Mai rubutu: Hamza Diso
Abinda yake taimakawa wajen tabbatar da Mulki shine tabbatar da adalci a tsakanin wadanda ake mulka gaba daya, Wanda wannan ya kunshi hana satar dukiyar Al’umma koyin ruf da ciki akanta, da kuma tabbatar da isar hakkin kowa zuwa gare shi, duk kasar da take haka to Allah bazai taɓar dasu ko ya halakar dasu ba Koda kuma mushirikaine, Allah yace
وَمَا كَانَ رَبُّكَ لِيُهْلِكَ الْقُرَىٰ بِظُلْمٍ وَأَهْلُهَا مُصْلِحُونَ
Mahaliccin ka bai kasance mai halakar da mutan Alkaryu Don suna shirka ba idan har mutan garin suna kokarin kawo gyara.
Haka wasu daga cikin malamai suka fassara wanga aya, har ma suke cewa dukkannin Al’ummatan da aka halakar zaka samu suna da wani abu na laifi da sukeyi doriya akan shirka!!
Kuma komai adadin mutanan kirki da suke cikin Al’umma za a iya halakar da Al’umma idan ba a kokarin kawo gyara har barna ta yawaita,
Uwar muminai Zainab bint jahsh ta tambayi Annabi tace masa:
yanzu za a iya hallakamu Alhalin acikin mu akwai salihai?” Sai Annabi yace: kwarai idan barna tayi yawa.
Bukhari da Muslim
Shi kirkin mutum baya amfanar da wani sai kansa da iyalansa Kawai, abinda yake amfanarwa shine kokarin kawo gyara da samun ci gaba cikin Al’umma, wannan shiyasa a addini ake Fifita duk aikin da mutane zasu amfana dashi akan aikin da kai kadai Kawai zaiwa amfani, shiyasa neman ilimi yafi sallar Nafila ko Azumin nafila don Ilimi zai amfani Al’umma ne duka, Sallah kuma zata amfani Wanda yayitane Kawai da iyalansa.
Mumuni mai gwagwarmayar kawo gyara yafi Alkhairi Sama da muminin da baya gwagwarmaya
Annabi yace:
muminin da yake cakuduwa da mutane yake kuma hakuri da cutarwarsu yafi Alkhairi Sama da muminin da baya shiga mutane baya kuma hakuri da cutarwarsu.
Tirmizi ya ruwaito shi da sanadi ingantacce.
Leave a Reply