Mai Rubutu: Abdurrahman Muhd Sani Umar
Wannan ita ce wayewa da ‘ƴancin da ƴan boko akida ƴan dadi Arna wadanda Turawa suka yi musu barbarar tinani suke kiran Al’ummar mu gareshi
Dr Iyad Qeneby ya rubuta:
A kwana biyu da suka gabata ne wata kotu a jihar Texas a kasar America ta yanke hukunci game da yaro James Jeffrey dan shekara 7.
Mahaifiyar Jemis dai ta saki Mahaifinsa! Ta kuma kasance tana sanya mai tufafin Mata tana kiranshi da Luna (sunan Mata) sai tayi korafi a gaban kotu cewa James din da kanshi yana faman kin jininsa a matsayinsa na Namiji don haka tana son ta mayar dashi zuwa Mace ta hanyar dasamai kwayoyin halitta na Mata.
Anasa bangaren Mahaifin James (Jeffrey younger) ya nuna rashin amincewarsa sosai game da hakan yace mahaifiyar yaron ce take tsorata yaron tana gayama shi cewa (iya Maza ne kawai Dodanni suke cinyewa) ma’ana banda Mata!
Bayan tsawon lokaci da kafafun yada labaran kasar America suka dauka suna tattauna wannan batu, kotu ta yanke hukunci a jiya cewa ta baiwa Uwar hakkin canza James zuwa Mace!
Uwar kuma ta bukaci da a hana Mahaifin James wata alaka da shi in takama dole sai yayi to kar ya kuskura ya kirashi da James sai dai Luna, hakanan tana nema ga kotu da ta hana James alaka da duk wanda zai kira shi da sunan shi na gaske a maimakon luna.
Abinda kafafun yada labaran America suke tattaunawa yanzu kuma shine bukatar da wasu kungiyoyi da gidauniyoyi da suka nemi lallai sai an amsa cewa wajibine abawa yaran da ba su kai shekara 16 cikakken ‘yancin canza jinisin halittarsu (Transgender) koda iyayensu duka biyun ko dayansu basu yarda ba, kuma babu amfanin zaman bita da akeyi na bada sharwarwari da akeyi ga masu neman canza halittarsu (Transgender) kafin ayi musu aikin sabo da wannan bitar bata da amfani.
Sako ga wadanda suka fitinu da batun cikakken ‘yanci
Haka ‘yancin da suke riyawa yake suke yadawa a cikin manya da yara yale! Bada bayanan karya. toshe fiɗira sannan bawa wadannan masu batarwar cikakken ‘yanci.
Sako ga wadanda suke yada tinani da al’adun Turawan yamma a kasashen musulumai suke bata kwakwalen ‘ya’yanmu don kawai muma mu zama wasu halittun na da gwara dabbobi da su.
Yakin ba ga iya Musulunci yatsaya ba, yakine ga dan adantakar dan adam da fidirsa da dabi’arsa, don haka kuyi riko da addinin ku kuyi alfahiri da shi kafin ku zama wasu halittun daban
وَاللَّهُ يُرِيدُ أَن يَتُوبَ عَلَيْكُمْ وَيُرِيدُ الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ الشَّهَوَاتِ أَن تَمِيلُوا مَيْلًا عَظِيمًا
Leave a Reply