Akwai zantukan Maluma game da hukuncin zuwa biso game da mata, Amma zantuka da sukafi ƙarfi sune zantuka biyu.
Zance na farko: Makaruhi ne mace tabi gawa zuwa biso. Dalilinsu shine hadisin Ummu Aɗiyya tace:
An hanamu bin Janaza, amma ba’a ƙarfafa hanin ba.
Bukhari: 1278
cewa da tayi a hadisin ba’a ƙarfafa hanin ba shine Maluma masu ganin makaruhi ne suka ɗauke shi a matsayin Makaruhi ne ba Haramun ba
Zance na biyu: Haramun ne mata subi Janaza. Suma sun kafa hujja ne da wannan hadisi da muka ambata a sama, su sun ɗauki wannan hani ɗin a matsayin sa na haramci. Sannan kuma sunyi duba ga yanayin ɗabi’ar mata na Rauni, kada a bari su rinƙa zuwa maƙabarta hakan yasa suje suna kuka a wurin ko kuma abu makamancin haka.
Leave a Reply