Imam ibnul Qayyim yace:
Sheikhul Islam Ibn taimiyyah ya kasance idan lamura sukayi masa tsanani sai ya karanta Ayoyin natsuwa
Sannan yasake cewa:
Haka nan ya sake faɗi game da lokacin da Sheikhul Islam yake rashin lafiya, lokacin da lamari ya tsananta a kansa, Sheikhul Islam yace lokacin da Al’amura sukayi min tsanani sai na faɗa wa makusanta na da wa’inda suke kewaye dani su karanta min Ayoyin natsuwa. Suna karanta min sai naji duk abinda nake fama dashi ya kau.
Imam ibnul Qayyim shima ya jarraba amfani da wannan Ayoyin kuma yaga tasirinsu sosai yake cewa:
Nima na jarraba karanta Ayoyin natsuwa lokacin kaɗuwar zuciya sabida tsananin tsoro, kuma naga tasirinta sosai na wurin samun natsuwar zuciya.
Ga Ayoyin natsuwa kamar haka:
{وَقَالَ لَهُمْ نِبِيُّهُمْ إِنَّ آيَةَ مُلْكِهِ أَن يَأْتِيَكُمُ التَّابُوتُ فِيهِ سَكِينَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ}. (البقرة: 248).
{ثُمَّ أَنَزلَ اللّهُ سَكِينَتَهُ عَلَى رَسُولِهِ وَعَلَى الْمُؤْمِنِينَ}. (التوبة: 26).
{إِذْ يَقُولُ لِصَاحِبِهِ لاَ تَحْزَنْ إِنَّ اللّهَ مَعَنَا فَأَنزَلَ اللّهُ سَكِينَتَهُ عَلَيْهِ وَأَيَّدَهُ بِجُنُودٍ لَّمْ تَرَوْهَا}. (التوبة:40).
{هُوَ الَّذِي أَنزَلَ السَّكِينَةَ فِي قُلُوبِ الْمُؤْمِنِينَ لِيَزْدَادُوا إِيمَاناً مَّعَ إِيمَانِهِمْ وَلِلَّهِ جُنُودُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا}. (الفتح: 4).
{لَقَدْ رَضِيَ اللَّهُ عَنِ الْمُؤْمِنِينَ إِذْ يُبَايِعُونَكَ تَحْتَ الشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمْ فَأَنزَلَ السَّكِينَةَ عَلَيْهِمْ وَأَثَابَهُمْ فَتْحًا قَرِيبًا}. (الفتح:18).
{إِذْ جَعَلَ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي قُلُوبِهِمُ الْحَمِيَّةَ حَمِيَّةَ الْجَاهِلِيَّةِ فَأَنزَلَ اللَّهُ سَكِينَتَهُ عَلَى رَسُولِهِ وَعَلَى الْمُؤْمِنِينَ}. (الفتح: 26).
Idan mutum yana halin damuwa da firgici zai iya karanta wa’innan ayoyin domin neman Allah ya yaye masa, kuma Insha’Allah Allah zai yayemasa.
Leave a Reply