Alqiyamah ta kusanto, ga wa su daga
cikin Alamomin ta, wasu sun faru,
wasu suna faruwa, wasu za su faru
nan gaba
Alamomi 001-100
1. Aiko Annabi (sallallahu-alaihi-
wasallam) {ranar litinin, 21/Ramadan/
0013bh daidai da 10/August/610m}
yana shekara arba’in 40 da wata shida
6 da kwana goma sha biyu 12 lissafin
wata/ shekara talatin da tara 39 wata
uku 3 da kwana ishirin 20
2. Wafatin Manzon Allah (sallallahu-
alaihi-wasallam) ranar litinin 12/
rabi’ul-Auwal/11ah yana da shekara
sittin da uku da kwana hu’du
3. Tsagewar wata
4. ‘Karewar Sahabbai
5. Bu’de Baitil-Maqdis
6. ‘Barkewar Annoba;- mai kama da
ciwon dabbobi
7. Bayyanar fitintunu masu yawa
8. Bapyyanar tashoshin tauraron ‘Dan
Adam
9. Yaqin Siffaini
10. Bayyanar khawarij
11. Masu da’awar Annabta ta qarya
12. Yalwatar Arzi’ki;- Arzi’ki zai
yalwata
13. Bayyanar wuta a Hijaz, dutse mai
aman wuta
14. Ya’ki da turkawa
15. Bayyanar Azzalumai masu dukan
babu dalili
16. Yawan zubar da jini;- kashe-kashe
17. ‘Dauke Amana;- ma su Amana za
suyi ‘karanci
18. Koyi da Yahudu da Nasara
19. Baiwa za ta haifi uwargijiyar ta
20. Bayyanar masu masu tsirara-
tsirara (ba sa shiga ta addini)
21. Matsiya ta, Matasa takalma masu
kiwon awaki, za su yi yin dogayen
gine-gine
22. Yin Sallama ga wanda aka sani
kawai;- mutane za su daina yi wa
mutum Sallama sai sun san shi
23. Ya’duwar kasuwanci;- ko ina zai
zama kasuwa
24. Mata za suyi tarayya da mazan su
a kasuwanci
25. Wasu tsirarun ‘yan kasuwa za su
mamaye kasuwanci;- ya zama ba ayi
da kai sai da yardar su
26. Shaidar Zur
27. ‘Boye shaidar gaskiya
28. Yawan Rowa;- mutane za su zama
marowata
29. Yanke zumunta
30. Munana maqotaka
31. Ya’duwar laifuffuka
32. Bayyanar jahilci
33. Amincewa maha’inci, da tuhumar
mai Amana
34. Mutuwar Mutanen ‘kwarai da
Ya’duwar lalatattu
35. Yaki Halal Yaki Haram
36. Rubda ciki akan Baitil-Mali
(Asusun-gwamnati)
37. Mayar da dukiyar Amana
ganimah
38. Rashin fitar da Zakkah da da’din
rai;- mutum ya ga zakka kamar Asara
Ce yayi
39. Yin Karatu dan Neman Abun
duniya
40. Yi wa mata biyayya da sa’bawa
Uwa
41. Fifita Abokai/’Kawaye akan iyaye
42. Hayaniya a masallatai
43. Mafi yawan shuwagabannin
Al’ummah za su zama fasiqai
44. ‘Kas’kantattu za su zama manyan
gari
45. Girmama mutum don tsoron
sharrin sa
46. Za a halatta Zina
47. Halatta Alhariri ga Maza (sa
Alhariri ga maza haramun ne, amma
za ayi zamanin da za a halatta shi
48. Ya’duwar Kayan maye
49. Ka’de ka’de da raye-raye za su
mamaye Al’ummah
50. Masifa da Bala’i za su yi wa Har
mutum ya dinga fatan mutuwa
51. Wani Zamani da mutum zai
kwana Mumini ya wuni kafiri;-
saboda mafi yawan maganganu da
aiyuka da ba sa kan Shari’ah
52. ‘Kawata Masallatai da yin gasar
Hakan (kaji ana Masallacin mu yafi
naku kyau)
53. ‘Kawata gidaje da yi musu
kwalliya
54. Yawan Saukar Kwarankwatsa da
Aradu
55. Yawan Rubuce-Rubuce;-
Ya’duwar Rubutuce-Rubuce marasa
amfani (jaridu da mujallu, da littafai
da internet) ba a tunanin amfanin
rubutun kawai da an rubuta
56. Wanda suka ‘kware a ro’ko da
ziga, su suka fi samun ku’di
57. Za shagala da karanta wasu
abubuwa a bar Al’qur’ani
58. ‘Karancin Malaman fi’khu da
yawan Gardawa
59. Neman Ilimi a wajen ‘kananan
mutane;- ‘karamin Mutum wanda ba
ya aiki da ilimin sa
60. Yawan mutuwar ba-zata
61. Shugabancin Wawaye (kuma suna
ganin kan su wayaiyu)
62. Lokaci zai dinga sauri
63. Banzaye za su mamaye kafafan
ya’da labarai;- Mutumin da ba kowa
ba, kuma bai zan komai ba, zai dinga
magana kan abubuwan da suka shafi
Al’ummah
64. Ma’daukaki a duniya shine banza
‘dan banza;- kaga ana ta rububin wani
wanda bai da amfanin komai saboda
wani shirme da yake Misali;- ‘Yan Bal
da Mawa’ka
65. Mai da cikin masallatai Hanyoyi
66. Sadakin Aure zai yi tsada, sai
kuma ya zo yai arha
67. Dawakai za su yi tsada sai kuma
su zo su yi arha
68. Kasuwanci zai yi sau’ki (ta yadda
zaka sai Abu ko ka sayar daga ‘dakin
ka, ba tare da ka je ko ina ba) Misali;-
yanar gizo
69. Kafiran duniya za su yi taron
dangi akan musulmi
70. Mutane za su dinga gudun limanci
a cikin Sallah (saboda ba cikakken
Albashi)
71. Aukuwar Mafarkin Mumini (in
Mumini yai mafarki sai Abu ya faru
72. Yawan ‘karaya
73. yawan gaba
74. Girgizar ‘kasa
75. Yawan Mata
76. ‘Karancin Maza
77. Aikata Sa’bo a filigahh
78. Mai da karatun Al’qur’ani hanyar
Neman ku’di
79. ‘Kiba, mutane za su yi ta ‘kiba mai
yawa
80. Bayyanar mutane masu yin shaida
tun ba a tambaye su ba
81. Masu Bakance ba sa cikawa
82. Masu ‘karfi za su danne raunana
83.’Rashin Hukunci da Alqur’ani
84. Yawan rumawa da ‘karancin
larabawa
85. Ya’duwar ku’di
86. ‘Kasa za ta fitar da taskokin ta
87. MòZa a dinga shafe halittar wasu
mutane suna komawa wata 88.Halitta
daban
89. Tsagewar ‘kasa, ta ha’diye mutane
90. Wasu ‘kwarangwazai, duwatsun da
ba a San su ba za su dinga 91. fa’dowa
mutane aka
92. Yawan ambaliyar ruwa
93. Ruwan ‘bala’i;- wanda ba ya fidda
shuka ko tsiWwFitina da za ta 93.wata
fitina za ta’barke tsakanin larabawa
Har ta kusa ‘karar da su
94. Bishiya za ta yi magana don
taimakawa musulmi
95. Dutse zai magana don taimakawa
musulmi
96. Ya’kin Musulmi da Yahudu
97. Kogin furat zai ‘kafe, a hango
Dutsen Gwal a ciki
98. Zamanin da za a yiwa masu addini
kallon ba wayayyu ba
99. ‘Kasashen larabawa za su samu ci-
gaba mai yawa
100.Bayyanar wata Babbar fitina da
zata shafi kowa
Mu ha’du a darasi na gaba
Allah ya kare mu sharrin fitintunu
Leave a Reply