Yau Malam yayi maganane kan Fitintinu dasuka shafi dakin Allah. Kafin turo annabi(Sallallahu alaihi wasallam) da kuma bayan turoshi.
Wanda wa’innan fitintinu suna da yawa amma wanda malam yayi magana akansu sune kaman haka.
1.Fitinan ‘kharamidah’
wanda wannan wasu ‘yan ta’addan ‘yan shi’ah ne masu tsattsauran ra’ayi. Yakai ga sun kawo wa makkah hari suka Kai farmaki wa dakin Allah sannan suka ciro ‘hajr alaswad’ daga wurin da yake suka tafi dashi sukaje suka gina sabuwar ka’aba ta dabam. Wanda daga karshe aka kwatota aka dawo da’ita
2.Fitinan Hajjaj ibn yusuf assaQafi.
Alokacin Daulan umawiyyah. Wanda hajjaj da rundunarsa suka kai hari da har ta shafi ka’abah. Akayi kisa da kuma kone kone.
3.Fitinan Sufaye.
Bayan da Duniyar musulunci ta fada cikin rudani da shirka wanda Jahilan sufaye suka kirkirota. Suka maida makkah wurin bautan waliyyai wanda alokacin ansami hubbare wurin 360 na waliyyai wanda ake zuwa rokonsu. Kullum acikin mauludi ake na wa’innan waliyyan. Da sauran abubuwa wanda addini ya hana.. Ana cikin haka Allah ya kawo sheikh ibn Abdulwahab yazo ya jaddada tauhidi ya kuma Kori wannan dabi’a mummuna.
4. Fitinan Bayyanar mahadin karya.
Wanda ya faru a 1979 Miladiyyah. Inda aka samu wasu matasa mazu zafin kai suka kai wa wannan wuri mai tsarki hari. Hakan yakai ga zubda jini sosai da rushe rushe. Malam ya bayyana cewa yana nan alokacin da abin ya faru kuma alokacin da da’awar ta taso malamai sunyi zama da wa’innan matasa babu iyaka. Sannan yana daga cikin wa’inda aka saka musu nauyin yiwa wa’innan matsa raddi a rubuce ta wasika kaman yanda su matasan suka rubuto wasika suna neman ayi wa mahadinsu mubaya’a. Rikicin ya somane da asubahi Bayan idar da sallah kuma Rikicin ya dade tsawon kwana 13 anayinta. Haka Masallaci mai alfarma ya zauna ba’a sallah aciki har sai da Allah ya kawo nasara a rana ta 14 aka kammala kuma aka fara aikin ibadah a wannan wuri.
Allah muke roko ya kara karemu ya kare mana addininmu.
Wassalatu wassalam ala rasulillah.
Leave a Reply