ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa ta 10
Me Ya Sa Aka Zabi Yankin
Larabawa?
6. Yaren da suke amfani da shi; larabci
shi ne wanda Allah a cikin hikimarsa
ya sanya shi ya zamo yaren da za a isar
da sakonsa na karshe da shi. Alkur’ani
a matsayinsa na gamammen sako zuwa
ga duniya mai jama’a iri daban daban
da miliyoyin harsuna da dabi’u, wanda
kuma zai wanzu har zuwa tashin
kiyama yana bukatar harshe mai fadi
tare da sauki da fasaha da kuma
gwaninta wajen bayyana abinda ake so
zuwa ga mutane. Masana sun tabbatar
larabci shi kadai ke da wannan kamala.
Bari mu dan yi wani kwatance a nan
tsakanin harshen larabci da kuma na
nasara (turanci) wanda a duniyar yau
yake cin karensa ba babbaka a
matsayinsa na yare mai daraja ta daya
a idon duniya. Idan ka dauki wadannan
kalmomi na lamirin abokan magana
guda biyar a larabce, su ne: Anta, Anti,
Antuma, Antumu da kuma Antunna.
Ba wata fassarar da zaka iya ba su da
turanci sai “You”. Tun daga nan ka ga
fasahar ba ta zamo daya ba. A kan
haka ne cikin hikimar madaukakin
sarki ya zabi wannan kammalallen yare
don isar da mafi cikar sakonsa a
hannun mafi cikar mutane zuwa ga
al’umma mafificiya.
Wannan shi ne dalili na karshe da
zamu iya kawowa domin nuna hikimar
da ke cikin tada manzonmu na karshe a
wancan yanki na duniya da ake ganin
sa a matsayin mafi ci baya a duniyar
wancan lokaci. Babu shakka, Allah (T)
ya yi babbar ni’ima ga wadannan bayi
nasa; larabawa da ya dora ma su
wannan gagarumin aiki. Suna a cikin
halin rauni sai ya karfafa su. Suna
jahilai ya ilmantar da su. Suna
talakawa ya wadata su. Suna a tarwatse
ya hada kansu. Suna a matsayin sifili a
cikin duniya ya mayar da su su ne
kowa, albarkancin farin jakadan da
muke haramar shiga cikin cikin
tarihinsa mai tsarki, wanda suka zamo
baradensa. Take wadannan bayin Allah
da aka zaba suka rufa masa baya, suka
kulla adawa da duk wanda ya yi fatali
da kiransa. Suka kawar da manyan
daulolin da ke hada-hada a wancan
lokaci cikin yan shekaru kadan. A
hankali sai addinin musulunci ya game
duniya baki daya.
Don haka, daga cikin manyan darussan
wannan tarihi da zamu karanta akwai
koya mana mutuntawa da kauna da
kyakkyawar addu’a ga magabatan
wannan al’umma nagartacciya. Kamar
yadda madaukakin sarki ya karantar da
mu bayan da ya kawo labarinsu, in da
yake cewa:
( ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺟﺎﺅﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﺭﺑﻨﺎ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻨﺎ
ﻭﻹﺧﻮﺍﻧﻨﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺳﺒﻘﻮﻧﺎ ﺑﺎﻹﻳﻤﺎﻥ ﻭﻻ ﺗﺠﻌﻞ ﻓﻲ
ﻗﻠﻮﺑﻨﺎ ﻏﻼ ﻟﻠﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﺭﺑﻨﺎ ﺇﻧﻚ ﺭﺅﻭﻑ ﺭﺣﻴﻢ )
Ma’ana: “Kuma da wadanda suka zo a
bayan su suna cewa, ya ubangijinmu!
Ka gafarta mana kuma da yan uwanmu
da suka riga mu ba da gaskiya. Kuma
kada ka sanya jin haushi a cikin
zukatanmu ga wadanda suka yi imani.
Ya ubangijinmu! Hakika, kai ne mai
tausayi, mai jinkai”. Suratul Hashr: 10.
Mu kwana lafiya yan uwana.
Leave a Reply