Allah yana yafe wa masu aikata zunubi sai mai bayyana wa

Danna nan domin shiga karatu Online

An rawaito daga Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:

كُلُّ أُمَّتي مُعافًى إلَّا المُجاهِرِينَ، وإنَّ مِنَ المُجاهَرَةِ أنْ يَعْمَلَ الرَّجُلُ باللَّيْلِ عَمَلًا، ثُمَّ يُصْبِحَ وقدْ سَتَرَهُ اللَّهُ عليه، فَيَقُولَ: يا فُلانُ، عَمِلْتُ البارِحَةَ كَذا وكَذا، وقدْ باتَ يَسْتُرُهُ رَبُّهُ، ويُصْبِحُ يَكْشِفُ سِتْرَ اللَّهِ عنْه

duka Al’umma ta suna samun afuwar Allah da sitirarsa sai dai masu bayyana laifukansu, yana daga cikin bayyana laifi mutum ya aikata wani mummunan aiki da dare ya wayi gari Allah ya rufa masa asiri sai yace: ya kai wane jiya na aikata laifi kazaa da kazaa. Ya kwana Allah yana rufa masa asiri shi kuma ya wayi gari yana mai yaye sitirar Allah akansa.

Wannan hadisi Imamul Bukhari ya rawaito shi acikin littafinsa a hadisi mai lamba ta 6069.

Wannan hadisi yana nuna girman laifin mai bayyana laifi, kodai yayi mutane suna ganinsa, ko kuma yayi a ɓoye yazo yana bada labari wa mutane, duka wannan bai halatta ba, domin hakan na janyo fushin Allah da kuma rashin yafe wa bawansa. Allah yasa mudace. Allah ya yafe mana zunubanmu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates