Azumin sitta shawwal ga wanda ake bi azumin Ramadan

Danna nan domin shiga karatu Online

Abu Sananne ne cewa Azumin sitta shawwal yana da falala mai girman gaske, anaso Musulmi ya azumce shi in ya samu dama, Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya nuna cewa Azumtar Watan Ramadan sannan Azumi shida acikin watan shawwal bayan Ramadan yana daidai da Azumin shekara. Toh haƙiƙa wannan falala ce babba wanda bai dace Musulmi yayi wasa da ita ba. Toh shin Mutum zai iya yin wannan azumi koda ko ana binsa bashin azumin watan Ramadan?

An samu tsaɓani tsakanin Maluma kan halaccin hakan, wasu suna ga cewa dole sai mutum ya kammala ramakon Azumin watan Ramadan da ake binsa kafin ya fara wannan azumi shida na Shawwal, suka nuna cewa Annabi cewa yayi:

Wanda ya Azumci Ramadan sannan ya biyo bayansa da Azumi shida toh kamar yayi azumin shekara neMuslim 1164

Da wannan ne suke ganin cewa ai wanda bai yi azumin Ramadana cikakke ba, ba zai sami wannan lada da Annabi yayi bayani akai ba,

Magana ta biyu kuma wacce itace tafi inganci shine Mutum zai iya Azumtar Sitta shawwal sannan daga baya yazo ya rama azumin da ake binsa na Ramadan, saboda shi lokacin ramako baya taƙaita a cikin wata ɗaya, lokacinsa yana da faɗi, amma lokacin Azumin sitta shawwal kuma lokacin sa babu faɗi, domin da zarar watan ya fice shikenan. Kuma duk wanda ya sha azumin watan Ramadan saboda wani Uzuri wanda Shari’a ta yarda da shi toh kamar wanda yayi Azumi ne. Wannan yake nuna cewa zai iya yin azuminsa na sitta shawwal sannan sai daga baya yazo ya rama Azumi da ake binsa na Ramadan, sai dai kuma idan mutum ya samu daman Ramako kafin ya fara Sitta Shawwal to hakan shi yafi dace wa, musamman in ya zamto azumin da ake binsan basu da yawa. 

A taƙaice

Wanda ake bin shi ramakon Azumin watan Ramadan abin da yafi dacewa a gare shi shine yayi gaggawa wurin rama azumin da ake bin shi kafin yayi azumin sitta shawwal, amma idan azumin da ake bin shi na da yawa bazai iya rama wa kuma yayi azumin sitta shawwal a lokaci ɗaya ba to zai iya fara gabatar da azumin sitta shawwal kafin ramako, domin lokacin sitta shawwal lokaci ne taƙaitacce

Allah shine mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates