RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI1(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Wallafar:
SHeikh Faisal Bn Ali Al- Ba’adani
Fassarar:
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da
Mal. Aliyu Rufa’i Gusau.
GABATARWAR MASU FASSARA
Godiya ta tabbata ga Allah Mahalicci
wanda ayyukan alheri ba su kammala
sai da yardarsa. Tsira da aminci su
tabbata ga manzo mai girma.
Wannan littafi ya bada cikakkiyar sura
ta rayuwar Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam tun kafin kamawar
watan azumi har karewarsa, da irin
yadda watan azumi yake zame masa
babbar makaranta ta koyar da
al’ummarsa yadda ya kamata a bauta
ma Allah ba kuma tare da an yanke
hulda da mutane ba.
Babbar hikimar da ke cikin wannan
littafi ita ce, tattara sahihan bayanai
wadanda suka shafi yanayin ibada da
zamantakewa ta Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam a wannan
muhimmin lokaci, irin bayanan da zai
yi wuya ka same su a hade wuri guda
da kuma irin wannan tsari da mai
littafin ya shinfida.
Kasancewar cewa kowane musulmi
dole ne ya ratsa wannan makaranta ta
horaswa sau daya a kowace shekara
ya sanya bukatuwar musulmi zuwa ga
wannan littafi ta dada karfi. Domin
kuwa duk ibadar da mutum zai yi to,
ba zata zama karbabbiya a wurin Allah
ba sai ta hada sharuda biyu, su ne:
kasancewarta da kyakkyawar niyya da
kuma yin ta bisa ga Sunnah; koyarwar
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam.
Game da fassara dai tana nan yadda
aka saba. Amma a tsarin littafin mun
dan shigar da wani sabon salo na
gabatar da kowane zango da
takaitaccen abinda zai kunsa don
Karin zaburar da mai karatu da kara
masa karsashi da nishadin karatu.
Allah ya saka da alheri ga duk wanda
ya bada wata gudunmawa ta kowace
fuska ce don fitowar wannan aiki.
A Green Palace Hotel
Madina, K.S.A.
19 ga Ramadhan 1430H.”
In shaa Allah za mu ci gaba da kawo
muku jerin darussa a cikin wannan
littafi mai albarka a duk lokacin da
dama ta samu daga yau har zuwa
karshen watan Ramadana mai albarka.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates