AL-GHADIR: KALUBALE GA ‘YAN SHI’A(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

INGANTACCEN LABARIN GHADIR:
Kalmar Ghadir a larabce, tana nufin wurin da ya tara ruwa da ciyawa.
“Ghadir Khum” sunan wani tafki ne da yake a yankin Juhfa, kilomita 15 daga Rabigh. Nisan sa daga Makka kilomita 160 ne.
Labarin Ghadir:
Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aiki Khalid dan Walid a matsayin kwamandan rundunar da za ta yi yaki a kasar Yaman daf da fara aikin Hajjin shekara ta 10H, hajjin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kansa ya jagoranta.
Bayan da rundunar musulmi ta ci nasara sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aika Sayyidi Ali don ya kula da sha’anin Ganimar da aka samu.
Ali Radhiyallahu Anhu ya raba Ganima, kuma ya cire hakkin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam na Khumusi kamar yadda Alkur’ani ya zayyana. Daga ciki kuma ya cire ma kansa wata kuyanga da ta ba shi shawa.
Sayyidi Ali bai bata lokaci ba ya zarce zuwa Makka don ya riski maigidansa Sallallahu Alaihi wa Sallam a wurin aikin Hajji. Ya kuma wakilta wani daga cikin sojoji akan sauran aikin da ya rage.
Domin ya dadada ran sojojin, wakilin Sayyidi Ali ya raba ma su tufafi kyawawa daga cikin abin da aka ganimanto. Ya kuma yi ma su izini kowa ya hau rakumin da yake so daga cikin kayan Ganima. Kafin haka, sojoji sun gabatar da bukatar haka ga Sayyidi Ali amma bai amince ba. Sai ya ce ma su, rabonku sai an je Madina.
Sojojin wannan runduna sun hadu da Sayyidi Ali tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam a kan hanyar su ta dawowa bayan gama aikin Hajji. Sayyidi Ali ya nuna rashin jin dadinsa a kan wannan rabo da aka yi kafin lokacin yinsa. Nan take ya yi umurni duk su sauka daga rakuman, suka kuma mayar da tufafin da aka raba masu. Rayukansu sun baci matuka a kan haka kuma sun kai karar sa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam suna zargin sa da cewa ya kuntata masu.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya iso Ghadir Khum, kuma ya lura da fushi a fuskar wadannan sojoji. Ya yi huduba yana tambayar su
(!ألستُ أولى بالمؤمنين من أنفسهم؟)
“Ashe ban fi muminai cancanta da kawunansu ba?” Suka ce masa, haka ne. Sai ya ce,
(فمن كنت مولاه، فعلي مولاه)
“To, duk wanda nake majibincinsa Ali ma majibincinsa ne”. Ma’ana, bai dace ku bata ranku a kan hukuncin da ya yi ba.
Da wannan babban jagora ya kwantar da wannan rikici da rashin fahimta, ya kuma nuna wajabcin a yi ma jagora da’a, sa’annan ya bayyana matsayin dan uwansa Sayyidi Ali a wurin muminai. Sojojin suka ba shi hakuri, suka gane matsayinsa, suka wuce Madina tare da sauran ayarin mahajjata da suke tare da shi.
Wannan shi ne abin da ya faru. Illa iyaka.
TATSUNIYAR GHADIR
‘Yan Shi’a sun ribaci wannan abin da ya faru kuma ya zo ya wuce kamar sauran ire-irensa. Suka fankama shi, suka fadada shi, suka mayar da shi wani gagarumin bukin nadin sarauta. Suka kuma jefi duk Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kin Allah da kauce ma gaskiya, da jayayya da wannan nadi da suka ce an yi.
Wannan akidar ta Ghadir a matsayin ranar buki ba a san ta a cikin tarihi ba sai bayan sama da shekaru 340 gwamnatin Shi’a ta Buwaihawa ta kago wannan bidi’a a kasar Iraqi. Suka mayar da ranar 18 ga watan Dhul Hajji a matsayin ranar wannan buki ta kowace shekara. Sukan taru a wurin kaburburan manyansu suna ta kururuwa suna la’antar masoyan Allah wadanda suka ce sun kauce ma umurni Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da ya bayar na mika mulki ga maigida Sayyidi Ali.
Sun kago ruwayoyi barkatai a kan falalar wannan rana, cikin su har da cewa wai, Imam Ar-Ridha ya ce, da mutane sun san matsayi da falalar wannan rana da Mala’iku sun rinka musafaha da su har sau goma a kowace rana.
Haka kuma sun kitsa tatsuniyoyi masu nuna wai, manyan Sahabbai sun yi ma Ali mubaya’a amma a munafurce, sannan suka shirya makarkashiyar kashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam. A cikin su kuma wai har da duk sauran tara daga cikin mutane goma da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya yi ma su bushara da aljanna.
KALUBALE GA ‘YAN SHI’A
Muna kalubalantar ‘yan Shi’a a kan wannan batu da wadannan tambayoyi:
1. Idan wannan magana ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa “Duk wanda nake majibincinsa Ali ma majibincinsa ne” tana nuna wajabcin shugabantar da shi, to me za ku ce game da fadar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam “Ko wace al’umma tana da amintacce, mu kuma amintaccenmu a cikin wannan al’umma shi ne Abu Ubaida”? Wa ya fi cancanta a cikin su kenan?
2. Idan har gaskiya ne an yi wannan nadin kamar yadda kuke cewa, me ya sa ba a umurci Sayyidi Ali da ya ci gaba da ba da Sallah ba musamman bayan da ciwon ajali ya kama Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam?
3. Me ya sa ba ayi wannan bukin a zamanin da Sayyidi Ali yake Khalifa ba ko Sayyidi Al-Hasan ko a zamanin duk Imamanku goma sha daya da suka rayu kafin Malam Na-boye (Mahadinku) ya zo duniya? Me ya sa sai lokacin da Buwaihi Bafarise mai kamun kifi ya kafa gwamnati sannan aka fara wannan buki a shekarar 352H?
4. Idan hudubar Ghadir tana nufin nadin sarauta ne, me ya sa ba ayi ta a Makka ba in da duk alhazan duniya suka taru su sama da mahajjata dubu dari?
5. Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam bai yi hudubobi a can Makka da Minna da Arafat ba? Me ya sa bai ware huduba ta musamman a kan wannan babbar maganar ta halifancin Sayyidi Ali ba?
6. Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam bai yi huduba a kan jinainai da dukiyoyi a ranar babbar sallah ba? Ashe bai yi ma al’umma wasici da muhimman abubuwan da suke bukatar sani ba? Ita wannan maganar ba ta kai muhimmancinsu ba ne ya manta da ita? Me ya sa sai da aka watse, kowa ya bi hanyar garinsu saura mutanen Madina kawai suka rage sannan ya yi wannan magana a cikin sunkurmin daji a tafkin Ghadir?
7. Ya ya aka yi Sahabbai suka riwaito wannan hudubar ta Ghadir alhalin kun ce sun boye kaso biyu cikin uku na Alkur’ani masu bayyana falalar Ahlulbaiti?
8. Kun ce duk rikicin da musulmi suka shiga a tsawon tarihi dalilin kauce ma wannan umurni na ranar Ghadir ne da sahabbai suka yi. Me ya sa Alkur’ani ya yi biris da labarin Ghadir?
9. Allah Tabaraka wa Ta’ala ya saukar da sura ta musamman a cikin Alkur’ani kan maganar Hudaibiya da mubaya’ar da sahabbai suka yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da har wuri da bishiyar da suka yi mubaya’a a karkashinta, kuma ya ce ya yarda da su a kan haka bisa ga abin da ke cikin zukatansu na imani da ikhlasi. Kuma ya ce, a lokacin da suke yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam mubaya’a hannun Allah yana saman nasu. Me ya sa idan har an yi wannan mubaya’a Allah bai kawo ta ba a cikin Alkur’ani?
10. Mubaya’ar da mata suka yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ita ma Allah ya kawo labarinta cikin Suratul Mumtahana. Shin ita wannan mubaya’ar ta Ghadir ba ta da muhimmanci ne irin wannan mubaya’ar mata ko kuwa?
‘Yan Shi’a ku ji tsoron Allah! Malamanku suna zargin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da boye wannan bayani wai a cikin Makka har suna cewa a kan wannan boyewar da ya yi sai da Allah ya saukar da ayar ”Ya kai wannan manzo ka isar da sakon da aka saukar ma ka daga wurin Ubangijinka. Idan kuwa har ba ka yi ba to, ba ka isar da sakonsa ba. Kuma Allah zai kare ka daga mutane”. To, sannan wai, ya tsaya a Ghadir Khum ya isar da wannan sako. Ku ji tsoron Allah! Ku darajanta manzonsa, ku koma ga gaskiya.
Wallahi, Sayyidi Abubakar da Sayyidi Umar da Sayyidi Usmanu da ma duk sauran sahabbai almajiran Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ba su jiye ma Sayyidi Ali da kome. Kuma ba su da wani kwadayi ga duniya balle su nemi shugabanci. Allah Ta’ala da kansa cewa ya yi a kan su:
(للفقراء المهاجرين الذين أُخرجوا من ديارهم وأموالهم يبتغون فضلا من الله ورضوانا وينصرون الله ورسوله أولئك هم الصادقون)
“-A bayar da Fai’i- ga talakawa Muhajirai wadanda aka fitar da su daga gidajensu da dukiyoyinsu suna neman falala daga Allah da yarda, kuma suna taimakon Allah da manzonsa. Wadancan su ne masu gaskiya”
To, ka ji. An kore su daga garuruwansu, aka kwace dukiyarsu kuma a cikin zukatansu ba zaman gida ko mallakar dukiya ne a gabansu ba. Babban gurinsu shi ne taimakon Allah da manzonsa. Ka kuma ji Allah ya ce ma su masu gaskiya. Don Allah ta ina wadannan za su yi kwacen mulki kuma har su shirya ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam makarkashiyar kisan sa?!
Ya Allah! Ka shiryar da bayinka, ka ceto su daga muguwar akidar da Farisawa ‘yan bautar wuta suka kago suka lullube ta da rigar musulunci don su halaka su. Allahumma Ameen

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

4 responses to “AL-GHADIR: KALUBALE GA ‘YAN SHI’A(Dr. Mansur Sokoto)”
  1. عؤسئ ابوبكر Avatar
    عؤسئ ابوبكر

    السلام عليكم نشكر كم علئ الفتح هذه الصفحة المباركة واسال الله ان يجعله في ميزان حسناتكم.

    1. Nibras Avatar

      آمين, جزاكم الله خيرا على زياراتكم وتعليقاتكم.

  2. Yusufh Halilu Abubakar Avatar
    Yusufh Halilu Abubakar

    Masha Allah

  3. dahiru suleiman Avatar
    dahiru suleiman

    Allah ya saka da alkhairi

Leave a Reply

Categories
Latest updates