ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa Ta 20
Reno Da Shayarwa A Gidan Banu
Sa’ad
Makka – kamar yadda muka sani –
babbar mahada ce ta al’ummomi daban
daban na larabawa a wancan lokaci.
Abinda ya sanya mutanen garin suke
nisantar da kananan yaransu daga garin
tun daga haifuwarsu don kada yarensu
ya gurbata da yaren baki masu zuwa
ziyara daga sassa daban daban. Don
haka sai su bayar da su reno a cikin
kauyuka inda yaren Quraishu na asali
ba ya canjawa. Wannan ya kan sa yaro
ya tashi da mikakken harshe da
gangariyar larabci wanda babu
garwaye a cikinsa.
Daga cikin amfanin tashin yara kanana
a kauye kuma akwai nisantar cinkoson
jama’a wanda sau da yawa yakan
haddasa curutoci da annoba sakamakon
gurbatar yanayi. Samun sarari da iska
mai dadi da ke kauye kan sanya
kwakwalwar yaro ta zamo mai fadi,
basirarsa ta zamo mai kaifi, jikinsa
kuma ya yi kwari.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam na cikin wadanda suka
amfana da wannan al’ada kyakkyawa
domin kuma Halima ‘yar gidan Harith
daga cikin matan Banu Sa’ad ita ce
wacce ta karvi renon sa a daidai
wannan lokaci. Ta kuwa tafi da shi can
tungarsu ta bani Sa’ad in da ya zauna
wurinta har zuwa lokacin yaye. An ba
da labarin irin albarkoki da alhairai da
wannan baiwar Allah ta gani a lokacin
zaman sa a tungarsu ta Banu Sa’ad,
abin da ya sa ita da kanta ta fahimci
cewa lallai wannan yaro yana da wani
sha’ani na musamman. Halima ta fadi
cewa, ba ta da wadataccen nono kafin
ta dauki manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam. Haka su ma
dabbobin da suke kiwo suna cikin
fatara da bushewa; babu ni’ima ko
kadan ga jikinsu. Ta ci gaba da cewa,
tun daga ranar da ta dauko Muhammad
Sallallahu Alaihi Wasallam sai yanayi
ya canja. Mammanta suka cika har
suna darara, haka ma na dabbobinta.
Yalwantar arziki ta same su sosai har
makwauta suka ci albarkacinsu.
Wannan ya sa jinjirin – Sallallahu
Alaihi Wasallam – ya samu dadin so da
kauna da kulawa daga wurinsu.
A dalilin haka, da ta yaye shi sai ta
nemi alfarma daga wurin mahaifiyarsa
a dan kara ba ta lokaci domin ta ci gaba
da kula da shi. Fatarta ita ce, ta ci gaba
da rikonsa har girmansa domin ta ci
gaba da cin moriyar albarkokinsa kuma
ta gane ma idonta abinda Mai-sama
yake nufi da wannan nagartaccen taliki.
To, sai dai wannan gurin nata ya yanke
tun lokacin da wani abin al’ajabi ya
faru wanda ya sanya ta jin tsoro kuma
ala tilas ta hakura ta mayar da shi birni
in da mahaifiyarsa da danginsa. Daman
kuma haka Mai-sama ya tsara, lokacin
zamansa kauye ya zo karshe kenan,
duk abinda ake so ya koya daga
mutanen karkara ya riga ya gama
koyon sa.
Abin da ya faru shi ne, daidai lokacin
da Muhammad Sallallahu Alaihi
Wasallam yake karkashin kulawarta,
yana kimanin dan shekaru hudu, a wata
safiya sai ya fita wajen tunga suna
kiwon tumaki tare da abokan renonsa.
Kawai sai wasu mutane guda biyu suka
zo suka kama shi, suka kwantar da shi,
suka fito da wuka suka fasa kirjinsa,
suka ciro zuciyarsa. Ganin haka sai
abokan kiwonsa suka ruga zuwa wajen
iyayen rikon sa suna cewa, an kashe
Muhammad! An kashe Muhammad!.
Bayan fitowa da zuciyarsa sai daya
daga cikin mutanen nan biyu ya fizge
wata bakar tsoka daga cikin ta ya zubar
da ita, ya ce, wannan shi ne rabon
shedan a cikin ka, sa’annan ya dauko
wata tasa wacce take cike da qanqara
ya wanke zuciyar nan tas, ya mayar da
ita kamar yadda take, ya dunke.
Sannan su biyun suka kama hanya
suka yi tafiyar su.
Ko da mutanen tunga suka rugo domin
su ga abin da yake faruwa sai suka
hadu da shi yana dawowa duk fuskar
sa ta canja. Anas bin Malik (RA) ya
ce, na kasance ina ganin alamun zaren
da aka yi dunki da shi a kirjin manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.
Sahihu Muslim, Kitabul Iman, hadisi
na 261.
Allahu akbar! Ka ji dalilin da ya sa
shedan tun asali ba ya da rabo a cikin
wannan wankakkiyar zuciya ta manzon
Allah. Don haka bai taba fushi don an
taba shi ba sai dai idan an saba ma
mahaliccinsa. Kuma shi ne ya sa bai
taba yi wa gumaka sujuda ba, bai
kuma shiga cikin duk wasu wasanni da
suka danganci jahiliyyah ba.
Allah gwanin sarki! Wannan tiyata ta
sake faruwa bayan haka a lokuta guda
biyu. Na farko shi ne lokacin samun
annabtarsa. Imam Al-Bazzar, ya
ruwaito haka a cikin Musnad nasa,
Hadisi na 4048 kuma Al-Hakim ya
inganta shi. Na biyun kuma shi ne
lokacin Isra’i da Mi’iraji kamar yadda
zamu gani a nan gaba, kuma labarin
wannan tiyata ta uku ya tabbata a mafi
ingnacin littafan ruwaya “Bukhari da
Muslim”. A wannan karon Jibrilu (AS)
shi kadai ya zo ya yi tiyatar kuma ya yi
amfani da ruwan Zamzam wajen
wanke zuciyar. Sannan bayan da ya
kare wanke ta karo na uku sai ya
kwarara ma sa hikima a cikin ta.
Malamai suka ce, amfanin yin tiyata
karo na biyu shi ne sanya rahama da
tausayi a cikin zuciyarsa bayan an cire
ma sa jin haushi da hasadar jama’a
wadanda al’adance akwai su a cikin
zukatan mutane. A karo na ukku kuma,
an kara tsarkake zuciyar ne daidai
lokacin da zai gana da mahaliccinsa in
da zai karbo wani muhimmin sako; shi
ne sallah wacce ba a yin ta sai an yi
alwala. A alwala kuma ai sau uku ne
ake wanke gabbai. Don haka zuciyarsa
ta bukaci wanki karo na uku don kai
matuka wajen tsarkakewa da
wankewa. Kwarara hikima da aka yi a
zuciyarsa a wannan lokaci ya sanya shi
shi ne mutum na farko da ya iya isar da
sakon Allah zuwa ga mutane cikin
hikima da tsanaki, wanda mutum ya
kan zo ma sa da nufin ya kashe shi
saboda kiyayya amma cikin
gwanintarsa sai ya dauki matakin da
nan take wannan mutum zai koma
cikin masoyansa, kai ma cikin
mabiyansa wadanda ke iya ba da
rayuwarsu kai tsaye don kariyarsa.
Nan gaba zamu ga misalai da dama
kan wadannan abubuwa cikin yardar
Allah.
Akwai ruwayar wata tiyata a lokacin
da Sallallahu Alaihi Wasallam ya kai
shekaru goma. To, sai dai duk da yake
Imam Ahmad ya ruwaito ta a cikin
Musnad (5/139) amma isnadin ruwayar
bai inganta ba kamar yadda Sheikh
Shu’aib Al- Arna’ut ya tabbatar a cikin
nazarinsa.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: