina
amanu, abin sai hattara.
Su kuwa sauran jama’a musulmi,
wadanda ba Malamai ba; mazansu da
mata, ba abin da ya kamace su illa su
mayar da hankali ga neman sanin
makamar hukunce-hukuncen Shari’a
wadanda suka shafi ibadodi na yau da
kullum, da irin shirin da ya kamata su
yi don fuskantar wannan wata na
Azumi mai alfarma. Su lizimci karanta
littafai, da sauraren kasakasai, da
halartar wuraren wa’azi da tafsirin
Alqur’ani. Domin kuwa babu yadda za
a yi aikin mutum ya yi kyau face ya
qetaro irin wadannan matakai. Yin
haka ko shakka babu wajibi ne a
kansu, matuqar suna son tsira da wani
abu gobe qiyama. Domin kuwa duk
wanda ya aikata wani aiki ba yadda
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ce a yi shi ba, to, ya yi
aikin banza. A duk lokacin da kuma
mutum ya dage kai da fata a kan biyar
tafarkin Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama da koyi da shi, a cikin
komai nasa, da ya hada da magana da
aiki da gargadi, to shi ne mutum na
gari wanda kuma ya yi gam da katar.
A dakace mu a darasi na gaba in Allah
ya so.
Leave a Reply