ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA (2)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

Mun tsaya a alama ta 100, zamuci gaba
101 Bayyanar bakar fitina gama gari sai ta shafi kowa.
102 masifu za suyi yawa birni da kauye
103 Wani zamani zezo sujjada daya tafi duniya da abinda yake cikin ta, saboda karancin masu ibada,
104 Ragima akan ganin wata, saboda wata zai kumbura, ya dinka fiyowa babba
105 za a dinka kaura ana komawa yankin Sham. Syria,
106 Yakin duniya tsakanin musulmi da Rumawa (
Turawa)
107 Zaa bude yankin Qusdunsuniyya, karo na biyu, bayan na zamanin daular Usmaniyya
108 Zaa dena rabon gado, ( masu karfi su cinye na kanana)
109 Zaa dena farin ciki da samun ganima (saboda wadata tayi yawa)
110 Zaa koma amfani da makamai na gargajiya, saboda na zamani zasu dena amfani,
111 Zaa raya baitul Maqdis, bayan karbo shi daga yahudawa
112 Mutane zasu kauracewa Madina, idan shagala tayi yawa
113 Madina zata kore ashararai daga cikin ta, babu mai jin dadin zaman madina sai mumini
114 Duwatsu zasu gushe daga gurin su, saboda gine-gine na ci gaba.
115 Wani mutum zai fito daga yankin Qahdan na larabawa kuma mutane zasu bishi,
116 Bayyanar wani mutum mai suna Jah,Jah
117 Dabbobin dawa zasuyi magana irin ta mutane, kamar zaki da kura da makaman tansu.
118 Tsumagiya ma zatayi magana,( Bulala)
119 Hancin takalmi zaiyi magana,
120 Jikin mutum zaiyi magana (kamar cinyarsa) ya bashi labarin abin da iyalansa suke aikayawa idan bayanan
121 Alkiyama baza ta tashiba sai anyi watsi da musulunci, ba karatu ba aiki.
122 Alkiyama baza ta tashi ba sai an dauke Alkur’ani mai girma daga cikin takardu, da kirjin mahaddata,
123 Wata bataliyar mayaka zasu tunkari macca da niyar yaki, amma kasa zata hadiye su a hanya
124 Zaa kauracewa zuwa aikin hajji
125 Kabilar kuraishawa zasuyi kadan a duniya
126 Rushe kaabah ta hannun wani mutum daga yankin Habasha
127 Wata iska mai dadi zata dinka dauke ran muminai idan musifa tayi yawa
128 Zaa dinka yin ginai- ginai masu tsawo a Macca
129 Wasu tsinannun mutane, zasu dinka laantar magabata, (Masu zagin sahabbai)
130 Zaa sami kayan hawa na zamani,
131 Bayyanar Ma’hadi,
Zamu ci gaba a darasi na uku, kuma insha Allahu zamu dauki daya bayan daya domin sharhi da karin bayani, duka wadananan alamomi wadanda suka zo ne a cikin ingatattun hadisai, na sunnah (Allah ya sa mu cika da imani)

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

3 responses to “ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA (2)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)”
  1. Haxxanyally Avatar

    I’m just want it

  2. Haxxanyally Avatar

    I’m just want open it

  3. Haxxanyally Avatar

    Anything what you want do, just put it in your heart.

Leave a Reply

Categories
Latest updates